< Yahuda 1 >

1 Yahuza, bawan Yesu Almasihu kuma dan'uwan Yakubu, zuwa ga kirayayyu, kaunatattu a cikin Allah Uba, kebabbu domin Yesu Kristi:
Ἰούδας Ἰησοῦ Χριστοῦ δοῦλος, ἀδελφὸς δὲ Ἰακώβου, τοῖς ἐν θεῷ πατρὶ ⸀ἠγαπημένοιςκαὶ Ἰησοῦ Χριστῷ τετηρημένοις κλητοῖς·
2 bari jinkai da salama da kauna su ribabanya a gare ku.
ἔλεος ὑμῖν καὶ εἰρήνη καὶ ἀγάπη πληθυνθείη.
3 Kaunatattu, ina iyakar kokari in rubuta maku game da ceton mu duka, ya zama dole in gargade ku sosai game da bangaskiya wadda aka mika wa masu bi sau daya tak ba kari.
Ἀγαπητοί, πᾶσαν σπουδὴν ποιούμενος γράφειν ὑμῖν περὶ τῆς κοινῆς ⸀ἡμῶνσωτηρίας ἀνάγκην ἔσχον γράψαι ὑμῖν παρακαλῶν ἐπαγωνίζεσθαι τῇ ἅπαξ παραδοθείσῃ τοῖς ἁγίοις πίστει.
4 Don wasu mutane sun sadado sun shigo da sanda a asirce wadanda an rubuta game da hukuncin su tun da dadewa-mutane marasa imani, wanda suka canza alherin Allah zuwa lalata, kuma sun karyata makadaicin Shugaba da Ubangijinmu, Yesu Almasihu.
παρεισέδυσαν γάρ τινες ἄνθρωποι, οἱ πάλαι προγεγραμμένοι εἰς τοῦτο τὸ κρίμα, ἀσεβεῖς, τὴν τοῦ θεοῦ ἡμῶν χάριτα μετατιθέντες εἰς ἀσέλγειαν καὶ τὸν μόνον ⸀δεσπότηνκαὶ κύριον ἡμῶν Ἰησοῦν Χριστὸν ἀρνούμενοι.
5 Ina so in tunashe ku-ko da shike kun rigaya kun san abin, da cewa Allah ya ceci wasu mutane daga kasar masar, amma daga baya ya hallaka wadanda basu ba da gaskiya ba.
Ὑπομνῆσαι δὲ ὑμᾶς βούλομαι, εἰδότας ⸂ὑμᾶς ἅπαξ ⸀πάντα ὅτι ⸀Ἰησοῦςλαὸν ἐκ γῆς Αἰγύπτου σώσας τὸ δεύτερον τοὺς μὴ πιστεύσαντας ἀπώλεσεν,
6 Kuma mala'iku wadanda ba su rike matsayin ikon su ba, amma suka bar wurin zaman su na ainihi-Allah ya tsare su a sarka na har'abada a cikin bakin duhu domin babban ranar shari'a. (aïdios g126)
ἀγγέλους τε τοὺς μὴ τηρήσαντας τὴν ἑαυτῶν ἀρχὴν ἀλλὰ ἀπολιπόντας τὸ ἴδιον οἰκητήριον εἰς κρίσιν μεγάλης ἡμέρας δεσμοῖς ἀϊδίοις ὑπὸ ζόφον τετήρηκεν· (aïdios g126)
7 Suna nan kamar Saduma da Gwamrata da kuma biranen da ke kewaye da su, wadanda suka ba da kansu ga fasikanci suna bin sha'awoyi wanda ba na dabi'a ba. Aka mai da su abin misalin wadanda suka sha wuta mara matuka. (aiōnios g166)
ὡς Σόδομα καὶ Γόμορρα καὶ αἱ περὶ αὐτὰς πόλεις, τὸν ὅμοιον ⸂τρόπον τούτοις ἐκπορνεύσασαι καὶ ἀπελθοῦσαι ὀπίσω σαρκὸς ἑτέρας, πρόκεινται δεῖγμα πυρὸς αἰωνίου δίκην ὑπέχουσαι. (aiōnios g166)
8 Haka kuma, wadannan masu mafarkan suna lalatar da jikinsu. Suna raina masu mulki, kuma suna fadar miyagun abubuwa a kan masu daukaka.
Ὁμοίως μέντοι καὶ οὗτοι ἐνυπνιαζόμενοι σάρκα μὲν μιαίνουσιν, κυριότητα δὲ ἀθετοῦσιν, δόξας δὲ βλασφημοῦσιν.
