< Markus 11 >

1 Da suka kusa Urushalima, kusa da Betafaji, da Betanya, wajen dutsen zaitun, sai Yesu ya aiki almajiransa biyu
Καὶ ὅτε ἐγγίζουσιν εἰς Ἱερουσαλὴμ εἰς Βηθσφαγῆ καὶ Βηθανίαν πρὸς τὸ ὄρος τῶν ἐλαιῶν, ἀποστέλλει δύο τῶν μαθητῶν αὐτοῦ
2 ya ce masu, “ku shiga kauyen can kusa da mu. Da zarar kun shiga za ku ga aholaki a daure, wanda ba a taba hawa ba. Ku kwance shi, ku kawo mani.
καὶ λέγει αὐτοῖς· ὑπάγετε εἰς τὴν κώμην τὴν κατέναντι ὑμῶν, καὶ εὐθέως εἰσπορευόμενοι εἰς αὐτὴν εὑρήσετε πῶλον δεδεμένον, ἐφ᾽ ὃν οὐδεὶς ἀνθρώπων κεκάθικε· λύσαντες αὐτὸν ἀγάγετε.
3 In wani ya ce maku, “Don me kuke haka? ku ce, 'Ubangiji ne yake bukatarsa, zai kuma komo da shi nan da nan.”'
καὶ ἐάν τις ὑμῖν εἴπῃ· τί ποιεῖτε τοῦτο; εἴπατε ὅτι ὁ Κύριος αὐτοῦ χρείαν ἔχει, καὶ εὐθέως αὐτὸν ἀποστέλλει πάλιν ὧδε.
4 Sai suka tafi, suka tadda aholakin a daure a kofar gida a bakin hanya, suka kwance shi.
ἀπῆλθον δὲ καὶ εὗρον τὸν πῶλον δεδεμένον πρὸς τὴν θύραν ἔξω ἐπὶ τοῦ ἀμφόδου, καὶ λύουσιν αὐτόν.
5 sai wadanda suke tsaye a gun suka ce masu, “Don me kuke kwance aholakin nan?
καί τινες τῶν ἐκεῖ ἑστηκότων ἔλεγον αὐτοῖς· τί ποιεῖτε λύοντες τὸν πῶλον;
6 Suka fada masu abinda Yesu yace, sai suka kyale su suka tafi.
οἱ δὲ εἶπον αὐτοῖς καθὼς ἐνετείλατο ὁ Ἰησοῦς, καὶ ἀφῆκαν αὐτούς.
7 Almajiran nan biyu suka kawo wa Yesu aholakin, suka shimfida mayafansu a kai, sai ya hau.
καὶ ἤγαγον τὸν πῶλον πρὸς τὸν Ἰησοῦν καὶ ἐπέβαλον αὐτῷ τὰ ἱμάτια αὐτῶν, καὶ ἐκάθισεν ἐπ᾽ αὐτῷ.
8 Sai mutane da yawa suka shimfida mayafansu a hanya, wadansu kuma suka baza ganyen da suka yanko daga filayen.
πολλοὶ δὲ τὰ ἱμάτια αὐτῶν ἔστρωσαν εἰς τὴν ὁδόν, ἄλλοι δὲ στοιβάδας ἔκοπτον ἐκ τῶν δένδρων καὶ ἐστρώννυον εἰς τὴν ὁδόν.
9 Wadanda suke gaba da shi da wadanda ke bin bayansa suka yi sowa suna cewa, “Hosanna! Albarka ta tabbata ga mai zuwa cikin sunan Ubangiji.
καὶ οἱ προάγοντες καὶ οἱ ἀκολουθοῦντες ἔκραζον λέγοντες· ὡσαννά, εὐλογημένος ὁ ἐρχόμενος ἐν ὀνόματι Κυρίου.
10 Albarka ta tabbata ga mulkin nan mai zuwa na Ubanmu Dawuda! Dukaka a cikin sama!”
εὐλογημένη ἡ ἐρχομένη βασιλεία ἐν ὀνόματι Κυρίου τοῦ πατρός ἡμῶν Δαυΐδ· ὡσαννὰ ἐν τοῖς ὑψίστοις.
11 San nan Yesu ya shiga Urushalima, ya shiga Haikalin. Sai ya dudduba komai, da magariba ta yi, ya fita ya tafi Betanya tare da goma sha biyu nan.
Καὶ εἰσῆλθεν εἰς Ἱεροσόλυμα ὁ Ἰησοῦς καὶ εἰς τὸ ἱερόν· καὶ περιβλεψάμενος πάντα, ὀψίας ἤδη οὔσης τῆς ὥρας, ἐξῆλθεν εἰς Βηθανίαν μετὰ τῶν δώδεκα.
