< Luka 2 >
1 Ananan cikin kwanakin, sai Kaisar Augustas ya yi shela ya umarta a kidaya dukan mutane da ke zaune a cikin duniya.
У то време пак изиђе заповест од ћесара Августа да се препише сав свет.
2 Wannan itace kidaya ta farko da aka yi lokacin da Kiriniyus yake mulkin Suriya.
Ово је био први препис за владања Киринова Сиријом.
3 Sabili da haka, kowa ya koma garinsa domin a yi masa rijista domin kidayan.
И пођоше сви да се препишу, сваки у свој град.
4 Yusufu kuma ya tashi ya bar birnin Nazarat zuwa garin Baitalami da ke Yahudiya, wanda ake kuma kira birnin Dauda, domin shi daga zuriyar iyalin Dauda ne.
Тада пође и Јосиф из Галилеје, из града Назарета у Јудеју у град Давидов који се зваше Витлејем, јер он беше из дома и племена Давидовог,
5 Ya je can ya yi rijista tare da Maryamu, wadda yake tashi tana kuma da juna biyu.
Да се препише с Маријом, испрошеном за њега женом, која беше трудна.
6 Ya zama sa'adda suke can, lokaci ya yi da za ta haifi danta.
И кад онамо беху, дође време да она роди.
7 Ta haifi da, dan farinta kuwa, ta nade shi da kyau da 'yan tsummoki. Ta sa shi cikin wani kwami na dabbobi, gama babu daki dominsu a masaukin.
И роди Сина свог првенца, и пови Га, и метну Га у јасле; јер им не беше места у гостионици.
8 A cikin wannan yankin, akwai makiyaya wadanda suke zama a sarari suna tsaron garken tumakinsu da dare.
И беху пастири у оном крају који чуваху ноћну стажу код стада свог.
9 Nan da nan, sai mala'ikan Ubangiji ya bayyana gare su, daukakar Ubangiji kuma ta haskaka kewaye da su, sai suka figita kwarai.
И гле, анђео Господњи стаде међу њима, и слава Господња обасја их; и уплашише се врло.
10 Sai mala'ikan ya ce masu, “Kada ku ji tsoro, domin na kawo maku labari mai dadi da zai kawo murna da yawa ga dukan mutane.
И рече им анђео: Не бојте се; јер гле, јављам вам велику радост која ће бити свему народу.
11 Yau an haifi maku mai ceto a cikin birnin Dauda! Shine Almasihu Ubangiji!
Јер вам се данас роди спас, који је Христос Господ, у граду Давидовом.
12 Wannan itace alama da za a ba ku. Za ku ga dan jariri nade cikin 'yan tsummoki kwance cikin kwamin dabbobi.”
И ето вам знака: Наћи ћете дете повито где лежи у јаслама.
13 Nan take, sai ga babban taro daga sama tare da mala'ikan suna yabon Allah, suna cewa,
И уједанпут постаде с анђелом мноштво војника небеских, који хваљаху Бога говорећи:
14 “Daukaka ga Allah daga bisa, bari salama ta kasance a duniya tsakanin mutanen da ya ke jin dadinsu.”
Слава на висини Богу, и на земљи мир, међу људима добра воља.
15 Ya zama sa'adda mala'iku suka bar su zuwa cikin sama, sai makiyayan su ka ce wa junansu, “Bari mu je Baitalami mu ga wannan abin da ya faru, wanda Ubangiji ya nuna mana.”
И кад анђели отидоше од њих на небо, пастири говораху један другом: Хајдемо до Витлејема, да видимо то што се тамо догодило шта нам каза Господ.
16 Su ka yi hamzari suka tafi can sun iske Maryamu da Yusufu, suka ga jaririn kuwa kwance a cikin kwamin dabbobin.
И дођоше брзо, и нађоше Марију и Јосифа и дете где лежи у јаслама.
17 Bayan da sun ga wannan, suka gaya wa mutane abinda aka gaya masu game da wannan yaro.
А кад видеше, казаше све што им је казано за то дете.
18 Dukan wadanda su ka ji, su ka yi mamaki kwarai game da abin da makiyayan su ka gaya masu.
И сви који чуше дивише се томе што им казаше пастири.
