< Luka 22 >
1 Anan nan idin gurasa mara yisti ya yi kusa, wanda a ke kira Idin ketarewa.
2 Manyan firistoci da marubuta suka yi shawara yadda za su kashe Yesu, gama suna jin tsoron mutane.
3 Shaidan ya shiga Yahuza Iskariyoti, daya daga cikin goma sha biyun.
4 Yahuza ya je ya yi shawara da manyan firistoci da Jarumawa yadda zai ba da Yesu a garesu.
5 Suka yi farin ciki, suka yarda su ba shi kudi.
6 Sai ya yarda, sai ya nimi dama yadda zai ba da shi garesu a lokacin da babu taro.
7 Ranar idin gurasa mara yisti ya yi, da dole za a yi hadayan rago na Idin ketarewa.
8 Yesu ya aiki Bitrus da Yahaya, ya ce masu, “Ku je ku shirya mana abincin Idin ketarewa, domin mu ci.”
9 Suka tambaye shi, “A ina ka ke so mu shirya?”
10 Ya amsa masu, “Ku ji, sa'adda ku ka shiga birnin, wani mutum mai dauke da tulun ruwa zai same ku. Ku bishi zuwa cikin gidan da za ya shiga.
11 Sai ku gaya wa mai gidan, 'Malam ya ce, “Ina dakin baki, inda zan ci abincin Idin ketarewa da almajirai na?'”
12 Zai nuna maku babban bene wanda yake a shirye. Ku shirya a can.”
13 Sai suka tafi, suka sami komai kamar yadda ya gaya masu. Sai suka shirya abincin Idin ketarewan.
14 Sa'adda lokacin ya yi, ya zauna da almajiran.
15 Sai ya ce masu, “Ina da marmari matuka in ci wannan abincin Idin ketarewa da ku kamin in sha wahala.
16 Gama na ce maku, ba zan ci shi kuma ba, sai dai an cika shi a mulkin Allah.”
17 Sai Yesu ya dauki koko, sa'adda ya yi godiya, sai yace, “Karba wannan, ku rarraba a tsakaninku.
18 Gama ina ce maku, ba zan sha wannan ruwan inabi kuma ba, sai dai mulkin Allah ya zo.”
19 Sai ya dauki gurasa, sa'adda ya yi godiya, ya kakkarya shi, sai ya ba su, cewa, “Wannan jikina ne wanda aka bayar dominku. Ku yi wannan domin tunawa da ni.”
20 Sai ya dauki kokon kuma bayan jibi, cewa, “Wannan koko sabon alkawari ne cikin jinina, wanda aka zubar dominku.
21 Amma ku yi lura. Wanda zai bashe ni yana tare da ni a teburi.
22 Gama Dan Mutum zai tafi lallai kamar yadda aka kaddara. Amma kaiton wannan mutum da shine za ya bashe shi!”
23 Sai suka fara tambaya a tsakaninsu, wanene a cikinmu da zai yi wannan abu.
24 Sai gardama ta tashi a tsakaninsu game da wanene mafi girma.
25 Ya ce masu, “Sarakunan al'ummai suna nuna iko akansu, kuma wadanda suke da iko a kansu ana ce da su masu mulki da daraja.
26 Amma kada ya zama haka da ku. A maimakon haka, bari wanda ya ke mafi girma a cikinku ya zama mafi kankanta. Bari wanda yafi muhimmanci kuma ya zama kamar mai hidima.
27 Gama wanene yafi girma, wanda ya zauna a teburi, ko kuwa wanda yake yin hidima? Ba wanda ya zauna a teburi ba? Duk da haka ina kamar mai hidima a tsakaninku.
28 Amma ku ne wadanda ku ke tare da ni a cikin jarabobina.
29 Na baku mulki, kamar yadda Ubana ya ba ni mulki,
30 domin ku ci ku kuma sha a teburi na mulkina. Za ku zauna a kan kursiyai kuna shari'anta kabilun nan goma sha biyu na Israila.
31 Siman, Siman, ka yi hankali, shaidan ya nemi izini a bada kai domin ya tankade ka kamar alkama.
32 Amma na yi maka addu'a, saboda kada bangaskiyarka ta fadi. Bayan da ka juyo kuma, ka karfafa 'yan'uwanka.”
33 Bitrus ya ce masa, “Ubangiji, ina shirye in tafi tare da kai zuwa cikin kurkuku da zuwa mutuwa.”
34 Yesu ya amsa masa, “Ina gaya maka, Bitrus, kamin caran zakara a yau, za ka yi musu na sau uku cewa ba ka sanni ba.”
35 Sa'annan Yesu ya ce masu, “Lokacin da na aike ku babu jaka, ko burgami ko takalma, ko kun rasa wani abu? Sai suka amsa, “Babu.”
36 Ya kuma ce masu, “Amma yanzu, wanda ya ke da jaka, bari ya dauka, da kuma burgami. Wanda ba shi da takobi sai ya sayar da taguwarsa ya sayi guda.
