< Luka 11 >
1 Wani lokaci, Yesu yana yin addu'a a wani wuri, sai daya daga cikin almajiransa yace da shi, “Ubangiji, ka koya mana yin addu'a kamar yadda Yahaya ya koya wa almajiransa.”
I stalo se, když byl na jednom místě, modle se, že když přestal, řekl k němu jeden z učedlníků jeho: Pane, nauč nás modliti se, jako i Jan učil učedlníky své.
2 Yesu ya ce ma su, “Sa'anda ku ke yin addu'a ku ce, 'Uba a tsarkake sunanka. Mulkin ka ya zo.
I řekl jim: Když se modlíte; říkejte: Otče náš, jenž jsi v nebesích, posvěť se jméno tvé. Přijď království tvé. Buď vůle tvá, jako v nebi tak i na zemi.
3 Ka ba mu abin da za mu ci a kowacce rana.
Chléb náš vezdejší dávej nám každého dne.
4 Gafarta mana zunubanmu, kamar yadda muke gafarta ma wadanda suke mana laifi. Kada ka kai mu cikin jaraba.'”
I odpusť nám hříchy naše, nebo i my odpouštíme všelikému vinníku našemu. A neuvoď nás v pokušení, ale zbav nás od zlého.
5 Yesu ya ce masu, “Wanene a cikinku idan yana da aboki, za ya je wurinsa da tsakar dare ya ce masa, ''Aboki, ka ba ni rancen dunkulen gurasa guda uku,
I řekl k nim: Kdo z vás bude míti přítele, a půjde k němu o půlnoci, a dí jemu: Příteli, půjč mi tří chlebů.
6 da ya ke wani abokina ya iso yanzu daga tafiya, kuma ba ni da abin da zan ba shi ya ci,'
Nebo přítel můj přišel s cesty ke mně, a nemám, co bych předložil před něj.
7 Sai wanda yake ciki, ya amsa, ya ce, 'Kada ka dame ni. Na riga na rufe kofa ta, kuma ni da yarana mun riga mun kwanta. Ba zan iya tashi in ba ka gurasa ba.'
A on vnitř jsa, odpověděl by, řka: Nečiň mi nevole, neb jsou již dveře zavříny, a dítky mé se mnou jsou v pokoji. Nemohuť vstáti a dáti tobě.
8 Na fada maku, ko da bai tashi ya ba ka gurasar ba, a matsayin abokinsa, ba ka ji kunya ba, ka nace da rokonsa, za ya tashi ya ba ka dukan yawan gurasar da kake bukata.
Pravím vám: Ačť nedá jemu, vstana, protože jest přítel jeho, ale však pro nezbednost jeho vstana, dá jemu, kolikožkoli potřebuje.
9 Ni kuma ina ce maku, ku roka za a ba ku; ku nema za ku samu; ku kwankwasa za a bude maku.
I jáť pravím vám: Proste, a budeť vám dáno; hledejte, a naleznete; tlucte, a budeť vám otevříno.
10 Domin dukan wanda yake roko ya na karba; dukan wanda ya ke nema kuma yana samu; kuma wanda yake kwankwasawa, za a bude masa.
Neb každý, kdož prosí, béře; a kdož hledá, nalézá; a tomu, kdož tluče, bude otevříno.
11 Wanne uba ne a cikinku, idan dansa ya tambaye shi kifi, zai ba shi maciji a maimakon kifi?
Kterého pak z vás otce prosil by syn za chléb, zdali kamene podá jemu? Aneb za rybu, zdali místo ryby dá jemu hada?
12 Ko kuwa idan ya tambaye shi kwai, za ya ba shi kunama?
Aneb prosil-li by za vejce, zdali podá jemu štíra?
13 To, da yake ku da kuke masu mugunta kun san ku ba 'yanyan ku abu mai kyau. Yaya fa ga Ubanku wanda yake cikin sama, za ya ba da Ruhu Mai Tsarki ga wadanda suka roke shi?”
Poněvadž tedy vy, zlí jsouce, umíte dobré dary dávati dětem svým, čím více Otec váš nebeský dá Ducha svatého těm, kteříž ho prosí?
