< Luka 6 >
1 Ana nan wata Asabaci Yesu yana ratsawa cikin gonar hatsi, almajiransa kuma na karyar zangarkun hatsin, suna murtsukawa a hanayensu suna ci.
2 Amma wasu daga cikin Farisawa suka ce, “Saboda me kuke yin abin da bai halatta a yi a ranar Asabaci ba?”
3 Yesu ya amsa masu, ya ce, “Ba ku karanta abin da Dauda ya yi a lokacin da yake jin yunwa ba, shi da mutanen da ke tare da shi?
4 Ya je cikin gidan Allah, ya dauki gurasar alfarwa ya kuma ci daga ciki, ya kuma ba mazajen da ke tare da shi su ci, ko da shike ya halarta ga Firistoci ne kadai su ci.”
5 Sai ya ce masu, “Dan Mutum shi ne Ubangijin asabaci.”
6 Ya kasance a wata ranar Asabaci ya shiga cikin majami'a ya kuma koya wa mutane a can. Wani mutum na can wurin wanda hannun damansa ya shanye.
7 Marubuta da Farisawa na kallonsa su ga ko zai warkar da wani a ranar Asabaci, domin su samu dalilin zarginsa da yin abin da bai cancanta ba.
8 Amma ya san abin da suke tunani, sai ya ce wa mai shanyeyen hannun, “Tashi, ka tsaya a nan tsakiyar jama'a.” Sai mutumin ya tashi ya tsaya a nan.
9 Yesu ya ce masu, “Ina tambayar ku, ya halatta a ranar Asabaci a yi nagarta ko mugunta, a ceci rai ko a hallaka shi?
10 Sai ya dube su duka, ya kuma ce wa mutumin, “Mika hannunka.” Ya yi haka, sai hannunsa ya koma lafiyayye.
11 Amma suka fusata kwarai, suka yi shawara da junansu game da abin da za su yi da Yesu.
12 Ya zama a kwanakin nan, ya hawo bisan dutse domin ya yi addu'a. Ya ci gaba dukan dare yana addua'a ga Allah.
13 Da safiya ta yi, ya kira almajiransa zuwa wurinsa, ya kuma zabi goma sha biyu daga cikinsu, wadanda ya kira su “Manzanni.”
14 Sunayen Manzannin sune Siman (wanda ya kuma kira Bitrus) da dan'uwansa, Andrawus, Yakubu, Yahaya, Filibus, Bartalamawus,
15 Matta, Toma, Yakubu dan Halfa, Siman, wanda ake kira Zaloti, Yahuda dan Yakubu,
16 da Yahuda dan Iskariyoti, wanda ya zama maci amana.
17 Sai Yesu ya gangaro daga dutsen tare da su, suka kuma tsaya a sarari. Almajiransa da yawa na nan a wurin, tare da mutane da yawa daga Yahudiya da Urushalima, da kuma bakin tekun Taya da Sidon.
18 Sun zo domin su ji shi, da kuma su sami warkarwa daga dukan cututukansu. Mutane waddan da ke fama da kazaman ruhohi ma sun sami warkarwa.
19 Dukan taron jama'ar suna kokarin su taba shi domin ikon warkarwa yana fitowa daga wurinsa, ya kuma warkar da su duka.
20 Sai ya dubi almajiransa ya ce, “Masu albarka ne ku matalauta, gama Mulkin Allah naku ne.
21 Masu albarka ne ku masu yunwa yanzu, domin za a kosar da ku. Masu albarka ne ku masu kuka a yanzu, domin za ku yi dariya.
22 Masu albarka ne ku idan mutane sun ki ku, suka nuna maku wariya suna mai da sunayen ku na mugunta, domin Dan Mutum.
23 Za ku yi farin ciki a ranan nan kuna tsalle domin murna, domin hakika za ku samu lada mai girma a sama, domin haka kakannin-kakannin su suka yi wa annabawa.
24 Amma kaitonku mawadata! Domin kun rigaya kun samu ta'aziyar ku.
25 Kaitonku kosassu a yanzu! Domin za ku ji yunwa nan gaba. Kaitonku masu dariya yanzu! Domin za ku yi makoki kuna kuka nan gaba.
