< Markus 14 >

1 Idin Ketarewa da bukin gurasa mara yisti sauran kwana biyu kenan, sai shugabanin firistoci da malaman attaura suka nemi yadda zasu kama Yesu a asirce domin su kashe shi.
Now the Passover and the Feast of Unleavened Bread were two days away, and the chief priests and the scribes were looking for a way to arrest Jesus secretly and kill him.
2 Suna cewa amma “Ba a lokacin idin ba, domin kada su haddasa hargitsi a tsakanin mutane”.
But they said, “Not during the feast, otherwise there will be a riot among the people.”
3 Yesu yana Betanya a gidan Saminu kuturu, yana shirin liyafa kenan sai ga wata mace dauke da kwalbar turare mai tamanin kwarai, ta shafa masa a kansa.
Meanwhile Jesus was in Bethany, reclining at the table in the house of Simon the leper, and a woman came with an alabaster jar of very expensive ointment made of pure nard. She broke the alabaster jar and poured the ointment on his head.
4 wasu dake tare da Yesu suka husata, suna kwalbarta da cewa
But some were expressing indignation to one another, saying, “Why has this ointment been wasted?
5 “Ai wannan turare ne mai tsada, ina laifin a sayar a raba wa talakawa kudin? ina dalilin wannan almubazaranci?
It could have been sold for more than three hundred denarii, and the money could have been given to the poor.” So they began scolding her.
6 Sai Yesu yace masu “Ku kyaleta, don me kuke tsauta mata,
But Jesus said, “Leave her alone. Why are you causing trouble for her? She has done a good deed to me.
7 ai Idan kuna da niyyar taimakon talakawa ko matalauta, suna nan tare da ku ko a yaushe amma ni bazan kasance da ku kullum ba.
For you always have the poor with you, and you can do good to them whenever you want, but you will not always have me.
8 Macen nan tayi aiki nagari domin shirya jikina ga jana'iza.
She has done what she could; she has anointed my body beforehand to prepare me for burial.
9 hakika, Ina gaya maku, duk inda za'a yi bishara a duniya baza a mance da matan nan da hidimar da ta tayi mini ba.”
Truly I say to you, wherever this gospel is preached in the whole world, what this woman has done will also be spoken of as a memorial to her.”
10 Da jin haka sai Yahuza Iskariyoti, daya daga cikin manzannin ya ruga zuwa wurin baban firist domin ya bashe shi a garesu,
Then Judas Iscariot, one of the twelve, went to the chief priests to deliver Jesus up to them.
11 Da mayan firistoci suka ji haka suka yi murna matuka tare da alkawarin kudi ga Yahuza, shi kuwa sai ya fara neman zarafin da zai mika Yesu a gare su.
When they heard why he had come, they were glad and promised to give him money. So he began looking for a way to betray Jesus at an opportune time.
12 A ranar farko ta bukin gurasa marar yisti da kuma hadayar ragon Idin ketarewa, almajiransa suka ce masa “Ina zamu shirya liyafar domin idin ketarewa?
On the first day of the Feast of Unleavened Bread, when the Passover lamb is sacrificed, Jesus' disciples said to him, “Where do yoʋ want us to go and make preparations for yoʋ to eat the Passover?”
13 Ya aiki biyu daga cikin almajiransa da cewa “Ku shiga cikin birnin, zaku tarar da wani mutum dauke da tullun ruwa.
So he sent two of his disciples and said to them, “Go into the city, and a man carrying a jug of water will meet you. Follow him.
14 Duk gidan da ya shiga ku bishi, sai ku cewa mai gidan, malam yace “ina bukatar masauki domin hidimar idin ketarewa tare da almajiraina?”'
Wherever he enters, tell the master of the house, ‘The Teacher asks, “Where is the guest room where I can eat the Passover with my disciples?”’
15 Zai kuwa nuna maku babban bene gyararre. Sai ku yi mana shiri a can.”
He will then show you a large upper room, furnished and prepared; make preparations for us there.”
16 Da shigar almajiran cikin birnin, sai kome ya kasance yadda ya fada, su kuwa suka yi shirye shiryen idin ketarewar.
So his disciples left, went into the city, and found it just as Jesus had told them, and they prepared the Passover.
17 Da maraice ta yi, sai ya tare da sha biyun.
When it was evening, Jesus came with the twelve.
18 Yayin da suke zazzaune a teburin suna cin abincin, sai Yesu ya ce “Hakika ina gaya maku wani da ke ci tare da ni a nan zai bashe ni”.
