< Luka 19 >

1 Yesu ya shiga Yariko ya na wucewa cikinta.
He entered and was passing through Jericho.
2 Sai ga wani mutum a wurin mai suna Zakka. Shugaba ne na masu karban haraji, kuma mai arziki ne.
There was a man named Zacchaeus. He was a chief tax collector, and he was rich.
3 Yana kokarin ya ga ko wanene Yesu, amma bai iya gani ba sabo da yawan jama'a, domin shi gajere ne.
He was trying to see who Jesus was, and could not because of the crowd, because he was short.
4 Sai ya ruga gaba ya hau itacen baure domin ya gan shi, saboda Yesu zai wuce ta wannan hanya.
He ran on ahead and climbed up into a sycamore tree to see him, for he was going to pass that way.
5 Sa'adda Yesu ya zo wurin, ya kalli sama sai ya ce masa, “Zakka, ka sauko da sauri, domin yau dole in sauka a gidanka.”
When Jesus came to the place, he looked up and saw him, and said to him, “Zacchaeus, hurry and come down, for today I must stay at your house.”
6 Sai ya sauko da sauri, ya karbe shi da farin ciki.
He hurried, came down, and received him joyfully.
7 Sa'adda dukansu suka ga wannan, sai suka yi gunaguni, cewa, “Ya ziyarci mutum mai zunubi.”
When they saw it, they all murmured, saying, “He has gone in to lodge with a man who is a sinner.”
8 Zakka ya tsaya ya ce wa Ubangiji, “Duba, Ubangiji, zan ba matalauta rabin arzikina, idan kuma na cuci wani a kome, zan mai da adadinsa sau hudu.”
Zacchaeus stood and said to the Lord, “Behold, Lord, half of my goods I give to the poor. If I have wrongfully exacted anything of anyone, I restore four times as much.”
9 Yesu ya ce masa, “Yau ceto ya shigo wannan gida, domin shi ma dan Ibrahim ne.
Jesus said to him, “Today, salvation has come to this house, because he also is a son of Abraham.
10 Gama Dan Mutum ya zo ne domin ya nemi, ya kuma ceci batattun mutane.”
For the Son of Man came to seek and to save that which was lost.”
11 Da suka ji wadannan abubuwan, ya cigaba da magana, sannan ya fada masu wani misali, domin yana kusa da Urushalima, sai suka yi tsamani mulkin Allah za ya bayyana nan da nan.
As they heard these things, he went on and told a parable, because he was near Jerusalem, and they supposed that God’s Kingdom would be revealed immediately.
12 Sai ya ce, “Akwai wani mutum mai sarauta wanda ya tafi wata kasa mai nisa domin ya karba wa kansa mulki sa'annan ya dawo.
He said therefore, “A certain nobleman went into a far country to receive for himself a kingdom and to return.
13 Sai ya kira bayinsa guda goma, ya ba su fam goma, sai ya ce masu, 'Ku yi kasuwanci da wannan har sai na dawo.'
He called ten servants of his and gave them ten mina coins, and told them, ‘Conduct business until I come.’
14 Amma mutanensa suka ki shi sai suka aiki jakadu bayansa, cewa, 'Ba za mu yarda wannan mutum ya yi mulki a kanmu ba.'
But his citizens hated him, and sent an envoy after him, saying, ‘We do not want this man to reign over us.’
15 Anan nan sa'adda ya koma kuma, bayan da ya sami mulkin, sai ya ba da umarni a kira masa bayin da ya basu kudi, domin ya san ribar da suka samu wajen kasuwancin da suka yi.
“When he had come back again, having received the kingdom, he commanded these servants, to whom he had given the money, to be called to him, that he might know what they had gained by conducting business.
16 Na farkon ya zo wurinsa, cewa, 'Ubangiji, fam nan na ka ya yi riban fam goma.'
The first came before him, saying, ‘Lord, your mina has made ten more minas.’
17 Masaraucin ya ce masa, 'Madalla, bawan kirki. Domin ka yi aminci a karamin abu, za a baka iko kan birane goma.'
“He said to him, ‘Well done, you good servant! Because you were found faithful with very little, you shall have authority over ten cities.’
18 Na biyun ya zo, yana cewa, 'Fam na ka, Ubangiji, ya yi ribar fam biyar.'
“The second came, saying, ‘Your mina, Lord, has made five minas.’
19 Sai masarauncin yace masa, 'Ka dauki mulkin birane biyar.'
“So he said to him, ‘And you are to be over five cities.’
20 Wani kuma ya zo, yana cewa, 'Ubangiji, ga fam naka da na ajjiye shi da kyau cikin kaya,
Another came, saying, ‘Lord, behold, your mina, which I kept laid away in a handkerchief,
21 gama na ji tsoronka, domin kai mutum mai tsanani ne. Kana daukar abu da baka ajiye ba, kana kuma girbin abin da ba ka shuka ba.'
for I feared you, because you are an exacting man. You take up that which you did not lay down, and reap that which you did not sow.’
22 Masarauncin ya ce masa, 'Da kalmominka zan shari'antaka, kai mugun bawa. Ka sani cewa ni mutum mai tsanani ne, ina daukan abinda ban ajiye ba, ina kuma girbin abinda ban shuka ba.
“He said to him, ‘Out of your own mouth I will judge you, you wicked servant! You knew that I am an exacting man, taking up that which I did not lay down and reaping that which I did not sow.
23 To don me ba ka kai kudi na wurin masu banki ba, saboda bayan da na dawo zan karbe shi da riba?'
Then why did not you deposit my money in the bank, and at my coming, I might have earned interest on it?’