19 Amma ita Maryamu ta ci gaba da tunani akan wadanan abubuwa da ta ji, tana tunani mai zurfi a cikin zuciyarta.
А Марија чуваше све речи ове и слагаше их у срцу свом.
20 Makiyayan suka koma suna ta daukaka da yabon Allah domin dukan abubuwan da suka ji, suka kuma gani, dadai da yadda aka gaya masu.
И вратише се пастири славећи и хвалећи Бога за све што чуше и видеше, као што им би казано.
21 Da ya kai kwana takwas, lokacin da za a yi wa jaririn kaciya, sai aka rada masa suna Yesu, sunan da mala'ikan ya bashi kamin a yi cikinsa.
И кад се наврши осам дана да Га обрежу, наденуше Му име Исус, као што је анђео рекао док се још није био ни заметнуо у утроби.
22 Da kwanakin tsarkakewar su ya wuce bisa ga shari'ar Musa, Yusufu da Maryamu suka kawo shi cikin haikali a Urushalima dominsu mika shi ga Ubangiji.
И кад дође време да иду на молитву по закону Мојсијевом, донеше Га у Јерусалим да Га метну пред Господа,
23 Kamar yadda aka rubuta a dokokin Ubangiji, “Za a kira duk da na fari kebabbe ga Ubangiji.”
(Као што је написано у закону Господњем: Да се свако дете мушко које најпре отвори материцу посвети Господу; )
24 Suka kuma zo su mika hadaya bisa ga yadda aka fada a shari'ar Ubangiji, “Kurciyoyi biyu ko 'yan tantabaru biyu.”
И да принесу прилог, као што је речено у закону Господњем, две грлице, или два голубића.
25 Ga shi akwai wani mutum a Ushalima mai suna Siman. Wannan mutum adali ne kuma mai ibada. Yana jiran mai ta'aziyar Isra'ila, kuma Ruhu Mai-sarki na bisansa.
И гле, беше у Јерусалиму човек по имену Симеун, и тај човек беше праведан и побожан, који чекаше утехе Израиљеве, и Дух Свети беше у њему.
26 An kuma bayyana masa ta wurin Ruhu Mai-tsarki cewa ba zai mutu ba sai ya ga Kristi na Ubangiji.
И њему беше Свети Дух казао да неће видети смрт док не види Христа Господњег.
27 Wata rana Siman ya zo cikin haikali ta wurin jagorar Ruhu Mai-tsarki. Da iyayen suka kawo yaron ciki, wato Yesu, domin su cika sharudan da shari'ar ke bukata,
И каза му Дух те дође у цркву; и кад донесоше родитељи дете Исуса да сврше за Њега закон по обичају,
28 sai Siman ya karbe shi cikin hanuwansa, ya yabi Allah ya ce,
И он Га узе на руке своје, и хвали Бога и рече:
29 “Yanzu bari bawanka ya tafi da salama, Ubangiji, bisa ga kalmarka.
Сад отпушташ с миром слугу свог, Господе, по речи својој;
30 Domin idanuna sun ga cetonka,
Јер видеше очи моје спасење Твоје,
31 wanda ka shirya a gaban dukan mutane:
Које си уготовио пред лицем свих народа,
32 Haske ne na wahayi ga al'ummai, kuma daukakar mutanenka Isra'ila.”
Видело, да обасја незнабошце, и славу народа Твог Израиља.
33 Mahaifin yaron da Mahaifiyarsa, sun yi mamaki kwarai domin abubuwan da aka fada akansa.
И Јосиф и мати Његова чуђаху се томе што се говораше за Њега.
34 Sai Siman ya albarkace su ya ce wa uwatasa Maryamu, “Ki ji da kyau, wannan yaro zai zama sanadiyar faduwa da tashin mutane dayawa a Isra'ila, kuma alama wadda ake kushen ta.
И благослови их Симеун, и рече Марији, матери Његовој: Гле, Овај лежи да многе обори и подигне у Израиљу, и да буде знак против кога ће се говорити
35 Kuma takobi zai tsaga zuciyar ki yadda tunanin mutane za ya bayyana.”
(А и теби самој пробошће нож душу), да се открију мисли многих срца.