As they were reclining at the table and eating, Jesus said, “Truly I say to you, one of you who is eating with me will betray me.”
19 Sai suka damu suka tambaye shi daya bayan daya suna cewa “Hakika bani bane ko?”
So they began to be sorrowful and to say one after another, “Surely not I?” and, “Surely not I?”
20 Yesu ya amsa masu da cewa “Daya daga cikin sha biyu ne, wanda ke sa hannu tare da ni yanzu cikin tasar”.
Jesus answered them, “It is one of the twelve, one who is dipping bread with me into the dish.
21 Dan Mutum zai tafi ne yadda nassi ya umarta game da shi amma kaiton wanda zai bashe shi! “zai, fiye masa, dama ba a haife shi ba”.
The Son of Man indeed goes just as it is written of him, but woe to that man by whom the Son of Man is betrayed. It would have been better for that man if he had not been born.”
22 Lokacin da suke cin abincin, Yesu ya dauki gurasa ya sa albarka, ya gutsuttsura ta, sai ya basu yana cewa “Wannan jikinana ne”.
As they were eating, Jesus took bread, and when he had blessed it, he broke it, gave it to them, and said, “Take and eat this bread; this is my body.”
23 Ya kuma dauki koko, yayi godiya, ya basu, su kuwa suka sha daga kokon.
Then he took the cup, and when he had given thanks, he gave it to them, and they all drank of it.
24 Ya ce “Wannan jinina ne na alkawari da an zubar ga yawancin mutane”.
He said to them, “This is my blood of the new covenant, which is poured out for many.
25 Hakika, bazan kara sha daga wannan ruwan inabi ba sai a ranar da zan sha sabo cikin mulkin Allah.”
Truly I say to you, I will certainly not drink again from the fruit of the vine until that day when I drink it anew in the kingdom of God.”
26 Bayan sun raira wakar yabo ga Allah, sai suka tafi wurin dutsen zaitun.
And after singing a hymn, they went out to the Mount of Olives.
27 Yesu ya ce masu dukkan ku zaku yi tuntube harma ku fadi saboda ni gama rubuce take cewa “Zan buge makiyayin, tumakin kuwa za su watse;
Then Jesus said to them, “All of you will fall away because of me this night. For it is written, ‘I will strike the shepherd, and the sheep will be scattered.’
28 Amma bayan tashina, zai yi gaba in riga ku zuwa Galili.
However, after I have been raised up, I will go ahead of you to Galilee.”
29 Bitrus ya ce masa “ko dukkansu sun fadi, faufau banda ni”.
But Peter said to him, “Even if everyone else falls away, I will not.”
30 Yesu yace masa “Hakika ina gaya maka, cikin wannan dare kafin carar zakara ta biyu zaka yi musun sani na sau uku”.
Jesus said to him, “Truly I say to yoʋ that today, on this night, before a rooster crows twice, yoʋ will deny me three times.”
31 Amma Bitrus ya sake cewa “Koda za'a kasheni tare da kai ba zan yi musun sanin ka ba”. Dukkan su kuwa suka yi wannan Alkawari.
But Peter said all the more vehemently, “Even if I must die with yoʋ, I will certainly not deny yoʋ.” And they all said the same thing.
32 Suka isa wani wuri da ake kira Getsamani, sai Yesu ya ce wa almajiransa “Ku dakata anan domin zan je inyi addu'a”.
Then they went to a place called Gethsemane, and Jesus said to his disciples, “Sit here while I go and pray.”
33 Sai ya dauki Bitrus, da Yakubu, da Yahaya. Ya fara jin wahala mutuka tare da damuwa kwarai.
He took with him Peter, James, and John, and began to be greatly disturbed and distressed.
34 Sai ya ce masu “Raina na shan wahala harma kamar in mutu. Ku dakata a nan, ku zauna a fadake”.
He said to them, “My soul is very sorrowful, even to the point of death; stay here and keep watch.”
35 Da Yesu yayi gaba kadan, sai ya fadi kasa yayi addu'a yana cewa idan mai yiwuwa ne “A dauke masa wannan sa'a daga gare shi.
Going a little farther, he fell on the ground and prayed that, if it were possible, the hour might pass from him.
36 Ya ce “Ya Abba Uba, kome mai yuwane gare ka, ka dauke mini kokon wahalan nan, duk da haka ba nufina ba sai dai naka”.
He said, “Abba, Father, all things are possible for yoʋ. Take this cup away from me; nevertheless, not what I will, but what yoʋ will.”
