< Luka 4 >

1 Sai Yesu, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya dawo daga kogin Urdun, sai Ruhu Mai Tsarki ya bishe shi zuwa cikin jeji
Then Jesus, full of the Holy Spirit, returned from the Jordan and was led by the Spirit into the wilderness,
2 kwana arba'in, shaidan kuma ya jarabce shi. A kwanakin nan, bai ci abinci ba, kuma yunwa ta kama shi bayan karshen lokacin.
where for forty days He was tempted by the devil. He ate nothing during those days, and when they had ended, He was hungry.
3 Shaidan ya ce masa, “Idan kai Dan Allah ne, ka umarci wannan dutse ya zama gurasa.”
The devil said to Him, “If You are the Son of God, tell this stone to become bread.”
4 Yesu ya amsa masa, “A rubuce yake, 'Ba da gurasa kadai Mutum zai rayu ba.'”
But Jesus answered, “It is written: ‘Man shall not live on bread alone.’”
5 Sai shaidan ya kai shi zuwa wani tudu mai tsawo, ya kuma nuna masa dukan mulkokin duniyan nan a dan lokaci.
Then the devil led Him up to a high place and showed Him in an instant all the kingdoms of the world.
6 Shaidan ya ce masa, “Zan ba ka iko ka yi mulkin dukan wadannan, da dukan daukakarsu. Zan yi haka domin an ba ni su duka in yi mulkinsu, kuma ina da yanci in ba dukan wanda na ga dama.
“I will give You authority over all these kingdoms and all their glory,” he said. “For it has been relinquished to me, and I can give it to anyone I wish.
7 Saboda da haka, idan ka rusuna ka yi mani sujada, dukansu za su zama naka.”
So if You worship me, it will all be Yours.”
8 Amma Yesu ya amsa ya ce masa, “A rubuce yake, 'Dole ne Ubangiji Allahnka za ka yi wa sujada, shi kadai kuma za ka bauta wa.”
But Jesus answered, “It is written: ‘Worship the Lord your God and serve Him only.’”
9 Sai shaidan ya kai Yesu Urushalima, ya tsayadda shi a bisan kololuwar haikali, kuma ya ce masa, “Idan kai Dan Allah ne, ka jefas da kanka kasa daga nan.
Then the devil led Him to Jerusalem and set Him on the pinnacle of the temple. “If You are the Son of God,” he said, “throw Yourself down from here.
10 Domin a rubuce yake, 'Zai ba mala'ikunsa umarni su kiyaye ka, su kuma tsare ka,'
For it is written: ‘He will command His angels concerning You to guard You carefully;
11 kuma, 'Za su daga ka sama a hannunsu, don kada ka yi tuntube a kan dutse.”
and they will lift You up in their hands, so that You will not strike Your foot against a stone.’”
12 Yesu ya amsa masa cewa, “An fadi, 'Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.'”
But Jesus answered, “It also says, ‘Do not put the Lord your God to the test.’”
13 Da shaidan ya gama yi wa Yesu gwaji, sai ya kyale shi sai wani lokaci.
When the devil had finished every temptation, he left Him until an opportune time.
14 Sai Yesu ya koma Galili cike da ikon Ruhu, kuma labarinsa ya bazu cikin dukan wuraren dake wannan yankin.
Jesus returned to Galilee in the power of the Spirit, and the news about Him spread throughout the surrounding region.
15 Ya yi ta koyarwa a cikin majami'unsu, sai kowa na ta yabon sa.
He taught in their synagogues and was glorified by everyone.
16 Wata rana ya zo Nazarat, birnin da aka rene shi. Kamar yadda ya saba yi, ya shiga cikin majami'a a nan ranar Asabaci, ya kuma tashi tsaye domin ya karanta Nassi.
Then Jesus came to Nazareth, where He had been brought up. As was His custom, He entered the synagogue on the Sabbath. And when He stood up to read,
17 An mika masa littafin anabi Ishaya, ya bude littafin ya kuma ga inda an rubuta,
the scroll of the prophet Isaiah was handed to Him. Unrolling it, He found the place where it was written:
18 “Ruhun Ubangiji yana kai na, domin ya shafe ni in yi wa'azin Bishara ga matalauta. Ya aike ni in yi shelar yanci ga daurarru, da kuma budewar idanu ga makafi, in 'yantar da wadanda su ke cikin kunci,
“The Spirit of the Lord is on Me, because He has anointed Me to preach good news to the poor. He has sent Me to proclaim liberty to the captives and recovery of sight to the blind, to release the oppressed,
19 in kuma yi shelar shekarar tagomashi na Ubangiji.”
to proclaim the year of the Lord’s favor.”
20 Sai ya rufe littafin, ya mai da shi ga ma'aikacin majami'ar, sai ya zauna. Dukan wadanda suke cikin majami'ar suka zura Idanuwansu a kansa.
Then He rolled up the scroll, returned it to the attendant, and sat down. The eyes of everyone in the synagogue were fixed on Him,
21 Sai ya fara masu magana, “Yau wannan Nassi ya cika a kunuwanku.”
and He began by saying, “Today this Scripture is fulfilled in your hearing.”
22 Dukan wadanda ke wurin sun shaida abin da ya fadi kuma dukansu sun yi ta mamakin kalmomin alheri da suke fitowa daga bakinsa. Suna cewa, “Wannan ai dan Yusufu ne kawai, ko ba haka ba?”
All spoke well of Him and marveled at the gracious words that came from His lips. “Isn’t this the son of Joseph?” they asked.
23 Yesu ya ce masu, “Lallai za ku fada mani wannan karin magana, 'Likita, ka warkar da kanka. Duk abin da mun ji wai ka yi a Kafarnahum, ka yi shi a nan garinka ma.'”
