< Markus 10 >
1 Yesu ya bar wannan wurin, ya tafi yankin Yahudiya, wajen hayin kogin Urdun. Sai jama'a suka je wurinsa. Ya ci gaba da koya masu, kamar yadda ya zama al'adarsa.
Et inde exurgens venit in fines Iudææ ultra Iordanem: et conveniunt iterum turbæ ad eum: et sicut consueverat, iterum docebat illos.
2 Sai Farisawa su ka zo wurinsa, su ka ce, '' dai dai ne mutum ya saki matarsa?'' Wannan tambaya sun yi ta ne domin su gwada shi.
Et accedentes Pharisæi interrogabant eum: Si licet viro uxorem dimittere: tentantes eum.
3 Ya amsa ya ce, menene Musa ya umarce ku?
At ille respondens, dixit eis: Quid vobis præcepit Moyses?
4 Suka ce, ''Musa ya yarda mutum ya rubuta takardar saki ga matarsa, ya sallameta ta fita.''
Qui dixerunt: Moyses permisit libellum repudii scribere, et dimittere.
5 “Domin taurin zuciyarku ne ya rubuta maku wannan dokar,” Yesu ya ce masu.
Quibus respondens Iesus, ait: Ad duritiam cordis vestri scripsit vobis præceptum istud.
6 Amman tun daga farkon halitta, 'Allah ya halicci namiji da ta mata.'
Ab initio autem creaturæ masculum, et feminam fecit eos Deus.
7 Domin wannan dalilin ne mutum zai rabu mahaifinsa da mahaifiyarsa ya mannewa matarsa.
Propter hoc relinquet homo patrem suum, et matrem, et adhærebit ad uxorem suam:
8 Su biyu kuwa sun zama jiki daya, ba biyu ba,
et erunt duo in carne una. Itaque iam non sunt duo, sed una caro.
9 Saboda haka abinda Allah ya hada kada mutum ya raba.”
Quod ergo Deus coniunxit, homo non separet.
10 Lokacin da suke cikin gida, sai almajiransa suka sake tambayarsa akan wannan magana.
Et in domo iterum discipuli eius de eodem interrogaverunt eum.
11 Ya ce da su. Dukan wanda ya saki matarsa ya kuma auro wata matar yayi zina da ita kenan.
Et ait illis: Quicumque dimiserit uxorem suam, et aliam duxerit, adulterium committit super eam.
12 Haka nan duk matar da ta saki mijinta ta auri wani ta yi zina da shi kenan.”
Et si uxor dimiserit virum suum, et alii nupserit, mœchatur.
13 Mutane suka kawo masa 'ya'yansu kanana don ya taba su, sai almajiransa suka kwabe su.
Et offerebant illi parvulos ut tangeret illos. Discipuli autem comminabantur offerentibus.
14 Da Yesu ya gani, ya ji haushi, ya ce masu. Ku bar yara kanana su zo wurina, kada ku hana su domin mulkin Allah na irinsu ne.
Quos cum videret Iesus, indigne tulit, et ait illis: Sinite parvulos venire ad me, et ne prohibueritis eos: talium enim est regnum Dei.
15 Gaskiya na ke fada maku duk mutumin da bai karbi mulkin Allah kamar karamin yaro ba, babu shakka ba zai shiga mulkin Allah ba.
Amen dico vobis: Quisquis non receperit regnum Dei velut parvulus, non intrabit in illud.
16 Sai ya rungume su ya sa masu albarka.
Et complexans eos, et imponens manus super illos, benedicebat eos.
17 Lokacin da ya fara tafiya, sai wani mutum ya rugo wurinsa, ya durkusa a gabansa. Ya tambaye shi, yace ya ''Malam managarci, me zan yi domin in sami rai na har abada?'' (aiōnios )
Et cum egressus esset in viam, procurrens quidam genu flexo ante eum, rogabat eum: Magister bone, quid faciam ut vitam æternam percipiam? (aiōnios )
18 Amma Yesu ya ce masa. Don me ka ke kira na managarci? Babu wani managarci sai dai Allah kadai.
Iesus autem dixit ei: Quid me dicis bonum? Nemo bonus, nisi unus Deus.
19 Kasan dokokin. Kada ka yi kisan kai, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka yi shaidar zur, kada ka yi zamba, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.”
Præcepta nosti: Ne adulteres, Ne occidas, Ne fureris, Ne falsum testimonium dixeris, Ne fraudum feceris, Honora patrem tuum et matrem.
20 Sai mutumin ya ce masa Malam ai na kiyayye duk wadannan abubuwa tun ina yaro.
At ille respondens, ait illi: Magister, hæc omnia observavi a iuventute mea.