14 Wani lokaci, Yesu yana fitar da wani beben aljani. Sa'adda aljanin ya fita, sai mutumin da yake bebe ya yi magana. Sai taron mutanen suka yi mamaki!
I vymítal Ježíš ďábelství, a to bylo němé. Stalo se pak, když vyšlo ďábelství, že mluvil němý. I divili se zástupové.
15 Amma, wadansu daga cikin mutanen suka ce, “Da ikon Ba'alzabuba sarkin aljanu ne yake fitar da aljanu.”
Ale někteří z nich pravili: V Belzebubu, knížeti ďábelském, vymítá ďábly.
16 Wadansu suka gwada shi, suka nemi ya nuna masu wata alama daga sama.
A jiní pokoušejíce ho, znamení s nebe hledali od něho.
17 Amma Yesu da yake ya san tunaninsu, ya ce da su, “Dukan mulkin da ya rabu biyu, gaba da kansa, ya rushe kenan, kuma idan gida ya rabu biyu, gaba da kansa za ya fadi.
Ale on znaje myšlení jejich, řekl jim: Každé království samo v sobě rozdělené pustne, a dům na dům padá.
18 Idan Shaidan ya rabu biyu gaba da kansa, ta yaya mulkinsa zai iya tsayawa? Gama kun ce ina fitar da aljanu ta wurin Ba'alzabuba.
Jestližeť jest pak i satan proti sobě rozdělen, kterakž stane království jeho? Nebo pravíte, že já v Belzebubu vymítám ďábly.
19 Idan ni na fitar da aljanu ta wurin Ba'alzabuba, ta wurin wa wadanda suke bin ku suke fitar da aljanu? Saboda haka, su ne zasu zama masu yi maku shari'a.
Jestliže já v Belzebubu vymítám ďábly, synové vaši v kom vymítají? Protož oni soudcové vaši budou.
20 Amma idan daga wurin Allah na ke fitar da aljanu, to, ya zama ke nan mulkin Allah ya zo wurinku.
Pakliť prstem Božím vymítám ďábly, jistěť jest přišlo k vám království Boží.
21 Idan mutum mai karfi, mai kayan fada ya tsare gidansa, kayansa za su tsira.
Když silný oděnec ostříhá síně své, v pokoji jsou všecky věci, kteréž má.
22 Amma idan wani mutum wanda ya fi shi karfi ya zo ya ci nasara a kansa, zai dauke kayan fadan daga wurin mutumin, kuma ya kwashe kayansa.
Pakli by silnější než on přijda, přemohl jej, všecka odění jeho odejme, v něž úfal, a loupeže jeho rozdělí.
23 Wanda ba ya tare da ni, gaba da ni ya ke yi, kuma wanda ba ya tattarawa tare da ni, watsarwa yake yi.
Kdožť není se mnou, proti mně jest; a kdož neshromažďuje se mnou, rozptylujeť.
24 Idan kazamin ruhu ya fita daga cikin mutum, ya kan bi ta wurin busassun wurare yana neman wurin da zai huta. Idan bai samu ba sai ya ce, 'Bari in koma gidana inda na baro.
Když nečistý duch vyjde od člověka, chodí po místech suchých, hledaje odpočinutí. A nenalezna, dí: Vrátím se do domu svého, odkudž jsem vyšel.
25 Sa'adda ya dawo, ya tarar an share gidan, an kuma gyara shi tsaf.
A přijda, nalezne jej vymetený a ozdobený.
26 Sai ya je ya dauko wadansu aljanu guda bakwai wadanda su ka fi shi mugunta, su zo su zauna a wurin. Sai karshen mutumin nan ya fi farkonsa muni.”
I jde, a přijme k sobě jiných sedm duchů horších sebe, a vejdouce, přebývají tam. I jsou poslední věci člověka toho horší nežli první.
27 Ya zama, lokacin da ya ke fadin wadannan abubuwa, wata mace ta tada muryarta a cikin taron mutanen ta ce da shi, “Mai albarka ne cikin da ya haife ka, da maman da ka sha.”
I stalo se, když on to mluvil, pozdvihši hlasu jedna žena z zástupu, řekla jemu: Blahoslavený život, kterýž tebe nosil, a prsy, kterýchž jsi požíval.