12 Kashe gari, suka tashi daga Betanya, sai ya ji yunwa.
Καὶ τῇ ἐπαύριον ἐξελθόντων αὐτῶν ἀπὸ Βηθανίας ἐπείνασε·
13 Da ya hango itacen baure mai ganye daga nesa sai ya je ya ga ko za sami 'ya'ya. Da ya iso wurinsa bai ga komai ba sai ganye, don ba lokacin 'ya'yan baure ba ne.
καὶ ἰδὼν συκῆν ἀπὸ μακρόθεν ἔχουσαν φύλλα, ἦλθεν εἰ ἄρα τι εὑρήσει ἐν αὐτῇ· καὶ ἐλθὼν ἐπ᾽ αὐτὴν οὐδὲν εὗρεν εἰ μὴ φύλλα· οὐ γὰρ ἦν καιρὸς σύκων.
14 Sai ya ce wa bauren, “Kada kowa ya kara cin ''ya'yanka har abada!” Almajiransa kuwa sun ji maganar. (aiōn g165)
καὶ ἀποκριθεὶς εἶπεν αὐτῇ· μηκέτι ἐκ σοῦ εἰς τὸν αἰῶνα μηδεὶς καρπὸν φάγοι. καὶ ἤκουον οἱ μαθηταὶ αὐτοῦ. (aiōn g165)
15 Suka iso Urushalima, da shigar su, ya kori masu saye da sayarwa, ya watsar da taburan 'yan canjin kudi, da kujerun masu sayar da tantabaru.
Καὶ ἔρχονται πάλιν εἰς Ἱεροσόλυμα· καὶ εἰσελθὼν ὁ Ἰησοῦς εἰς τὸ ἱερὸν ἤρξατο ἐκβάλλειν τοὺς πωλοῦντας καὶ τοὺς ἀγοράζοντας ἐν τῷ ἱερῷ, καὶ τὰς τραπέζας τῶν κολλυβιστῶν καὶ τὰς καθέδρας τῶν πωλούντων τὰς περιστερὰς κατέστρεψε,
16 Ya hana kowa ya dauki wani abu da za a i ya sayarwa a cikin haikalin.
καὶ οὐκ ἤφιεν ἵνα τις διενέγκῃ σκεῦος διὰ τοῦ ἱεροῦ,
17 Sai ya koyar da su cewa, “Ashe ba rubuce yake ba, “Za a kira gidana gidan addu'a na dukan al'ummai? Amma ku kun mayar da shi kogon yan fashi”.
καὶ ἐδίδασκε λέγων αὐτοῖς· οὐ γέγραπται ὅτι ὁ οἶκός μου οἶκος προσευχῆς κληθήσεται πᾶσι τοῖς ἔθνεσιν; ὑμεῖς δὲ αὐτὸν ἐποιήσατε σπήλαιον λῃστῶν.
18 Da mayan Faristoci da marubutan attaura suka ji maganar da ya yi, sai suka nami hanyar da za su kashe shi. Amma suka ji tsoronsa domin dukkan taron na mamakin koyarwarsa.
καὶ ἤκουσαν οἱ γραμματεῖς καὶ οἱ Φαρισαῖοι καὶ οἱ ἀρχιερεῖς, καὶ ἐζήτουν πῶς αὐτὸν ἀπολέσωσιν· ἐφοβοῦντο γὰρ αὐτόν, ὅτι πᾶς ὁ ὄχλος ἐξεπλήσσετο ἐπὶ τῇ διδαχῇ αὐτοῦ.
19 Kowace yamma kuma, sukan fita gari.
καὶ ὅτε ὀψὲ ἐγένετο, ἐξεπορεύετο ἔξω τῆς πόλεως.
20 Da safe suna wucewa, sai suka ga bauren nan ya bushe.
Καὶ παραπορευόμενοι πρωῒ εἶδον τὴν συκῆν ἐξηραμμένην ἐκ ῥιζῶν.
21 Bitrus kuwa ya tuna ya ce “Malam, dubi! Baurenan da ka la'anta ya bushe.”
καὶ ἀναμνησθεὶς ὁ Πέτρος λέγει αὐτῷ· ῥαββί, ἴδε ἡ συκῆ ἣν κατηράσω ἐξήρανται.
22 Yesu ya amsa masu ya ce, “ku gaskata da Allah.”
καὶ ἀποκριθεὶς ὁ Ἰησοῦς λέγει αὐτοῖς· ἔχετε πίστιν Θεοῦ.
23 Hakika, ina gaya maku, duk wanda ya ce wa dutsen nan tashi ka fada cikin tekun', bai kuwa yi shakka a zuciyarsa ba, amma ya gaskata haka kuwa zai faru, haka kuwa Allah zai yi.