21 Yesu ya dube shi duban kauna ya ce masa. Abu daya ka rasa. Shi ne ka je ka sayar da duk mallakarka ka ba mabukata, za ka sami wadata a sama. Sa'annan ka zo ka bi ni.
Iesus autem intuitus eum, dilexit eum, et dixit ei: Unum tibi deest: vade, quæcumque habes vende, et da pauperibus, et habebis thesaurum in cælo: et veni, sequere me.
22 Da ya ji haka sai ransa ya baci, ya tafi yana bakin ciki, don shi mai arziki ne kwarai.
Qui contristatus in verbo, abiit mœrens: erat enim habens multas possessiones.
23 Yesu ya dubi almajiransa ya ce. ''Yana da wuya masu arziki su shiga mulkin Allah!''
Et circumspiciens Iesus, ait discipulis suis: Quam difficile qui pecunias habent, in regnum Dei introibunt!
24 Almajiransa suka yi mamakin maganarsa. Sai Yesu ce masu, ya ku ya'ya'na yana da wuya kamar me a shiga mulkin Allah.
Discipuli autem obstupescebant in verbis eius. At Iesus rursus respondens ait illis: Filioli, quam difficile est, confidentes in pecuniis, in regnum Dei introire!
25 Zai zama da sauki ga rakumi yabi ta kafar allura da mai arziki ya shiga mulkin Allah.
Facilius est, camelum per foramen acus transire, quam divitem intrare in regnum Dei.
26 Sai suka cika da mamaki sosai, su kace wa juna, ''to idan haka ne wanene zai iya tsira kenan?''
Qui magis admirabantur, dicentes ad semetipsos: Et quis potest salvus fieri?
27 Yesu ya dube su ya ce masu. Ga mutane a bu ne mai wuyar gaske, amma a wurin Allah komai yiwuwa ne.
Et intuens illos Iesus, ait: Apud homines impossibile est, sed non apud Deum: omnia enim possibilia sunt apud Deum.
28 Bitrus ya ce masa, ''to gashi mu mun bar kome, mun bika''.
Et cœpit ei Petrus dicere: Ecce nos dimisimus omnia, et secuti sumus te.
29 Yesu ya ce. Gaskiya na ke fada maku, babu wanda zai bar gidansa, da yan'uwansa maza da mata, da mahaifiya ko mahaifi, ko 'ya'ya ko gona, saboda da ni da kuma bishara,
Respondens Iesus, ait: Amen dico vobis: Nemo est, qui reliquerit domum, aut fratres, aut sorores, aut patrem, aut matrem, aut filios, aut agros propter me, et propter Evangelium,
30 sa'annan ya rasa samun nikinsu dari a zamanin yanzu, na gidaje, da yan'uwa mata da maza' da iyaye mata da 'ya'ya da gonaki, game da tsanani, a duniya mai zuw kuma ya sami rai madawwami. (aiōn , aiōnios )
qui non accipiat centies tantum, nunc in tempore hoc: domos, et fratres, et sorores, et matres, et filios, et agros, cum persecutionibus, et in sæculo futuro vitam æternam. (aiōn , aiōnios )
31 Da yawa wadanda suke na farko za su koma na karshe, na karshe kuma za su zama na farko.
Multi autem erunt primi novissimi, et novissimi primi.
32 Suna tafiya Urushalima, Yesu kuwa na gabansu. Almajiransa sun yi mamaki, mutane da ke biye da su kuwa sun tsorata. Yesu kuwa ya sake kebe sha biyun nan, ya fara fada masu abin da zai same shi.
Erant autem in via ascendentes Ierosolymam: et præcedebat illos Iesus, et stupebant: et sequentes timebant. Et assumens iterum duodecim, cœpit illis dicere quæ essent ei eventura.
33 “Kun ga, za mu Urushalima za a bada Dan mutum ga manyan Firistoci da malan Attaura, za su kuma yi masa hukuncin kisa su kuma bada shi ga al'ummai.
Quia ecce ascendimus Ierosolymam, et Filius hominis tradetur principibus sacerdotum, et scribis, et senioribus, et damnabunt eum morte, et tradent eum Gentibus:
34 Za su yi masa ba a, su tofa masa yau, su yi masa bulala, su kashe shi, bayan kwana uku kuwa zai tashi.”
et illudent ei, et conspuent eum, et flagellabunt eum, et interficient eum: et tertia die resurget.
35 Yakubu da Yahaya, 'ya'yan Zabadi, suka zo wurin sa, suka ce, ''Malam muna so kayi mana duk abin da mu ka roke ka''
Et accedunt ad eum Iacobus, et Ioannes filii Zebedæi, dicentes: Magister, volumus ut quodcumque petierimus, facias nobis.
