< Luka 21 >
1 Yesu ya tada ido sai ya ga mutane masu arziki wadanda suke saka baikonsu a cikin ma'aji.
2 Ya ga wata gwauruwa matalauciya tana saka anini biyu a ciki.
3 Sai ya ce, “Gaskiya ina gaya maku, wannan matalauciyar gwauruwa ta saka fiye da dukansu.
4 Duka wadannan sun bayar da baikonsu daga cikin yalwarsu. Amma wannan gwauruwan, daga cikin talaucin ta, ta saka dukan iyakar kudinta na zaman gari da take da shi.”
5 Kamar yadda wadansu suke maganan haikali, yadda aka yi masa ado da duwatsu masu daraja da bayebaye, ya ce,
6 “Game da wadannan abubuwa da ku ke gani, rana tana zuwa da ba dutse ko daya da zai zauna kan dan'uwansa da ba za a rushe kasa ba.”
7 Sai suka yi masa tambaya, cewa, “Malam, yaushe ne wadannan abubuwan zasu faru? Menene kuma zai zama alama sa'adda wadannan abubuwa suna shirin faruwa?”
8 Yesu ya amsa, “Ku yi hankali kada a rude ku. Gama dayawa zasu zo a cikin sunana, suna cewa, 'Ni ne shi,' kuma, 'Lokaci ya yi kusa.' Kada ku bi su.
9 Sa'adda ku ka ji game da yakoki da hargitsi, kada ku firgita, dole ne wadannan abubuwa su faru tukuna, amma karshe ba zai faru nan da nan ba.”
10 Sa'annan ya ce masu, “Al'umma za ta tasar ma al'umma, mulki kuma za ya tasar wa mulki.
11 Za a yi babbar girgizan kasa, a wurare dabam dabam kuma za a yi yunwa da annoba. Za a yi al'amura masu ban tsoro da manyan alamu daga sama.
12 Amma kafin abubuwan nan duka, za su kama ku, su kuma tsananta maku, suna mika ku ga majami'u da kuma gidajen kurkuku, za su kawo ku gaban sarakuna da gwamnoni saboda sunana.
13 Zai zamar maku zarafin shaida.
14 Saboda haka ku kudurta a ranku kada ku shirya yadda za ku amsa,
15 gama ni zan ba ku kalmomi da hikima, wadda dukan makiyanku ba za su yi tsayayya ko su karyata ku ba.
16 Amma har da mahaifa da 'yan'uwa da dangi da abokai za su bashe ku, su kuma kashe wadansun ku.
17 Kowa zai ki ku saboda sunana.
18 Amma ba ko gashin kanku da zai hallaka.
19 A cikin hankurin ku za ku ribato rayukanku.
20 Sa'adda ku ka ga Urushalima tana kewaye da sojoji, sai ku sani da cewa faduwarta ta yi kusa.
21 Sai wadanda su ke Yahudiya su gudu zuwa kan tuddai, wadanda suke tsakiyar gari kuma su tafi, kada su bar wadanda suke kauyuka su shigo ciki.
22 Gama wadannan ranakun ramako ne, saboda duka abubuwan da aka rubuta su cika.
23 Kaiton wadanda suke da juna biyu da masu ba da mama a wannan kwanakin! Gama za a sha kunci mai girma a kasan, da fushi kuma zuwa ga mutanen nan.
24 Za su fadi ta kaifin takobi kuma za a kai su cikin bauta ga dukan kasashe, al'ummai za su tattake Urushalima, har ya zuwa lokacin al'ummai ya cika.
25 Za a ga alamomi cikin rana da wata da kuma taurari. A duniya kuma, al'ummai za su sha kunci, za su rude saboda rurin teku da rakuman ruwa.
26 Mutane za su suma da tsoro da kuma da tunanin abubuwa da za su abko wa duniya. Gama za a girgiza ikokin sammai.
27 Sa'annan za su ga Dan Mutum yana zuwa a cikin gajimarai da iko da daukaka mai girma.
28 Amma sa'adda wadannan abubuwa suka fara faruwa, tashi saye, sai ku daga kanku sama, saboda ceton ku ya kusato.”
29 Yesu ya bada misali, “Duba itacen baure, da duka itatuwa.
30 Sa'adda su ke fitar da ganye, za ku gani da kanku cewa bazara ta yi kusa kuma.
31 Haka kuma, sa'adda ku ka ga wadannan abubuwa suna faruwa, ku sani cewa mulkin Allah ya yi kusa.
32 Gaskiya, na ke gaya maku, wannan zamani ba za ya shude ba, sai duka abubuwan nan sun faru.
33 Sama da kasa za su shude, amma maganata ba za ta shude ba.
34 Amma ku lura da kanku, domin kada ku nawaita zuciyarku da tararradin duniya da shayeshaye da damuwa ta rayuwa. Gama ranar za ta zo babu shiri
35 kamar tarko. Gama zai zo akan kowa da ke rayuwa a fuskar dukan duniya.
36 Amma ku zama a fadake kowanne lokaci, kuna addu'a domin ku iya samun karfin tserewa dukan wadannan abubuwa da za su faru, da kuma yadda za ku tsaya a gaban Dan Mutum.”
37 Da rana yana koyarwa a cikin haikali, dukan dare kuma yakan tafi dutsen da a ke kira zaitun.
38 Dukan mutane suka rika zuwa wurinsa da sassafe domin su ji shi a haikali.