28 Sai shi kuma ya ce, “Masu albarka ne wadanda suke jin maganar Allah suke yin biyayya da ita.”
A on řekl: Ovšem pak blahoslavení, kteříž slyší slovo Boží a ostříhají jeho.
29 Lokacin da mutane suke kara taruwa, sai ya fara cewa, “Wannan tsara, muguwar tsara ce. Ta na neman alama, Ko da yake ba wata alamar da za a bata sai irin ta Yunusa.
A když se zástupové scházeli, počal praviti: Pokolení toto nešlechetné jest. Znamení vyhledává, a znamení jemu nebude dáno, než znamení Jonáše proroka.
30 Domin kamar yadda Yunusa ya zama alama ga mutanen Neneba, haka kuma Dan Mutum za ya zama alama ga wannan tsara.
Nebo jakož Jonáš učiněn byl znamením Ninivitským, takť bude i Syn člověka pokolení tomuto.
31 Sarauniyar Kudu, za ta tsaya ta yi shari'a da mutanen wannan tsara, kuma za ta kashe su, gama ta zo daga wuri mai nisa domin ta saurari hikimar Sulaimanu. Kuma ga wani wanda ya fi Sulaimanu a nan.
Královna od poledne stane na soudu s muži pokolení tohoto, a odsoudí je. Nebo přijela od končin země, aby slyšela moudrost Šalomounovu, a aj, více než Šalomoun tuto!
32 Mutanen Neneba, za su tsaya shari'a da matanen wannan tsara, kuma za su kashe su. Gama sun ji wa'azin Yunusa sun tuba. Kuma ga wani wanda ya fi Yunusa a nan.
Muži Ninivitští povstanou na soudu s pokolením tímto, a odsoudí je. Nebo činili pokání k kázání Jonášovu, a aj, více nežli Jonáš tuto!
33 Ba wanda zai kunna fitila ya boye ta, ko kuwa ya sa ta a karkashin kasko, amma zai sa ta a mazaunin ta domin dukan wanda ya shiga dakin ya ga haske.
Žádný rozsvítě svíci, nepostaví jí do skrýše, ani pod kbelec, ale na svícen, aby ti, kteříž vcházejí, světlo viděli.
34 Idon ku shine fitilar jikinku. Idan idonku yana gani sosai, jikinku zai cika da haske. Amma idan idonku ba ya gani sosai, jikinku zai cika da duhu.
Svíce těla tvého jest oko tvé. Když by tedy oko tvé sprostné bylo, i tělo tvé všecko bude světlé; a pakliť bude nešlechetné, takéť i tělo tvé tmavé bude.
35 Ku yi hankali fa, domin kada hasken da ya ke wurinku ya zama duhu.
Viziž tedy, aby světlo, kteréž jest v tobě, nebylo tmou.
36 Idan dukan jikinku yana cike da haske, babu duhu ko kadan, to sai dukan jikinku ya zama kamar fitilar da take bada haskenta a bisanku.”
Pakli celé tělo tvé světlé bude, nemaje žádné částky tmavé, budeť všecko tak světlé, že tě jako svíce bleskem osvítí.
37 Sa'adda ya gama jawabi, sai wani Bafarise ya ce da shi ya zo gidansa ya ci abinci, sai Yesu ya shiga ya zauna.
A mezi tím když on mluvil, prosil ho jeden farizeus, aby obědval u něho. A všed, posadil se za stůl.
38 Sai Bafarisen ya yi mamaki da ganin bai wanke hannu kafin ya ci abinci ba.
Farizeus pak viděv to, podivil se, že se neumyl před obědem.
39 Amma sai Ubangiji ya ce da shi, “Ku Farisawa kuna tsabtace bayan kofi da bangaji, amma cikin yana cike da kazamta da mugunta.
I řekl Pán k němu: Nyní vy farizeové povrchu konvice a mísy čistíte, ale to, což vnitř jest v vás, plno jest loupeže a nešlechetností.
40 Ku mutane marasa tunani, wanda ya yi wajen, ba shine ya yi cikin ba?
Blázni, zdaliž ten, kterýž učinil, což zevnitř jest, neučinil také i toho, což jest vnitř?
41 Ku bayar da abin da ke ciki ga matalauta, kuma dukan abu zai zamar maku da tsafta.
Ale však i z toho, což máte, dávejte almužnu, a aj, všecky věci vaše čisté budou.
