< Markus 13 >

1 da Yesu ke fita daga Haikalin, sai daya daga cikin almajirnsa ya ce masa “malam, dubi kyawawan duwatsunnan da kyawawan gine-ginnenan!”
Καὶ ἐκπορευομένου αὐτοῦ ἐκ τοῦ ἱεροῦ λέγει αὐτῷ εἷς τῶν μαθητῶν αὐτοῦ· Διδάσκαλε, ἴδε ποταποὶ λίθοι καὶ ποταπαὶ οἰκοδομαί.
2 Ya ce masa, ka ga wadannan kyawawan gine- ginen? babu wani dutsen da za a bar shi akan dan'uwansa, da ba za a rushe shi ba.”
καὶ ὁ ⸀Ἰησοῦςεἶπεν αὐτῷ· Βλέπεις ταύτας τὰς μεγάλας οἰκοδομάς; οὐ μὴ ἀφεθῇ ⸀ὧδελίθος ἐπὶ ⸀λίθονὃς οὐ μὴ καταλυθῇ.
3 Yana zaune a kan dutsen zaitun wanda yake kusa da Haikali, sai Bitrus, da Yakubu, da Yahaya, da Andarawus suka tambaye shi a asirce, suka ce.
Καὶ καθημένου αὐτοῦ εἰς τὸ Ὄρος τῶν Ἐλαιῶν κατέναντι τοῦ ἱεροῦ ⸀ἐπηρώτααὐτὸν κατʼ ἰδίαν Πέτρος καὶ Ἰάκωβος καὶ Ἰωάννης καὶ Ἀνδρέας·
4 Gaya mana yaushe za a yi wadannan abubuwa? mecece zata zama alamar faruwar wadanna abubuwa da zasu faru?''
Εἰπὸν ἡμῖν πότε ταῦτα ἔσται, καὶ τί τὸ σημεῖον ὅταν μέλλῃ ⸂ταῦτα συντελεῖσθαι πάντα.
5 Yesu ya ce masu, “ku kula, kada kowa ya rudeku.
ὁ δὲ Ἰησοῦς ⸂ἤρξατο λέγειν αὐτοῖς· Βλέπετε μή τις ὑμᾶς πλανήσῃ·
6 Da yawa za su zo da sunana, suna cewa nine shi, har su bad da mutane da yawa.
⸀πολλοὶἐλεύσονται ἐπὶ τῷ ὀνόματί μου λέγοντες ὅτι Ἐγώ εἰμι, καὶ πολλοὺς πλανήσουσιν.
7 In kuka ji labarin yake- yake, da jita-jitarsu kada ku damu, wannan zai faru, amma karshen duniya bai gabato ba.
ὅταν δὲ ⸀ἀκούσητεπολέμους καὶ ἀκοὰς πολέμων, μὴ θροεῖσθε· ⸀δεῖγενέσθαι, ἀλλʼ οὔπω τὸ τέλος.
8 Al'umma za ta tasarwa al'umma, mulki ya tasarwa mulki. Za a yi girgizar kasa awurare dabam-dabam, da kuma yunwa, amma fa dukkan wadanna abubuwan mafarin azaba ne.
ἐγερθήσεται γὰρ ἔθνος ἐπʼ ἔθνος καὶ βασιλεία ἐπὶ βασιλείαν, ⸀ἔσονταισεισμοὶ κατὰ τόπους, ⸁ἔσονται⸀λιμοί ⸀ἀρχὴὠδίνων ταῦτα.
9 Amma, ku zauna a fadake. Don za su kai ku gaban majalisa. za a yi maku duka a cikin majami'u. Su kuma kai ku gaban masu mulki da sarakuna, saboda sunana, domin ku ba da shaida a gare su.
βλέπετε δὲ ὑμεῖς ἑαυτούς· ⸀παραδώσουσινὑμᾶς εἰς συνέδρια καὶ εἰς συναγωγὰς δαρήσεσθε καὶ ἐπὶ ἡγεμόνων καὶ βασιλέων σταθήσεσθε ἕνεκεν ἐμοῦ εἰς μαρτύριον αὐτοῖς.
10 Amma lallai sai an fara yi wa dukkan al, ummai bishara.
καὶ εἰς πάντα τὰ ἔθνη ⸂πρῶτον δεῖ κηρυχθῆναι τὸ εὐαγγέλιον.
11 Sa'ad da suka kai ku gaban shari'a suka mika ku, kada ku damu a wannan lokacin, za a baku abin da zaku fada, Amma duk abin da aka yi muku a wannn lokacin, shi za ku fada, domin ba ku ne kuke magana ba, Ruhu mai tsarki ne.
⸂καὶ ὅταν ⸀ἄγωσινὑμᾶς παραδιδόντες, μὴ προμεριμνᾶτε τί ⸀λαλήσητε ἀλλʼ ὃ ἐὰν δοθῇ ὑμῖν ἐν ἐκείνῃ τῇ ὥρᾳ τοῦτο λαλεῖτε, οὐ γάρ ἐστε ὑμεῖς οἱ λαλοῦντες ἀλλὰ τὸ πνεῦμα τὸ ἅγιον.