24 Masaraucin ya ce wa wadanda suke a tsaye a wurin, 'Ku karba fam da ke a wurinsa, ku ba mai fam goman nan.'
He said to those who stood by, ‘Take the mina away from him and give it to him who has the ten minas.’
25 Suka ce masa, 'Ubangiji, yana da fam goma.'
“They said to him, ‘Lord, he has ten minas!’
26 'Ina ce maku, duk wanda yake da abu za a kara masa, amma wadda bai da shi, za a karba sauran da ke wurinsa.
‘For I tell you that to everyone who has, will more be given; but from him who does not have, even that which he has will be taken away from him.
27 Amma wadannan abokan gabana, wadanda ba sa so in yi mulki bisansu, a kawo su nan a kashe su a gaba na.'
But bring those enemies of mine who did not want me to reign over them here, and kill them before me.’”
28 Da ya fadi wadannan abubuwan, sai ya yi gaba, yana tafiya zuwa Urushalima.
Having said these things, he went on ahead, going up to Jerusalem.
29 Ananan sa'adda ya zo kusa da Baitfaji da Baitanya, a kan tudu da a ke kira Zaitun, sai ya aiki almajiransa guda biyu, cewa,
When he came near to Bethsphage and Bethany, at the mountain that is called Olivet, he sent two of his disciples,
30 cewa, “Ku tafi cikin kauye da ke gabanku. Sa'adda ku ka shiga, za ku same dan aholaki da ba a taba hawansa ba. Ku kwance sai ku kawo mani shi.
saying, “Go your way into the village on the other side, in which, as you enter, you will find a colt tied, which no man has ever sat upon. Untie it and bring it.
31 Idan wani ya tambaye ku, 'Don me ku ke kwance shi?' Ku ce, 'Ubangiji ne ke bukatarsa.”
If anyone asks you, ‘Why are you untying it?’ say to him: ‘The Lord needs it.’”
32 Wadanda aka aike su suka je sun sami aholakin kamar yadda Yesu ya gaya masu.
Those who were sent went away and found things just as he had told them.
33 Sa'adda suna kwance aholakin, sai masu shi suka ce masu, “Don me ku ke kwance aholakin?”
As they were untying the colt, its owners said to them, “Why are you untying the colt?”
34 Suka ce, “Ubangiji yana bukatar sa.”
They said, “The Lord needs it.”
35 Suka kawo wa Yesu, suka shimfida tufafinsu akan aholakin sai suka dora Yesu akansa.
Then they brought it to Jesus. They threw their cloaks on the colt and sat Jesus on them.
36 Da yana cikin tafiya, suka shimfida tufafinsu akan hanya.
As he went, they spread their cloaks on the road.
37 Da ya yi kusa da gangaren tudun Zaitun, sai dukan taron almajiransa suka fara yin murna suna kuma yabon Allah da murya mai karfi domin dukan ayukan al'ajibi da suka gani,
As he was now getting near, at the descent of the Mount of Olives, the whole multitude of the disciples began to rejoice and praise God with a loud voice for all the mighty works which they had seen,
38 cewa, “Albarka ta tabbata ga sarki da ke zuwa cikin sunan Uba! Salama a sama da daraja mafi daukaka kuma!”
saying, “Blessed is the King who comes in the name of the Lord! Peace in heaven, and glory in the highest!”
39 Wadansu Farisawa daga cikin taron jama'a suka ce masa, “Malam, ka tsauta wa almajiranka.”
Some of the Pharisees from the multitude said to him, “Teacher, rebuke your disciples!”
40 Yesu ya amsa ya ce, “Ina gaya maku gaskiya, in wadannan sun yi shiru, duwatsu za su yi shewa.”
He answered them, “I tell you that if these were silent, the stones would cry out.”
41 Sa'adda Yesu yana kusatowa, sai ya yi kuka akan birnin,
When he came near, he saw the city and wept over it,
42 cewa, “Da kun san wannan rana, ko ku ma, abubuwan da ke kawo maku salama! Amma yanzu an boye su daga idanunku.
saying, “If you, even you, had known today the things which belong to your peace! But now, they are hidden from your eyes.
43 Gama rana zata ta zo a gareki, da makiyan ki zasu gina ganuwa a kewaye da ke, su kuma fada maki daga kowace gefe.
For the days will come on you when your enemies will throw up a barricade against you, surround you, hem you in on every side,
44 Za su sare ki kasa tare da 'ya'yanki. Ba za su bar wani dutse akan dan'uwansa ba, domin ba ki lura da lokacin da Allah ya na kokarin ceton ki ba.”
and will dash you and your children within you to the ground. They will not leave in you one stone on another, because you did not know the time of your visitation.”
45 Yesu ya shiga Haikalin sai ya fara korar masu sayarwa,
He entered into the temple and began to drive out those who bought and sold in it,
46 ya na ce masu, “A rubuce yake, 'Gida na zai zama wurin addu'a,' amma kun mayar da shi kogon mafasa.”
saying to them, “It is written, ‘My house is a house of prayer,’ but you have made it a ‘den of robbers’!”
47 Yesu yana nan yana koyarwa kowace rana a cikin haikali. Amma manyan firistoci da marubuta da shugabanin jama'a suna so su kashe shi,
He was teaching daily in the temple, but the chief priests, the scribes, and the leading men among the people sought to destroy him.
48 amma ba su sami hanyar yin wannan ba, domin mutane suna sauraron sa sosai.
They could not find what they might do, for all the people hung on to every word that he said.

< Luka 19 >