42 Amma kaitonku Farisawa, gama kuna karbar zakka da daddoya da karkashi da kowanne irin ganye na lambu, amma kun watsar da adalci da kaunar Allah. Dole ne a yi adalci, a kaunaci Allah, a yi sauran abubuwan kuma.
Ale běda vám farizeům, kteříž desátky dáváte z máty a z routy a ze všeliké byliny, ale opouštíte soud a lásku Boží; ješto tyto věci měli jste činiti, a oněch neopouštěti.
43 Kaitonku Farisawa, domin kuna so a ba ku wuraren zama masu kyau a cikin masujadai, a kuma yi maku gaisuwar bangirma a cikin kasuwanni.
Běda vám farizeům, nebo milujete první místa v školách a pozdravování na trzích.
44 Kaiton ku, gama kuna kama da kabarbarun da ba yi masu shaida ba, mutane kuwa suna tafiya akansu ba tare da saninsu ba.”
Běda vám, zákoníci a farizeové pokrytci, nebo jste jako hrobové nepatrní, po nichž lidé chodíce, nevědí o tom, co tam jest.
45 Wani malami a cikin shari'ar Yahudawa ya amsa masa ya ce, “Malam, abin da ka ce ya bata mana rai mu ma.”
I odpověděv jeden z zákoníků, řekl jemu: Mistře, tyto věci mluvě, i nám také lehkost činíš.
46 Sai Yesu ya ce, “Kaitonku malaman shari'a! Gama kun dora wa mutane kaya mai nauyi wanda ya fi karfinsu dauka. Amma ku, ko da dan yatsa ba ku taba kayan ba.
A on řekl: I vám zákoníkům běda, nebo obtěžujete lidi břemeny nesnesitelnými, a sami se těch břemen jedním prstem nedotýkáte.
47 Kaiton ku, gama kuna gina abubuwan tunawa a kabuburan annabawa, alhali kuwa kakanni-kakanninku ne suka kashe su.
Běda vám, jenž vzděláváte hroby prorocké, kteréž otcové vaši zmordovali.
48 Ya zama kenan kuna sane da ayyukan kakanni-kakanninku, domin sune suka kashe annabawan da kuke tunawa da su.
A tak osvědčujete a potvrzujete skutků otců vašich. Nebo oni zajisté zmordovali jsou je, vy pak vzděláváte hroby jejich.
49 Saboda wannan daliline hikimar Allah ta ce, ''Zan aika manzanni da annabawa a wurinsu, kuma za su tsananta masu har ma za su kashe wadansu daga cikinsu.'
Protož i Moudrost Boží řekla: Pošliť k nim proroky a apoštoly, a z těch některé mordovati budou, a jiné vyháněti,
50 Wannan tsarar, za ta dauki alhakin jinin dukan annabawan da aka kashe tun kafuwar duniya.
Aby požádáno bylo od tohoto pokolení krve všech proroků, kteráž vylita jest od ustanovení světa,
51 Tun daga jinin Habila, har zuwa jinin Zakariya wanda aka kashe tsakanin bagadi da wuri mai tsarki. I, na gaya ma ku za a nemi hakin su a wurin wannan tsarar
Od krve Abelovy až do krve Zachariášovy, kterýž zahynul mezi oltářem a chrámem. Jistě, pravím vám, požádáno bude od pokolení tohoto.
52 Kaitonku malaman shari'a na Yahudawa, domin kun dauke mabudin sani, ku da kanku ba ku shiga ba, kuma kun hana masu shiga su shiga.”
Běda vám zákoníkům, nebo jste vzali klíč umění; sami jste nevešli, a těm, kteříž vcházeli, zbránili jste.
53 Bayan da Yesu ya bar nan wurin, Marubuta da Farisawa suka yi gaba da shi, suka yi jayayya da shi a kan abubuwa da yawa,
A když jim to mluvil, počali zákoníci a farizeové přísně jemu odpírati, a k mnohým řečem příčiny jemu dávati,
54 suna kokari su kafa masa tarko domin su kama shi a cikin kalmomin da yake fadi.
Ukládajíce o něm, a hledajíce popadnouti něco z úst jeho, aby jej obžalovali.