36 Ya ce masu. ''Me ku ke so in yi maku?''
At ille dixit eis: Quid vultis ut faciam vobis?
37 Suka ce, ''ka yardar mana, a ranar daukakarka, mu zauna daya a damanka, daya kuma a hagunka.''
Et dixerunt: Da nobis ut unus ad dexteram tuam, et alius ad sinistram tuam sedeamus in gloria tua.
38 Yesu ya ce masu. ''Ba ku san abinda ku ke roka ba. Kwa iya sha daga kokon da zan sha? Ko kuma za a yi maku baftismar da za a yi mani?''
Iesus autem ait eis: Nescitis quid petatis: potestis bibere calicem, quem ego bibo: aut baptismo, quo ego baptizor, baptizari?
39 Suka fada masa, ''Zamu iya.'' Yesu ya ce masu, '' kokon da zan sha, da shi zaku sha, baftismar da za ayi mani kuma da ita za a yi maku.''
At illi dixerunt ei: Possumus. Iesus autem ait eis: Calicem quidem, quem ego bibo, bibetis; et baptismo, quo ego baptizor, baptizabimini:
40 Amma zama a damata, ko a haguna, ba na wa ba ne da zan bayar, ai na wadanda a ka shiryawa ne.”
sedere autem ad dexteram meam, vel ad sinistram, non est meum dare vobis, sed quibus paratum est.
41 Da sauran almajiran nan goma suka ji, suka fara jin haushin Yakubu da Yahaya.
Et audientes decem cœperunt indignari de Iacobo, et Ioanne.
42 Yesu kuma ya kira su wurinsa ya ce masu, '' kun sani wadanda aka san su da mulkin al'ummai sukan nuna masu iko, hakimansu kuma sukan gasa masu iko.
Iesus autem vocans eos, ait illis: Scitis quia hi, qui videntur principari Gentibus, dominantur eis: et principes eorum potestatem habent ipsorum.
43 Amma ba haka zai kasance a tsakaninku ba. Duk wanda ya ke son zama babba a cikinku, lalle ne ya zama baranku.
Non ita est autem in vobis, sed quicumque voluerit fieri maior, erit vester minister:
44 Duk wanda ya ke so ya shugabance ku lalle ne ya zama bawan kowa.
et quicumque voluerit in vobis primus esse, erit omnium servus.
45 Saboda haka ne Dan mutum ya zo ba domin a bauta masa ba, sai dai domin shi yayi bautar, ya kuma ba da ransa fansa saboda da mutane da yawa.”
Nam et Filius hominis non venit ut ministraretur ei, sed ut ministraret, et daret animam suam redemptionem pro multis.
46 Sa'adda suka iso Yariko, yana fita daga Yariko kenan, shi da almajiransa, da wani babban taro, sai ga wani makaho mai bara, mai suna Bartimawas dan Timawas yana zaune a gefen hanya.
Et veniunt Iericho: et proficiscente eo de Iericho, et discipulis eius, et plurima multitudine, filius Timæ Bartimæus cæcus, sedebat iuxta viam mendicans.
47 Da ya ji Yesu Banazare ne, ya fara daga murya yana cewa, ''Ya Yesu, Dan Dauda, kaji tausayina''
Qui cum audisset quia Iesus Nazarenus est, cœpit clamare, et dicere: Iesu fili David, miserere mei.
48 Mutane da yawa suka kwabe shi, cewa yayi shiru. Sai ya kara daga murya kwarai da gaske, yana cewa, Ya Dan Dauda ka yi mani jinkai, ka ji tausayina!”
Et comminabantur ei multi ut taceret. At ille multo magis clamabat: Fili David miserere mei.
49 Yesu ya tsaya ya ce, ku kirawo shi. Su kuwa suka kirawo makahon suka ce masa. ''Albishrinka, ta so! Yana kiranka.''
Et stans Iesus præcepit illum vocari. Et vocant cæcum dicentes ei: Animæquior esto: surge, vocat te.
50 Makahon ya yar da mayafinsa, ya zaburo wurin Yesu.
Qui proiecto vestimento suo exiliens, venit ad eum.
51 Yesu ya tambaye shi, ya ce, '' me ka ke so in yi maka?'' Makahon ya ce, ''Malam in sami gani.''
Et respondens Iesus dixit illi: Quid tibi vis faciam? Cæcus autem dixit ei: Rabboni, ut videam.
52 Yesu ya ce masa. ''Yi tafiyarka, bangaskiyarka ta warkar da kai.'' Nan take idanunsa suka bude, ya bi Yesu, suka tafi tare.
Iesus autem ait illi: Vade, fides tua te salvum fecit. Et confestim vidit, et sequebatur eum in via.