< Luka 24 >
1 Da sassafe a ranar farko ta mako, suka zo kabarin, suka kawo kayan kamshi wadda suka shirya.
2 Sai suka samu dutsen a mirgine shi daga kabarin.
3 Suka shiga ciki, amma ba su sami jikin Ubangiji Yesu ba.
4 Ya faru kuwa, yayin da suke a rikice game da wannan, ba zato, mutane guda biyu suka tsaya a gabansu da tufafi masu walkiya.
5 Sa'adda matan suka sunkuyar da kansu kasa domin tsoro, suka ce wa matan, “Don me kuke neman mai rai ciki matattatu?
6 Baya nan, amma ya tashi! Ku tuna fa yadda ya yi maku magana tun sa'adda ya ke Galili,
7 cewa za a ba da Dan Mutum ga mutane masu zunubi su kuma giciye shi, a rana ta uku, zai tashi kuma”
8 Sai matan suka tuna da kalmominsa,
9 suka koma daga kabarin sai suka gaya wa sha dayan wadannan abubuwan da dukan sauran.
10 Su Maryamu Magadaliya, Yuwana, Maryamu uwar Yakubu, da sauran matan da ke tare da su suka ba manzanni rohoton wadannan abubuwan.
11 Amma manzannin suka dauki maganar kamar ba ta da amfani, kuma ba su bada gaskiya ga matan ba.
12 Duk da haka Bitrus ya tashi, sai ya gudu zuwa kabarin, ya sunkuya yana kallon ciki, sai ya gan likaftani linin kadai. Sa'annan Bitrus ya tafi gidansa, yana ta mamakin abinda ya faru.
13 A ranan nan, sai ga biyu daga cikinsu suna tafiya zuwa wani kauye suna Imawus, wanda nisansa kimanin mil ne daga Urushalima.
14 Suna tattaunawa da junansu game da dukan abubuwan da suka faru.
15 Sai ya zama da cewa, sa'adda su ke tattaunawa tare da tambayoyi, sai Yesu da kansa ya matsa kusa yana tafiya tare da su.
16 Amma idanunsu basu iya ganewa da shi ba.
17 Yesu ya ce masu, “Menene ku ke magana akai sa'adda ku ke tafiya?” Suka tsaya a wurin suna bakin ciki.
18 Daya daga cikinsu, mai suna Kiliyobas, ya amsa masa, “Kai ne kadai mutumin da ke Urushalima wanda bai san abubuwan da suka faru a can a wannan kwanakin ba?”
19 Yesu ya ce masu, “Wadanne abubuwa?” Suka amsa masa, “Abubuwa game da Yesu ba Nazarat, wanda ya ke annabi ne, mai manyan ayuka da kalmomi daga Allah da kuma mutane.
20 Da yadda manyan firistoci da masu mulkinmu suka bada shi domin a hukunta shi ga mutuwa a kuma giciye shi.
21 Amma mun yi begen cewa shine wanda za ya yantar da Isra'ila. I, bayan wannan kuma, yanzu kwana uku kenan tunda wadannan abubuwan suka faru.
22 Amma har'ila yau, wadansu mata da ke tare da mu sun yi mana abin al'ajabi, da suka kasance a kabarin tunda sassafe.
23 Sa'adda ba su sami jikinsa ba, suka zo, da cewa su ma sun ga wahayin mala'iku wadanda suka ce masu ya na da rai.
24 Wasu maza wadanda ke tare da mu suka tafi kabarin, suka tarar da shi kamar yadda matan suka fada. Amma ba su ganshi ba.”
25 Yesu ya ce masu, “Ku mutane masu wauta da marasa ba da gaskiya ga abin da annabawa suka fada!
26 Bai zama dole ne Almasihu ya sha wahalan wadannan abubuwan ba, ya kuma shiga cikin daukakarsa?”
27 Sa'annan da farko daga Musa da har zuwa dukan annabawa, Yesu ya fasara masu duka abubuwa da ke game da kansa a dukan littattafai.
28 Da suka yi kusa da kauyen, inda suke tafiya, ko da yake Yesu ya yi kamar zai wuce su.
29 Amma suka tilasta shi, cewa, “Ka zauna da mu, gama yamma ta yi kusa rana kuma ta kusa karewa.” Sai Yesu ya tafi ya zauna da su.
30 Ya faru cewa, sa'adda ya zauna tare da su domin ya ci abinci, sai ya dauki gurasan, ya albarkace shi, ya kakkarya, sai ya ba su.
31 Sa'annan idanunsu suka bude, da suka gane shi, sai ya bace daga garesu,
32 Suka ce wa junansu, ashe zuciyarmu ba ta yi kuna a cikinmu ba, sa'adda yake magana da mu a hanya, sa'adda ya bude mana littattafai?”
33 Suka tashi a wancan sa'a, sai suka koma Urushalima. Suka sami sha dayan nan tare, da wadanda suke tare da su,
34 cewa, “Lalle ne Ubangiji ya tashi, ya kuma bayyana ga Siman.”
35 Sai suka fadi abubuwan da suka faru a hanya, da yadda aka bayyana masu Yesu sa'adda ya kakkarya gurasa.
36 Sa'adda suke fadin wadannan abubuwan, sai Yesu ya tsaya a sakaninsu, sai ya ce masu, “Salama a gareku.”
37 Amma suka firgita suna cike da tsoro, suna tsammani sun ga fatalwa.
38 Yesu ya ce masu, don me ku ke damuwa? Don me tambayoyi ke tasowa a zuciyarku?
39 Duba hannayena da kafafuna, cewa nine da kaina. Taba ni ku gani. Gama ruhu ba shi da jiki da kashi, kamar yadda ku ka ga nake da su.”
40 Bayan da ya fadi wannan, sai ya nuna masu hannayensa da kafafunsa.
41 Sa'adda suke cike da farin ciki, da mamaki, Yesu ya ce masu, “Kuna da wani abinci?”
42 Sai suka bashi gasasshen kifi.
43 Yesu ya karba, ya ci a gabansu.
44 Sai ya ce masu, “Sa'adda nake tare da ku na gaya maku cewa duka abin da aka rubuta a cikin dokokin Musa da na annabawa da Zabura dole su cika.”
45 Sai ya bude hankalinsu, saboda su gane littattafai.
46 Ya ce masu, “A rubuce yake, cewa Almasihu za ya sha wuya, zai tashi kuma daga matattu a rana ta uku.
47 Ku yi wa'azin tuba da gafarar zunubai a cikin sunansa ga dukan al'ummai, ku fara daga Urushalima.
48 Ku shaidu ne ga wadannan abubuwan.
49 Duba, ina aiko da alkawarin Ubana a kanku. Amma ku jira a birni, sai an suturta ku da iko daga sama.”
50 Sa'annan Yesu ya tafi tare da su har sai da suka kai kusa da Betanya. Sai ya daga hannunsa ya albarkace su.
51 Ya zama sa'adda yake sa masu albarka, ya bar su sai aka dauke shi zuwa cikin sama.
52 Sai suka yi masa sujada, suka komo Urushalima da murna mai yawa.
53 Kullayaumin suna cikin haikali, suna albarkatar Allah.