12 Dan'uwa zai bada dan'uwarsa akashe shi, uba kuwa dansa. Yara kuma zasu tayar wa iyayensu har su sa akashe su.
⸂καὶ παραδώσει ἀδελφὸς ἀδελφὸν εἰς θάνατον καὶ πατὴρ τέκνον, καὶ ἐπαναστήσονται τέκνα ἐπὶ γονεῖς καὶ θανατώσουσιν αὐτούς·
13 Za a ki ku saboda sunana, amma duk wanda ya jumre har karshe zai cetu.
καὶ ἔσεσθε μισούμενοι ὑπὸ πάντων διὰ τὸ ὄνομά μου. ὁ δὲ ὑπομείνας εἰς τέλος οὗτος σωθήσεται.
14 Sa'adda kuka ga an kafa mummunan aikin sabo mai ban kyama a wurin da bai kamata ba (bari mai karatu ya fahimta), to, bari wadanda suke kasar Yahudiya, su gudu zuwa dutse.
Ὅταν δὲ ἴδητε τὸ βδέλυγμα τῆς ἐρημώσεως ⸀ἑστηκόταὅπου οὐ δεῖ, ὁ ἀναγινώσκων νοείτω, τότε οἱ ἐν τῇ Ἰουδαίᾳ φευγέτωσαν εἰς τὰ ὄρη,
15 Wanda yake tudu kuma kada ya sauko ya shiga gida garin daukar wani abu.
⸀ὁἐπὶ τοῦ δώματος μὴ ⸀καταβάτωμηδὲ εἰσελθάτω ⸂τι ἆραι ἐκ τῆς οἰκίας αὐτοῦ,
16 Wanda yake gona kuma kada ya koma garin daukar mayafinsa.
καὶ ὁ εἰς τὸν ⸀ἀγρὸνμὴ ἐπιστρεψάτω εἰς τὰ ὀπίσω ἆραι τὸ ἱμάτιον αὐτοῦ.
17 Amma, kaiton masu juna biyu da masu goyo a wannan lokacin.
οὐαὶ δὲ ταῖς ἐν γαστρὶ ἐχούσαις καὶ ταῖς θηλαζούσαις ἐν ἐκείναις ταῖς ἡμέραις.
18 Ku yi addu, a kada abin ya faru da damina.
προσεύχεσθε δὲ ἵνα μὴ ⸀γένηταιχειμῶνος·
19 A lokacin za ayi wata matsanaciyar wahala, wadda bata taba faruwa ba, tun farkon halittar da Allah ya yi har zuwa yau, ba kuwa za a taba yi ba har abada.
ἔσονται γὰρ αἱ ἡμέραι ἐκεῖναι θλῖψις οἵα οὐ γέγονεν τοιαύτη ἀπʼ ἀρχῆς κτίσεως ⸀ἣνἔκτισεν ὁ θεὸς ἕως τοῦ νῦν καὶ οὐ μὴ γένηται.
20 In da ba ubangiji ya rage kwanakin nan ba, da ba Dan adam din zai tsira. Amma saboda zabbabunan da ya zaba, ya rage kwanakin.
καὶ εἰ μὴ ⸂ἐκολόβωσεν κύριος τὰς ἡμέρας, οὐκ ἂν ἐσώθη πᾶσα σάρξ. ἀλλὰ διὰ τοὺς ἐκλεκτοὺς οὓς ἐξελέξατο ἐκολόβωσεν τὰς ἡμέρας.
21 To, in wani ya ce maku, kun ga Almasihu nan!' ko, 'kun gan shi can, kada ku gaskata.
⸀καὶτότε ἐάν τις ὑμῖν εἴπῃ· ⸀Ἴδεὧδε ὁ ⸀χριστός ⸁Ἴδεἐκεῖ, μὴ πιστεύετε·
22 Gama almasihan karya, da annabawan karya zasu bayyana kuma, zasu yi abubuwan al'ajibai masu ban mamaki.
ἐγερθήσονται γὰρ ψευδόχριστοι καὶ ψευδοπροφῆται καὶ δώσουσιν σημεῖα καὶ τέρατα πρὸς τὸ ἀποπλανᾶν εἰ ⸀δυνατὸντοὺς ἐκλεκτούς·
23 Amma ku zauna a fadake, Na dai fada maku wadannan abubuwan kafin lokacin.
ὑμεῖς δὲ βλέπετε· ⸀προείρηκαὑμῖν πάντα.