26 Kaiton ku idan kowadanne mutane suna yabon ku! Domin haka kakannin-kakanninsu suka yi wa annabawan karya.
27 Amma ina ce maku ku masu saurare na, ku kaunaci magabtanku, ku kuma aikata nagarta ga wadanda suke kinku.
28 Ku albarkaci masu zaginku, ku kuma yi addu'a ga wadanda suke wulakanta ku.
29 Wanda ya mare ku a wannan kunci, ku juya masa dayan. Idan wani ya dauki mayafinka, kada ka hana masa taguwarka.
30 Ku bayar ga duk wanda ya roke ku. Idan wani ya dauki wani abu da ke naku, kada ku bidi ya mayar da shi.
31 Duk abin da kake so mutane su yi maka, ka yi masu hakan nan.
32 Idan ka kaunaci masoyan ka ne kadai, me wannan zai amfane ka? Ko masu zunubi ma na kaunar masoyan su.
33 Idan kuna nuna alheri ga wadan da ke maku alheri kadai, menene ladan ku a nan? Ko masu zunubi ma na yin hakan nan.
34 Idan kun ba da rancen abubuwa ga mutanen da kuna sa zuciya zasu mayar maku ne kadai, menene ribar ku a nan? Ko masu zunubi suna ba masu zunubi rance, suna kuma sa zuciya a mayar masu dadai gwargwado.
35 Amma ku kaunaci magabtan ku, ku kuma nuna masu alheri. Ku basu rance, kada ku sa zuciya a maido maku, kuma sakamakon ku zai zama da girma. Za ku zama yayan Mafifici, domin shi da kansa yana nuna jinkai ga marasa godiya da miyagun mutane.
36 Ku zama masu jinkai, domin Ubanku mai jinkai ne.
37 Kada ku shari'anta, kuma ba za a shari'anta ku ba. Kada ku kayar, ku ma ba za a kashe ku ba. Ku yafe wa wasu, kuma za a yafe maku.
38 Ku bayar ga wasu, ku ma za a ba ku da yawa. Magwaji dankararre, girgizajje har ya cika yana zuba, za su zuba har cinyarku. Domin duk ma'aunin da ku ka yi amfani da shi, da shi za a auna maku.
39 Sai ya sake basu wani misali, “Makaho yana iya yi wa makaho jagora? Idan ya yi haka, dukansu biyu za su fada cikin rami, ko ba haka ba?
40 Almajiri baya fin Malaminsa, amma duk wanda ya samu horo sosai zai zama kamar malaminsa.
41 Don me kake duba dan hakin da ke a idon dan'uwanka, amma ba ka iya ganin gungumen da ke a idonka ba?
42 Don me za ka ce wa dan'uwanka, 'Dan'uwa, bari in cire dan hakin da ke a idonka', bayan kai da kanka ba ka iya ganin gungumen da ke a idonka ba? Kai munafuki! Ka fara cire gungumen da ke a idonka, sa'annan za ka gani da kyau yadda zaka cire hakin da ke a idon dan'uwanka.
43 Domin babu itace mai kyau da ke haifar rubabbun 'ya'ya, ko rubabben itace da zai haifi kyawawan 'ya'ya.
44 Domin ana iya sanin ko wani itace ta wurin 'ya'yan da yake bayarwa. Domin mutane basu kan tsinki 'ya'yan baure a jikin kaya, ko kuwa su dibi inabi daga jikin sarkakkiya.
45 Mutumin kirki, daga wadatar zuciyarsa ya kan ba da yaya masu kyau, kuma mugu daga cikin muguwar ajiyar zuciyarsa yake aikata mugunta. Domin daga cikar zuciyarsa ne bakinsa yakan yi magana.
46 Don me kuke ce da ni, 'Ubangiji, Ubangiji', amma ba ku yin biyayya da magana ta?
47 Duk wanda ya zo wurina ya ji kalmomina ya kuma yi biyayya da su, zan gaya maku yadda yake.
48 Yana kama da mutum da ke gina gida, wanda ya haka da zurfi zuwa cikin kasa ya kuma gina harshashin gidan sa a kan dutse. Da rigyawa ta zo, sai ruwa ya buga gidan, amma bai iya girgiza shi ba, domin an gina shi da kyau.
49 Amma duk mutumin da ya ji kalmomina ya kuma ki biyayya da su, yana kamar mutum wanda ya gina gidansa a kan kasa, babu harshashi. Amma da ambaliyan ruwa ta buga gidan, nan take ya rushe, ragargajewar gidan kuma da girma take.