Jesus said to them, “Surely you will quote this proverb to Me: ‘Physician, heal yourself! Do here in Your hometown what we have heard that You did in Capernaum.’”
24 Ya sake cewa, “Hakika na fada maku, annabi baya samun karbuwa a garinsa.
Then He added, “Truly I tell you, no prophet is accepted in his hometown.
25 Amma na gaya maku gaskiya akwai gwauraye da yawa cikin Isra'ila a zamanin Iliya, lokacin da an rufe sammai shekaru uku da rabi babu ruwa, lokacin da anyi gagarumar yunwa a duk fadin kasar.
But I tell you truthfully that there were many widows in Israel in the time of Elijah, when the sky was shut for three and a half years and great famine swept over all the land.
26 Amma ba a aiki Iliya zuwa wurin waninsu ba, sai wurin gwauruwa da ke a Zarifat can kusa da Sidon.
Yet Elijah was not sent to any of them, but to the widow of Zarephath in Sidon.
27 Akwai kutare da yawa kuma a Isa'ila a zamanin anabi Elisha, amma babu wanda aka warkar sai dai Na'aman mutumin Suriya kadai.
And there were many lepers in Israel in the time of Elisha the prophet. Yet not one of them was cleansed—only Naaman the Syrian.”
28 Dukan mutanen da ke cikin majami'a suka fusata kwarai sa'adda suka ji wadannan zantattuka.
On hearing this, all the people in the synagogue were enraged.
29 Suka tashi suka tura shi zuwa wajen birnin, suka kai shi bakin dutsen da aka gina garinsu a kai dominsu jefar da shi kasa.
They got up, drove Him out of the town, and led Him to the brow of the hill on which the town was built, in order to throw Him over the cliff.
30 Amma ya ratsa tsakaninsu ya yi gabansa.
But Jesus passed through the crowd and went on His way.
31 Sannan ya gangara zuwa Kafarnahum, wani birni a Galili. Wata Asabaci yana koya wa mutane a cikin majami'a.
Then He went down to Capernaum, a town in Galilee, and on the Sabbath He began to teach the people.
32 Sun yi mamaki kwarai da koyarwan sa, domin maganarsa na da iko.
They were astonished at His teaching, because His message had authority.
33 A wannan lokacin akwai wani mutum a cikin majami'a mai kazamin ruhu, sai ya yi kara da babbar murya,
In the synagogue there was a man possessed by the spirit of an unclean demon. He cried out in a loud voice,
34 “Ina ruwan mu da kai, Yesu Banazarat? Ka zo domin ka hallaka mu ne? Na san ko kai wanene! Kai ne Mai Tsarki na Allah!”
“Ha! What do You want with us, Jesus of Nazareth? Have You come to destroy us? I know who You are—the Holy One of God!”
35 Yesu ya tsauta wa aljanin yana cewa, “Yi shiru ka fita daga cikinsa!” Da aljanin ya jefar da mutumin kasa a tsakiyarsu, ya fita daga cikinsa ba tare da yi masa rauni ba.
But Jesus rebuked the demon. “Be silent!” He said. “Come out of him!” At this, the demon threw the man down before them all and came out without harming him.
36 Dukan mutanen suka yi mamaki, kuma suna ta zancen wannan abu a tsakaninsu. Sun ce, “Wanda irin maganganu kenan? Ya umarce kazaman ruhohin da karfi da iko kuma sun fita.”
All the people were overcome with amazement and asked one another, “What is this message? With authority and power He commands the unclean spirits, and they come out!”
37 Saboda da haka, an fara yada labarinsa zuwa dukan kewayen yankin.
And the news about Jesus spread throughout the surrounding region.
38 Sai Yesu ya bar majami'ar ya shiga gidan Siman. A wannan lokacin, surukar Siman tana fama da zazzabi mai zafi, sai suka roke shi dominta.
After Jesus had left the synagogue, He went to the home of Simon, whose mother-in-law was suffering from a high fever. So they appealed to Jesus on her behalf,
39 Sai ya tsaya a kanta, ya tsautawa zazzabin, kuma ya rabu da ita. Nan take, ta tashi ta fara yi masu hidima.
and He stood over her and rebuked the fever, and it left her. And she got up at once and began to serve them.
40 Da faduwar rana, mutane suka kawo wa Yesu dukan wadanda suke ciwo da cuttuttuka dabam dabam. Ya dora masu hannuwansa ya warkar da su.
At sunset, all who were ill with various diseases were brought to Jesus, and laying His hands on each one, He healed them.
41 Aljanu kuma sun fita daga wadasunsu da dama, suna kuka cewa, “Kai ne Dan Allah!” Yesu ya tsauta wa aljannun ya kuma hana su magana, domin sun sani cewa shine Almasihu.
Demons also came out of many people, shouting, “You are the Son of God!” But He rebuked the demons and would not allow them to speak, because they knew He was the Christ.
42 Da safiya ta yi, ya kebe kansa zuwa wani wurin da babu kowa. Jama'a da dama suna neman sa suka zo inda yake. Sun yi kokari su hana shi barin su.
At daybreak, Jesus went out to a solitary place, and the crowds were looking for Him. They came to Him and tried to keep Him from leaving.
43 Amma ya ce masu, “Dole in yi bisharar Allah a wasu birane da dama, domin dalilin da aka aiko ni nan kenan.”
But Jesus told them, “I must preach the good news of the kingdom of God to the other towns as well, because that is why I was sent.”
44 Sai ya ci gaba da wa'azi cikin majami'u dukan fadin Yahudiya.
And He continued to preach in the synagogues of Judea.

< Luka 4 >