37 Da komowarsa ya same su suna barci, sai ya ce wa Bitrus, Siman barci kake? Ashe, ba za ka iya zama a fadake ko da sa'a daya ba?
Then he came and found them sleeping, and said to Peter, “Simon, are yoʋ sleeping? Could yoʋ not keep watch for one hour?
38 Ku zauna a fadake, kuyi addu'a kada ku fada cikin jaraba. Lalle ruhu na da niyya amma jiki raunana ne.
Keep watch and pray, lest you enter into temptation. The spirit indeed is willing, but the flesh is weak.”
39 Sai ya sake komawa, yayi addu'a, yana maimaita kalmominsa na farko.
Once again he went away and prayed the same prayer.
40 Har wa yau kuma ya sake dawowa, ya same su suna barci don barci ya cika masu idanu kwarai, sun kuwa kasa ce masa kome.
When he returned, he found them sleeping again, for their eyes were heavy, and they did not know what to say in response.
41 Ya sake komowa karo na uku yace masu “har yanzu barci kuke yi kuna hutawa? Ya isa haka! Lokaci yayi, an bada Dan Mutum ga masu zunubi”.
Then he came a third time and said to them, “Sleep on now and take your rest! That is enough; the hour has come. Behold, the Son of Man is delivered up into the hands of sinners.
42 Ku tashi mutafi kun ga, ga mai bashe ni nan ya kusato.”
Rise, let us go! Behold, my betrayer has drawn near.”
43 Nan da nan, kafin ya rufe baki sai ga Yahuza, daya daga cikin sha biyun da taron jama'a rike da takkuba da kulake. Manyan firistoci da malaman attaura da shugabanni suka turo su.
Immediately, as he was still speaking, Judas arrived, who was one of the twelve. With him was a large crowd with swords and clubs, sent by the chief priests, the scribes, and the elders.
44 Mai bashe shi din nan ya riga ya kulla da su cewa “Wanda zan yi wa sumba shine mutumin, ku kama shi ku tafi da shi a tsare.
Now his betrayer had given them a signal, saying, “Whomever I kiss, he is the one; arrest him and lead him away under guard.”
45 Da isowarsa kuwa, sai ya zo wurin Yesu ya ce “Ya malam!”. Sai ya sumbace shi.
When Judas came, he immediately went up to Jesus and said to him, “Rabbi! Rabbi!” And he kissed him.
46 Su kuwa suka kama shi, suka tafi da shi.
Then they took hold of Jesus and arrested him.
47 Amma daya daga cikin na tsaye ya zaro takobinsa ya kai wa bawan babban firist sara, ya yanke masa kunne.
But one of the bystanders drew his sword and struck the servant of the high priest, cutting off his ear.
48 Sai Yesu ya ce “kun fito kamar masu kama yan fashi da takkuba da kulake, domin ku kama ni?
Then Jesus said to them, “Have you come out to arrest me with swords and clubs as you would against a robber?
49 Lokacin da nake koyarwa a Haikali, kowace rana da ku, baku kama ni ba. Amma anyi haka ne domin a cika abinda Nassi ya fada.”
I was with you daily, teaching in the temple courts, and you did not arrest me. But these things are happening so that the Scriptures may be fulfilled.”
50 Daga nan duk wadanda suke tare da Yesu suka yashe shi, suka tsere.
Then they all the disciples left him and fled.
51 Wani saurayi, daga shi sai mayafi ya bi shi, suka kai masa cafka.
Now a certain young man was following Jesus, wearing nothing but a linen cloth. The young men tried to seize him,
52 Shi kuwa ya bar masu mayafin ya gudu tsirara.
but he left the linen cloth behind and ran away from them naked.
53 Daga nan suka tafi da Yesu wurin babban firist. a can suka tara dattawa duk da manyan firistoci da shugabanni da marubuta, suka taru a wurinsa.
Then they led Jesus away to the high priest, and all the chief priests, the elders, and the scribes were assembled together with him.
54 Bitrus kuwa ya bi shi daga nesa har cikin gidan babban firist. Ya zauna tare da dogaran Haikalin, yana jin dumin wuta.
Peter had followed Jesus at a distance, right into the courtyard of the high priest. There he sat with the officers, warming himself in the light of the fire.
55 Sai, manyan firistoci da duk 'yan majalisa Yahudawa suka nemi shaidar da za a tabbatar a kan Yesu, don su samu su kashe shi. Amma basu samu ba.