37 Gama ina ce maku, abin da aka rubuta game da ni dole sai ya cika, 'An lisafta shi kamar daya daga cikin masu karya doka.' Gama abinda aka fada akaina ya cika.”
38 Sai suka ce, “Ubangiji, duba! Ga takuba biyu.” Sai ya ce masu, “Ya isa.”
39 Bayan cin abincin yamma, Yesu ya tafi, kamar yadda ya saba yi, zuwa dutsen Zaitun, sai almajiran suka bi shi.
40 Sa'adda suka iso, ya ce masu, “Ku yi addu'a domin kada ku shiga cikin jaraba.”
41 Ya rabu da su misalin nisan jifa, sai ya durkusa kasa ya yi addu'a,
42 yana cewa “Uba, in ka yarda, ka dauke wannan kokon daga gareni. Ko da yake ba nufina ba, amma bari naka nufin ya kasance.”
43 Sai mala'ika daga sama ya bayyana a wurinsa, yana karfafa shi.
44 Yana cikin wahala sosai, sai ya dukufa cikin addu'a, har zufarsa kuma tana diga a kasa kamar gudajen jini.
45 Sa'adda ya tashi daga addu'arsa, sai ya zo wurin almajiran, ya same su suna barci domin bakin cikinsu,
46 sai ya tambaye su, “Don me kuke barci? Tashi ku yi addu'a, saboda kada ku shiga cikin jaraba.”
47 Sa'adda yana cikin magana, sai, ga taron jama'a suka bayana, tare da Yahuza, daya daga cikin sha biyun, ya na jagabansu. Sai ya zo kusa da Yesu domin ya yi masa sumba,
48 amma Yesu ya ce masa, “Yahuza, za ka ba da Dan Mutum da sumba?”
49 Sa'adda wadanda suke kewaye da Yesu suka ga abin da yake faruwa, sai suka ce, “Ubangiji, mu yi sara da takobi ne?”
50 Sai daya daga cikinsu ya kai wa bawan babban firist sara a kunne, sai ya yanke masa kunnensa na dama.
51 Yesu ya ce, “Ya isa haka.” Sai ya taba kunnensa, sai ya warkar da shi.
52 Yesu yace wa manyan firistoci, da masu tsaron haikali, da dattawa wadanda suke gaba da shi, “Kun fito kamar za ku kama dan fashi, da takuba da sanduna?
53 Sa'adda nake tare da ku kowace rana a haikali, ba ku kama ni ba. Amma wannan shine lokacinku, da kuma ikon duhu.”
54 Suka kama shi, sai suka tafi da shi, suka kawo shi cikin gidan babban firist. Amma Bitrus yana binsa daga nesa.
55 Bayan da suka hura wuta a tsakiyar gidan da suka zazzauna tare, Bitrus ya zaune a tsakaninsu.
56 Sai wata baranya ta ganshi ya zauna a hasken wuta, sai ta zura masa ido ta ce, “Wannan mutum ma yana tare da shi.”
57 Amma Bitrus ya yi musu, yana cewa, “Mace, ban san shi ba.”
58 Bayan dan karamin lokaci sai wani mutum ya gan shi, sai ya ce, “Kaima kana daya daga cikinsu.” Amma Bitrus ya ce, “Mutumin, ba ni ba ne.”
59 Bayan sa'a daya sai wani mutum ya nace da cewa, “Gaskiya wannan mutum yana tare da shi, gama shi dan Galili ne.”
60 Amma Bitrus ya ce, “Mutumin, ban san abin da kake fada ba.” Sai nan da nan, da yana cikin magana, sai zakara ta yi cara.
61 Yana juyawa, sai Ubangiji ya dubi Bitrus. Sai Bitrus ya tuna kalmar Ubangiji, sa'adda ya ce masa, “Kafin zakara ya yi cara yau za ka musunce ni sau uku.”
62 Da fitowarsa waje, Bitrus ya yi kuka mai zafi.
63 Sai mutanen da ke tsare da Yesu suka yi masa ba'a da bulala kuma.
64 Bayan da suka rufe masa idanu, suka tambaye shi, cewa, “Ka yi annabci! Wa ya buge ka?”
65 Suka yi wadansu miyagun maganganu na sabo game da Yesu.
66 Da gari ya waye, sai dattawa suka hadu tare, da manyan firistoci da marubuta. Sai suka kai shi cikin majalisa
67 suka ce, “Gaya mana, in kai ne Almasihu.” Amma yace masu, “Idan na gaya maku, ba za ku gaskanta ba,
68 idan na yi maku tambaya, ba za ku amsa ba.
69 Amma nan gaba, Dan Mutum zai zauna a hannun dama na ikon Allah.”
70 Suka ce masa, “Ashe kai Dan Allah ne?” Sai Yesu ya ce masu, “Haka kuka ce, nine.”
71 Suka ce, “Don me muke neman shaida? Gama mu da kanmu munji daga bakinsa.”