< Luka 24 >

1 Da sassafe a ranar farko ta mako, suka zo kabarin, suka kawo kayan kamshi wadda suka shirya.
Da sassafe a ranar farko ta mako, matan suka je kabarin, da kayan ƙanshin da suka shirya.
2 Sai suka samu dutsen a mirgine shi daga kabarin.
Suka iske an riga an gungurar da dutsen daga bakin kabarin.
3 Suka shiga ciki, amma ba su sami jikin Ubangiji Yesu ba.
Amma da suka shiga ciki, ba su iske jikin Ubangiji Yesu ba.
4 Ya faru kuwa, yayin da suke a rikice game da wannan, ba zato, mutane guda biyu suka tsaya a gabansu da tufafi masu walkiya.
Yayinda suna cikin tunani a kan wannan, nan take, ga waɗansu mutum biyu tsaye kusa da su, sanye da kaya masu ƙyalli, kamar walƙiya.
5 Sa'adda matan suka sunkuyar da kansu kasa domin tsoro, suka ce wa matan, “Don me kuke neman mai rai ciki matattatu?
A cikin tsoro, matan suka fāɗi da fuskokinsu a ƙasa, amma mutanen suka ce musu, “Me ya sa kuke neman mai rai a cikin matattu?
6 Baya nan, amma ya tashi! Ku tuna fa yadda ya yi maku magana tun sa'adda ya ke Galili,
Ba ya nan, ya tashi! Ku tuna yadda ya gaya muku tun yana tare da ku a Galili cewa,
7 cewa za a ba da Dan Mutum ga mutane masu zunubi su kuma giciye shi, a rana ta uku, zai tashi kuma”
‘Dole a ba da Ɗan Mutum ga hannun masu zunubi, a kuma gicciye shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.’”
8 Sai matan suka tuna da kalmominsa,
Sai suka tuna da maganarsa.
9 suka koma daga kabarin sai suka gaya wa sha dayan wadannan abubuwan da dukan sauran.
Da suka dawo daga kabarin, sai suka faɗa wa Sha Ɗayan nan da sauransu, dukan waɗannan abubuwa.
10 Su Maryamu Magadaliya, Yuwana, Maryamu uwar Yakubu, da sauran matan da ke tare da su suka ba manzanni rohoton wadannan abubuwan.
Matan da suka gaya wa manzannin waɗannan abubuwa su ne, Maryamu Magdalin, da Yowanna, da Maryamu uwar Yaƙub, da waɗansu da suke tare da su.
11 Amma manzannin suka dauki maganar kamar ba ta da amfani, kuma ba su bada gaskiya ga matan ba.
Amma ba su gaskata matan ba, domin sun ɗauki kalmominsu wani zancen banza ne.
12 Duk da haka Bitrus ya tashi, sai ya gudu zuwa kabarin, ya sunkuya yana kallon ciki, sai ya gan likaftani linin kadai. Sa'annan Bitrus ya tafi gidansa, yana ta mamakin abinda ya faru.
Duk da haka, Bitrus ya tashi a guje zuwa kabarin. Da ya sunkuya, sai ya ga ƙyallayen lilin kaɗai a kwance. Sai ya koma yana tunani a ransa, a kan abin da ya faru.
13 A ranan nan, sai ga biyu daga cikinsu suna tafiya zuwa wani kauye suna Imawus, wanda nisansa kimanin mil ne daga Urushalima.
A wannan rana kuma, biyu daga cikinsu suna tafiya zuwa wani ƙauye, da ake kira Emmawus, da suke kusan mil bakwai daga Urushalima.
14 Suna tattaunawa da junansu game da dukan abubuwan da suka faru.
Suna magana da juna a kan dukan abubuwan da suka faru.
15 Sai ya zama da cewa, sa'adda su ke tattaunawa tare da tambayoyi, sai Yesu da kansa ya matsa kusa yana tafiya tare da su.
Da suna magana, kuma suna tattauna waɗannan abubuwa da junansu, sai Yesu da kansa ya zo yana tafiya tare da su.
16 Amma idanunsu basu iya ganewa da shi ba.
Amma ba a ba su ikon gane shi ba.
17 Yesu ya ce masu, “Menene ku ke magana akai sa'adda ku ke tafiya?” Suka tsaya a wurin suna bakin ciki.
Sai ya tambaye, su ya ce, “Mene ne kuke tattaunawa da juna a cikin tafiyarku?” Suka tsaya shiru, da damuwa a fuskarsu.
18 Daya daga cikinsu, mai suna Kiliyobas, ya amsa masa, “Kai ne kadai mutumin da ke Urushalima wanda bai san abubuwan da suka faru a can a wannan kwanakin ba?”