Now the chief priests and the whole Sanhedrin were seeking testimony against Jesus so that they could put him to death, but they did not find any.
56 Da yawa kuma suka yi masa shaidar Zur (Karya), amma bakin su bai zama daya ba.
For many were giving false testimony against him, but their testimonies did not agree.
57 Sai wadansu kuma suka taso suka yi masa shaidar zur (karya) suka ce.
Then some stood up and gave false testimony against him, declaring,
58 “Mun ji ya ce, wai zai rushe haikalin nan da mutane suka gina, ya sake gina wani cikin kwana uku, ba kuwa ginin mutum ba”.
“We heard him say, ‘I will destroy this man-made temple, and in three days I will build another not made by man.’”
59 Duk da haka, sai shaidar tasu bata zo daya ba.
Yet even then their testimony did not agree.
60 Sai babban firist ya mike a tsakanin su, ya tambayi Yesu yace “Ba ka da wata amsa game da shaidar da mutanen nan suke yi a kanka?
Then the high priest stood up before them and asked Jesus, “Do yoʋ make no answer? What are these men testifying against yoʋ?”
61 Amma yayi shiru abinsa, bai ce kome ba. Sai babban firist din ya sake tambayarsa “To, ashe kai ne Allmasihu Dan Madaukaki?
But he was silent and made no answer. Again the high priest asked him, “Are yoʋ the Christ, the Son of the Blessed One?”
62 Yesu ya ce “Nine. Za ku kuwa ga Dan Mutum zaune dama ga mai iko, yana kuma zuwa cikin gajimare”.
Jesus said, “I am. And you will see the Son of Man sitting at the right hand of Power and coming with the clouds of heaven.”
63 Sai babban firist ya kyakketa tufafinsa yace “Wacce shaida kuma zamu nema?
Then the high priest tore his garments and said, “What further need do we have of witnesses?
64 Kun dai ji sabon da yayi! Me kuka gani? Duk suka yanke masa hukunci akan ya cancanci kisa.
You have heard his blasphemy. What seems right to you?” And they all condemned him as deserving death.
65 Wadansu ma suka fara tottofa masa yau, suka daure masa idanu, suka bubbuge shi suna cewa “Yi annabci” Dogaran kuma suka yi ta marinsa.
Then some began to spit on him, to blindfold him, and to beat him, saying to him, “Prophesy!” And the officers kept striking him with the palms of their hands.
66 Bitrus kuwa na kasa a filin gida, sai wata baranyar babban firist ta zo.
Now as Peter was in the courtyard below, one of the servant girls of the high priest came.
67 Da ta ga Bitrus na jin dumi, ta yi masa kallon gaske ta ce “Kaima ai tare kake da banazaren nan Yesu”.
When she saw Peter warming himself, she looked at him and said, “Yoʋ also were with Jesus of Nazareth.”
68 Amma ya musa ya ce “Ni ban ma san abinda kike fada ba balle in fahimta”. Sai ya fito zaure. Sai zakara yayi cara.
But he denied it, saying, “I neither know nor understand what yoʋ are talking about!” Then he went outside to the gateway, and a rooster crowed.
69 Sai baranyar ta ganshi, ta sake ce wa wadanda ke tsaitsaye a wurin, “Wannan ma daya daga cikinsu ne”.
When the servant girl saw him again, she began saying to the people standing nearby, “This man is one of them.”
70 Amma ya sake musawa, jim kadan sai na tsaitsayen suka ce wa Bitrus “Lalle kai ma dayansu ne don ba Galile ne kai”.
But again he denied it. After a little while, the people standing nearby said to Peter once again, “Truly yoʋ are one of them, for yoʋ also are a Galilean, and yoʋr accent is like theirs.”
71 Sai ya fara la'anta kansa yana ta rantsuwa yana ce wa “Ban ma san mutumin nan da kuke fada ba”.
But he began to invoke curses and to swear, saying, “I do not know this man of whom you speak.”
72 Nan da nan sai zakara ya yi cara ta biyu, Bitrus kuwa ya tuna da maganar Yesu a gare shi cewa “Kafin zakara ya yi cara ta biyu, za ka yi musun sani na sau uku”. Da ya tuno haka, sai ya fashe da kuka.
Then a rooster crowed a second time, and Peter remembered what Jesus had said to him: “Before a rooster crows twice, yoʋ will deny me three times.” And he broke down and wept.

< Markus 14 >