36 Wata annabiya mai suna Annatu ta na nan wurin. Ita diyar Fanuyila ce daga kabilar Ashiru. Ta riga ta manyanta a shekaru sosai. Ta kasance da maigidanta shekaru bakwai bayan auren ta,
И беше Ана пророчица, кћи Фануилова, од колена Асировог; она је остарела, а седам је година живела с мужем од девојаштва свог,
37 sannan ta yi zama gwambranci na shekaru tamanin da hudu. Ba ta taba barin haikali ba, tana ci gaba da yi wa Ubangiji sujada, dare da rana.
И удова око осамдесет и четири године, која не одлажаше од цркве, и служаше Богу дан и ноћ постом и молитвама.
38 A dadai lokacin nan, ta hau zuwa wurinsu ta fara yi wa Allah godiya. Ta gaya wa dukan wadanda ke jiran fansar Urushalima.
И она у тај час дође, и хваљаше Господа и говораше за Њега свима који чекаху спасења у Јерусалиму.
39 Da su ka gama komai da aka bukace su suyi bisa ga tafarkin shari'ar Ubangiji, sai suka koma Galili, zuwa birninsu, Nazarat.
И кад свршише све по закону Господњем, вратише се у Галилеју у град свој Назарет.
40 Yaron kuma ya yi girma ya zama da karfi, yana karuwa da hikima, alherin Ubangiji kuma yana kansa.
А дете растијаше и јачаше у духу, и пуњаше се премудрости, и благодат Божија беше на Њему.
41 Iyayensa sukan tafi Urushalima kowacce shekara domin idin ketarewa.
И родитељи Његови иђаху сваке године у Јерусалим о празнику пасхе.
42 Da yana shekara goma sha biyu, suka sake haurawa daidai lokacin idin a al'adance.
И кад Му би дванаест година, дођоше они у Јерусалим по обичају празника;
43 Bayan da sun cika dukan kwanakin idin, sun fara dawowa gida. Amma dan yaron Yesu ya jinkirta ya zauna a Urushalima, kuma iyayensa basu sani ba.
И кад дане проведоше и они се вратише, оста дете Исус у Јерусалиму; и не знаде Јосиф и мати Његова;
44 Suna tsammani yana tare da sauran mutane da suke tafiya tare, sai suka yi tafiya na kwana daya. Suka fara neman sa a cikin danginsu da abokansu.
Него мислећи да је с друштвом, отидоше дан хода, и стадоше Га тражити по родбини и по знанцима.
45 Da ba su gan shi ba, sai suka koma Urushalima suna cigiyar sa a can.
И не нашавши Га вратише се у Јерусалим да Га траже.
46 Ya zama bayan kwanaki uku, su ka same shi a cikin haikali, yana zama a tsakiyar malamai, yana sauraron su yana kuma yi masu tambayoyi.
И после три дана нађоше Га у цркви где седи међу учитељима, и слуша их, и пита их,
47 Dukan wadanda suka ji shi suna ta mamakin fahimtar sa da amsoshin sa.
И сви који Га слушаху дивљаху се Његовом разуму и одговорима.
48 Da suka gan shi, suka yi mamaki kwarai. Mahaifiyarsa ta ce masa, “Da na, don me ka yi mana haka? Ka ji, mahaifinka da ni muna ta neman ka rai a bace.”
И видевши Га зачудише се, и мати Његова рече Му: Сине! Шта учини нама тако? Ево отац твој и ја са страхом тражисмо те.
49 Ya ce masu, “Don me kuke nema na? Ba ku sani cewa dole in kasance a gidan Ubana ba?”
И рече им: Зашто сте ме тражили? Зар не знате да мени треба у оном бити што је Оца мог?
50 Amma ba su gane abin da yake nufi da kalmomin nan ba.
И они не разумеше речи што им рече.
51 Sa'annan ya koma gida tare da su zuwa Nazarat yana kuma masu biyayya. Mahaifiayarsa kuma ta ajiye dukan wadannan abubuwa a zuciyarta tana yin tunani akansu.
И сиђе с њима и дође у Назарет; и беше им послушан. И мати Његова чуваше све речи ове у срцу свом.
52 Amma Yesu ya ci gaba da hikima da girma, ya kuma karu da tagomashi wurin Allah da mutane.
И Исус напредоваше у премудрости и у расту и у милости код Бога и код људи.