Ɗaya daga cikinsu, mai suna Kiliyobas, ya tambaye shi ya ce, “Ashe, kai baƙo ne a Urushalima, da ba ka san abubuwan da suka faru a can, a cikin kwanakin nan ba?”
19 Yesu ya ce masu, “Wadanne abubuwa?” Suka amsa masa, “Abubuwa game da Yesu ba Nazarat, wanda ya ke annabi ne, mai manyan ayuka da kalmomi daga Allah da kuma mutane.
Sai ya yi tambaya, “Waɗanne abubuwa?” Suka amsa suka ce, “Game da Yesu Banazare. Shi annabi ne, mai iko ne kuma cikin ayyukansa da maganarsa, a gaban Allah da kuma dukan mutane.
20 Da yadda manyan firistoci da masu mulkinmu suka bada shi domin a hukunta shi ga mutuwa a kuma giciye shi.
Manyan firistoci da masu mulkinmu sun ba da shi a yi masa hukuncin mutuwa, suka kuwa gicciye shi.
21 Amma mun yi begen cewa shine wanda za ya yantar da Isra'ila. I, bayan wannan kuma, yanzu kwana uku kenan tunda wadannan abubuwan suka faru.
Amma da, muna sa zuciya cewa, shi ne wanda zai fanshi Isra’ila. Bugu da ƙari kuma yau kwana uku ke nan tun da wannan abin ya faru.
22 Amma har'ila yau, wadansu mata da ke tare da mu sun yi mana abin al'ajabi, da suka kasance a kabarin tunda sassafe.
Har wa yau, waɗansu daga cikin matanmu sun ba mu mamaki. Sun je kabarin da sassafen nan,
23 Sa'adda ba su sami jikinsa ba, suka zo, da cewa su ma sun ga wahayin mala'iku wadanda suka ce masu ya na da rai.
amma ba su sami jikinsa ba. Sun dawo sun faɗa mana cewa, sun ga wahayi na mala’iku, da suka ce yana da rai.
24 Wasu maza wadanda ke tare da mu suka tafi kabarin, suka tarar da shi kamar yadda matan suka fada. Amma ba su ganshi ba.”
Sa’an nan, waɗansu abokanmu suka je kabarin, suka kuma tarar da kome kamar yadda matan suka faɗa, amma shi, ba su gan shi ba.”
25 Yesu ya ce masu, “Ku mutane masu wauta da marasa ba da gaskiya ga abin da annabawa suka fada!
Sai ya ce musu, “Ashe, ku marasa azanci ne, masu nauyin zuciyar gaskata, da dukan abin da annabawa suka faɗa!
26 Bai zama dole ne Almasihu ya sha wahalan wadannan abubuwan ba, ya kuma shiga cikin daukakarsa?”
Ai, dole Kiristi yă sha waɗannan wahalolin, kafin yă shiga ɗaukakarsa.
27 Sa'annan da farko daga Musa da har zuwa dukan annabawa, Yesu ya fasara masu duka abubuwa da ke game da kansa a dukan littattafai.
Sai ya fara bayyana musu daga Musa da dukan Annabawa, abin da dukan Nassi ya faɗa a kansa.”
28 Da suka yi kusa da kauyen, inda suke tafiya, ko da yake Yesu ya yi kamar zai wuce su.
Da suka yi kusa da ƙauyen da za su, sai Yesu ya yi kamar zai ci gaba.
29 Amma suka tilasta shi, cewa, “Ka zauna da mu, gama yamma ta yi kusa rana kuma ta kusa karewa.” Sai Yesu ya tafi ya zauna da su.
Amma suka matsa masa suka ce, “Sauka wurinmu, don dare ya kusa, rana ta kusa fāɗuwa.” Sai ya sauka wurinsu.
30 Ya faru cewa, sa'adda ya zauna tare da su domin ya ci abinci, sai ya dauki gurasan, ya albarkace shi, ya kakkarya, sai ya ba su.
Da ya zauna a tebur tare da su, sai ya ɗauki burodi, ya yi godiya, ya kakkarya ya fara ba su.
31 Sa'annan idanunsu suka bude, da suka gane shi, sai ya bace daga garesu,
Sa’an nan idanunsu suka buɗe, suka gane shi. Sai ya ɓace musu.
32 Suka ce wa junansu, ashe zuciyarmu ba ta yi kuna a cikinmu ba, sa'adda yake magana da mu a hanya, sa'adda ya bude mana littattafai?”
Suka tambayi juna, “Ashe, shi ya sa zukatanmu suka kuna a cikinmu, sa’ad da yake magana da mu a hanya, yana bayyana mana Nassi.”