ἀμὴν γὰρ λέγω ὑμῖν ὅτι ὃς ἂν εἴπῃ τῷ ὄρει τούτῳ, ἄρθητι καὶ βλήθητι εἰς τὴν θάλασσαν, καὶ μὴ διακριθῇ ἐν τῇ καρδίᾳ αὐτοῦ, ἀλλὰ πιστεύσει ὅτι ἃ λέγει γίνεται, ἔσται αὐτῷ ὃ ἐὰν εἴπῃ.
24 Saboda haka ina dai gaya maku, komai kuka yi addu'a kuka roka, ku gaskata cewa samamme ne, zai kuma zama naku.
διὰ τοῦτο λέγω ὑμῖν, πάντα ὅσα ἂν προσευχόμενοι αἰτεῖσθε, πιστεύετε ὅτι λαμβάνετε, καὶ ἔσται ὑμῖν.
25 Duk sa'add da kuke addu'a ku gafarta wa wadanda suka yi maku laifi, domin Ubanku shima zai gafarta maku naku laifi.”
καὶ ὅταν στήκητε προσευχόμενοι, ἀφίετε εἴ τι ἔχετε κατά τινος, ἵνα καὶ ὁ πατὴρ ὑμῶν ὁ ἐν τοῖς οὐρανοῖς ἀφῇ ὑμῖν τὰ παραπτώματα ὑμῶν.
26 (Amma in baku gafartawa mutane laifofinsu ba, Ubanku ma da ke sama ba zai gafarta maku ba.)
εἰ δὲ ὑμεῖς οὐκ ἀφίετε, οὐδὲ ὁ πατὴρ ὑμῶν ἀφήσει τὰ παραπτώματα ὑμῶν.
27 Da suka sake dawowa Urushalima. Yasu na tafiya cikin haikali, sai manyan firistoci, da marubuta, da dattawa suka zo wurinsa,
Καὶ ἔρχονται πάλιν εἰς Ἱεροσόλυμα· καὶ ἐν τῷ ἱερῷ περιπατοῦντος αὐτοῦ ἔρχονται πρὸς αὐτὸν οἱ ἀρχιερεῖς καὶ οἱ γραμματεῖς καὶ οἱ πρεσβύτεροι
28 suka ce masa, “Da wanne iko kake yin wadanan abubuwa? Ko kuwa wa ya ba ka ikon yinsu? “
καὶ λέγουσιν αὐτῷ· ἐν ποίᾳ ἐξουσίᾳ ταῦτα ποιεῖς; ἢ τίς σοι ἔδωκε τὴν ἐξουσίαν ταύτην ἵνα ταῦτα ποιῇς;
29 Sai Yesu ya ce masu, “Zan yi maku wata tambaya. ku ba ni amsa, ni kuwa zan gaya maku ko da wanne iko ne nake yin wadannan abubuwan.
ὁ δὲ Ἰησοῦς ἀποκριθεὶς εἶπεν αὐτοῖς· ἐπερωτήσω ὑμᾶς κἀγὼ ἕνα λόγον, καὶ ἀποκρίθητέ μοι, καὶ ἐρῶ ὑμῖν ἐν ποίᾳ ἐξουσίᾳ ταῦτα ποιῶ.
30 Baftismar da Yahaya yayi, daga sama take ko kuwa daga mutum take? ku bani amsa”.
τὸ βάπτισμα Ἰωάννου ἐξ οὐρανοῦ ἦν ἢ ἐξ ἀνθρώπων; ἀποκρίθητέ μοι.
31 Sai suka yi mahuwara da juna, suka ce, “in kuwa muka ce, 'daga sama take,' za ya ce, “To, don me ba ku gaskata shi ba?
καὶ ἐλογίζοντο πρὸς ἑαυτοὺς λέγοντες· ἐὰν εἴπωμεν, ἐξ οὐρανοῦ, ἐρεῖ· διατί οὖν οὐκ ἐπιστεύσατε αὐτῷ;
32 In kuwa muka ce, “amma in muka ce ta mutum ce zasu jejjefemu domi suna jin tsoron jama'a, don duk kowa ya tabbata, cewa Yahaya annabi ne.
ἀλλὰ εἴπωμεν, ἐξ ἀνθρώπων; — ἐφοβοῦντο τὸν λαόν· ἅπαντες γὰρ εἶχον τὸν Ἰωάννην ὅτι προφήτης ἦν.
33 Sai suka amsa wa Yesu suka ce, “Ba mu sani ba” Yesu ya ce masu, “Haka ni kuma ba zan fada muku ko da wanne iko nake yin abubuwan nan ba.”
καὶ ἀποκριθέντες λέγουσι τῷ Ἰησοῦ· οὐκ οἴδαμεν. καὶ ὁ Ἰησοῦς ἀποκριθεὶς λέγει αὐτοῖς· οὐδὲ ἐγὼ λέγω ὑμῖν ἐν ποίᾳ ἐξουσίᾳ ταῦτα ποιῶ.

< Markus 11 >