24 Amma, bayan matsanaciyar wahalannan, rana zata duhunta, wata kuma ba zai bada haske ba.
Ἀλλὰ ἐν ἐκείναις ταῖς ἡμέραις μετὰ τὴν θλῖψιν ἐκείνην ὁ ἥλιος σκοτισθήσεται, καὶ ἡ σελήνη οὐ δώσει τὸ φέγγος αὐτῆς,
25 Taurari za su fado daga sararin sama, za a kuma girgiza manyan abubuwan da suke a sararin sama.
καὶ οἱ ἀστέρες ⸂ἔσονται ἐκ τοῦ οὐρανοῦ πίπτοντες, καὶ αἱ δυνάμεις αἱ ἐν τοῖς οὐρανοῖς σαλευθήσονται.
26 Sa' annan zasu ga Dan mutum na zuwa a cikin gajimare, da iko mai girma da daukaka.
καὶ τότε ὄψονται τὸν υἱὸν τοῦ ἀνθρώπου ἐρχόμενον ἐν νεφέλαις μετὰ δυνάμεως πολλῆς καὶ δόξης·
27 Zai aiko da mala'ikunsa su tattaro zabbabunsa daga kusuwoyi hudu na duniya(watau Gabas da Yamma, kudu da Arewa) har zuwa karshen sama.
καὶ τότε ἀποστελεῖ τοὺς ⸀ἀγγέλουςκαὶ ἐπισυνάξει τοὺς ⸀ἐκλεκτοὺςἐκ τῶν τεσσάρων ἀνέμων ἀπʼ ἄκρου γῆς ἕως ἄκρου οὐρανοῦ.
28 “Ku yi koyi da itacen baure. Da zarar rassansa sun fara taushi yana kuma fitar da toho, kun san damina ta yi kusa ke nan.
Ἀπὸ δὲ τῆς συκῆς μάθετε τὴν παραβολήν· ὅταν ⸂ἤδη ὁ κλάδος αὐτῆς ἁπαλὸς γένηται καὶ ἐκφύῃ τὰ φύλλα, γινώσκετε ὅτι ἐγγὺς τὸ θέρος ἐστίν·
29 Sa'adda kuka ga wadannan abubuwa suna faruwa, ku dai sani ya kusato, a bakin kofa ma ya ke.
οὕτως καὶ ὑμεῖς, ὅταν ⸂ἴδητε ταῦτα γινόμενα, γινώσκετε ὅτι ἐγγύς ἐστιν ἐπὶ θύραις.
30 Hakika ina gaya maku, zamanin nan ba zai shude ba sai dukan abubuwan nan sun faru.
ἀμὴν λέγω ὑμῖν ὅτι οὐ μὴ παρέλθῃ ἡ γενεὰ αὕτη μέχρις οὗ ⸂ταῦτα πάντα γένηται.
31 Sararin sama da kasa za su shude, amma maganata ba za ta shude ba.
ὁ οὐρανὸς καὶ ἡ γῆ ⸀παρελεύσονται οἱ δὲ λόγοι μου οὐ ⸀μὴ⸁παρελεύσονται
32 Amma wannan rana ko sa'a ba wanda ya sani, ko mala'ikun sama, ko Dan, sai dai Uban kadai.
Περὶ δὲ τῆςἡμέρας ἐκείνης ἢ ⸀τῆς ὥρας οὐδεὶς οἶδεν, οὐδὲ οἱ ἄγγελοι ⸀ἐνοὐρανῷ οὐδὲ ὁ υἱός, εἰ μὴ ὁ πατήρ.
33 Ku kula, ku zauna a fadake, kuna addu'a don baku san ranar da lokacin zai yi ba.
βλέπετε ⸀ἀγρυπνεῖτε οὐκ οἴδατε γὰρ πότε ὁ καιρός ἐστιν·
34 Kamar yadda mutum mai tafiya, in ya bar gida ya wakilta bayinsa kan gidansa, kowanne da aikinsa, ya kuma umarci mai gadi ya zauna a fadake.
ὡς ἄνθρωπος ἀπόδημος ἀφεὶς τὴν οἰκίαν αὐτοῦ καὶ δοὺς τοῖς δούλοις αὐτοῦ τὴν ἐξουσίαν, ⸀ἑκάστῳτὸ ἔργον αὐτοῦ, καὶ τῷ θυρωρῷ ἐνετείλατο ἵνα γρηγορῇ.
35 To, ku zauna a fadake don ba ku san lokacin da maigidan zai zo ba, ko da yamma ne, ko da tsakar dare ne, ko da carar zakara ne, ko da safe ne.
γρηγορεῖτε οὖν, οὐκ οἴδατε γὰρ πότε ὁ κύριος τῆς οἰκίας ἔρχεται, ⸀ἢὀψὲ ἢ ⸀μεσονύκτιονἢ ἀλεκτοροφωνίας ἢ πρωΐ,
36 Kada ya zo ba zato, ya samu kuna barci.
μὴ ἐλθὼν ἐξαίφνης εὕρῃ ὑμᾶς καθεύδοντας·
37 Abinda na gaya maku, ina gaya wa kowa, shine ku zauna a fadake!”
⸀ὃδὲ ὑμῖν λέγω πᾶσιν λέγω· γρηγορεῖτε.

< Markus 13 >