33 Suka tashi a wancan sa'a, sai suka koma Urushalima. Suka sami sha dayan nan tare, da wadanda suke tare da su,
Suka tashi nan da nan suka koma Urushalima. A can suka sami Sha Ɗayan nan da waɗanda suke tare da su a wuri ɗaya,
34 cewa, “Lalle ne Ubangiji ya tashi, ya kuma bayyana ga Siman.”
suna cewa, “Gaskiya ne! Ubangiji ya tashi, ya kuma bayyana ga Siman”
35 Sai suka fadi abubuwan da suka faru a hanya, da yadda aka bayyana masu Yesu sa'adda ya kakkarya gurasa.
Sai su biyun nan suka ba da labarin abin da ya faru a hanya, da kuma yadda suka gane Yesu yayinda ya kakkarya burodin.
36 Sa'adda suke fadin wadannan abubuwan, sai Yesu ya tsaya a sakaninsu, sai ya ce masu, “Salama a gareku.”
Suna cikin wannan zance, sai ga Yesu da kansa tsaye a tsakiyarsu. Sai ya ce musu, “Salama a gare ku!”
37 Amma suka firgita suna cike da tsoro, suna tsammani sun ga fatalwa.
Suka firgita, suka tsorota, suna tsammani fatalwa ce suka gani.
38 Yesu ya ce masu, don me ku ke damuwa? Don me tambayoyi ke tasowa a zuciyarku?
Sai ya ce musu, “Don me kuke damuwa, kuke kuma shakka a zuciyarku?
39 Duba hannayena da kafafuna, cewa nine da kaina. Taba ni ku gani. Gama ruhu ba shi da jiki da kashi, kamar yadda ku ka ga nake da su.”
Ku duba hannuwana da ƙafafuna. Ai, ni ne da kaina! Ku taɓa ni ku ji, ai, fatalwa ba ta da nama da ƙashi, yadda kuke gani nake da su.”
40 Bayan da ya fadi wannan, sai ya nuna masu hannayensa da kafafunsa.
Da ya faɗi haka, sai ya nuna musu hannuwansa da ƙafafunsa.
41 Sa'adda suke cike da farin ciki, da mamaki, Yesu ya ce masu, “Kuna da wani abinci?”
Kuma har yanzu, suna cikin rashin gaskatawa, saboda murna da mamaki, sai ya tambaye su, “Kuna da abinci a nan?”
42 Sai suka bashi gasasshen kifi.
Suka ba shi ɗan gasasshen kifi,
43 Yesu ya karba, ya ci a gabansu.
ya karɓa ya ci a gabansu.
44 Sai ya ce masu, “Sa'adda nake tare da ku na gaya maku cewa duka abin da aka rubuta a cikin dokokin Musa da na annabawa da Zabura dole su cika.”
Ya ce musu, “Wannan shi ne abin da na gaya muku tun ina tare da ku cewa, dole a cika kome da aka rubuta game da ni, a cikin Dokar Musa, da Annabawa, da kuma Zabura.”
45 Sai ya bude hankalinsu, saboda su gane littattafai.
Sai ya wayar da tunaninsu don su fahimci Nassi.
46 Ya ce masu, “A rubuce yake, cewa Almasihu za ya sha wuya, zai tashi kuma daga matattu a rana ta uku.
Ya ce musu, “Wannan shi ne abin da aka rubuta, cewa dole Kiristi yă sha wahala, a rana ta uku kuma yă tashi daga matattu.
47 Ku yi wa'azin tuba da gafarar zunubai a cikin sunansa ga dukan al'ummai, ku fara daga Urushalima.
Kuma a cikin sunansa za a yi wa’azin tuba da gafarar zunubai, ga dukan ƙasashe. Za a kuwa fara daga Urushalima.
48 Ku shaidu ne ga wadannan abubuwan.
Ku ne shaidun waɗannan abubuwa.
49 Duba, ina aiko da alkawarin Ubana a kanku. Amma ku jira a birni, sai an suturta ku da iko daga sama.”
Zan aika muku da abin da Ubana ya yi alkawari. Amma ku dakata a birnin tukuna, sai an rufe ku da iko daga sama.”
50 Sa'annan Yesu ya tafi tare da su har sai da suka kai kusa da Betanya. Sai ya daga hannunsa ya albarkace su.
Bayan ya kai su waje kusa da Betani, sai ya ɗaga hannuwansa ya sa musu albarka.
51 Ya zama sa'adda yake sa masu albarka, ya bar su sai aka dauke shi zuwa cikin sama.
Yana cikin sa musu albarka, sai ya rabu da su. Aka ɗauke shi zuwa cikin sama.
52 Sai suka yi masa sujada, suka komo Urushalima da murna mai yawa.
Sai suka yi masa sujada, suka koma Urushalima cike da murna sosai.
53 Kullayaumin suna cikin haikali, suna albarkatar Allah.
Sai suka ci gaba da zama a cikin haikalin, suna yabon Allah.

< Luka 24 >