9 Amma ko Mika'ilu babban mala'ika, a lokacin da yake jayyaya da muhawara da shaidan a kan gawar Musa, bai kuskura ya fadi wata kalmar hukunci a kansa ba. Maimakon haka ya ce, “Bari Ubangiji ya tsauta maka!''
ὁ δὲ Μιχαὴλ ὁ ἀρχάγγελος, ὅτε τῷ διαβόλῳ διακρινόμενος διελέγετο περὶ τοῦ Μωϋσέως σώματος, οὐκ ἐτόλμησεν κρίσιν ἐπενεγκεῖν βλασφημίας, ἀλλὰ εἶπεν· Ἐπιτιμήσαι σοι κύριος.
10 Amma waddannan mutane suna kawo batanci game da dukan abin da ba su gane ba. Wadannan mutane masu halin dabbobi ne, suna kwa jawo wa kansu hallaka kenan.
οὗτοι δὲ ὅσα μὲν οὐκ οἴδασιν βλασφημοῦσιν, ὅσα δὲ φυσικῶς ὡς τὰ ἄλογα ζῷα ἐπίστανται, ἐν τούτοις φθείρονται.
11 Kaiton su! Domin sun bi hanyar Kayinu, kuma sun tsunduma cikin kuskuren Bal'amu domin samun riba. Suka hallaka cikin husuma irin ta Kora.
οὐαὶ αὐτοῖς, ὅτι τῇ ὁδῷ τοῦ Κάϊν ἐπορεύθησαν, καὶ τῇ πλάνῃ τοῦ Βαλαὰμ μισθοῦ ἐξεχύθησαν, καὶ τῇ ἀντιλογίᾳ τοῦ Κόρε ἀπώλοντο.
12 Wadannan hatsari ne a boye cikin bukukuwan ku na kauna. Suna shagali ba kunya ba tsoro, suna ciyar da kansu kadai. Su holokon hadari ne marar ruwa, wanda iska ke korar sa. Su itatuwa ne shirim ba yaya, mattatu ribi biyu, tumbukakku tun daga saiwa.
οὗτοί εἰσιν ⸀οἱἐν ταῖς ἀγάπαις ὑμῶν σπιλάδες συνευωχούμενοι, ἀφόβως ἑαυτοὺς ποιμαίνοντες, νεφέλαι ἄνυδροι ὑπὸ ἀνέμων παραφερόμεναι, δένδρα φθινοπωρινὰ ἄκαρπα δὶς ἀποθανόντα ἐκριζωθέντα,
13 Su rakuman teku ne masu hauka, suna fahariya cikin kumfar kunyar su. Su kamar taurari ne masu tartsatsi. Wadanda aka tanada wa duhu baki kirin na har abada. (aiōn g165)
κύματα ἄγρια θαλάσσης ἐπαφρίζοντα τὰς ἑαυτῶν αἰσχύνας, ἀστέρες πλανῆται οἷς ὁ ζόφος τοῦ σκότους εἰς αἰῶνα τετήρηται. (aiōn g165)
14 Ahnuhu, mutum na bakwai daga Adamu, ya yi anabci game da su cewa, “Duba, Ubangiji zai zo da tsarkakan sa dubun dubbai.
Προεφήτευσεν δὲ καὶ τούτοις ἕβδομος ἀπὸ Ἀδὰμ Ἑνὼχ λέγων· Ἰδοὺ ἦλθεν κύριος ἐν ἁγίαις μυριάσιν αὐτοῦ,
15 Domin ya zartar da hukunci a kan dukan kowa, ya kuma cakune dukan marasa da'a a cikin dukan ayyukan su na rashin da'a wanda suka aikata a hanyar da bata cancanta ba, da kuma kalmomi masu kaifi da masu zunubi suka fada game da shi.”
ποιῆσαι κρίσιν κατὰ πάντων καὶ ἐλέγξαι ⸂πάντας τοὺς ἀσεβεῖς περὶ πάντων τῶν ἔργων ἀσεβείας αὐτῶν ὧν ἠσέβησαν καὶ περὶ πάντων τῶν σκληρῶν ὧν ἐλάλησαν κατʼ αὐτοῦ ἁμαρτωλοὶ ἀσεβεῖς.
16 Wadannan masu cecekuce ne, masu gunaguni, wadanda ke bin sha'awar su ta mugunta, masu tinkaho da fahariya, masu bambadanci domin ribar kansu.
οὗτοί εἰσιν γογγυσταί, μεμψίμοιροι, κατὰ τὰς ἐπιθυμίας ⸀αὐτῶνπορευόμενοι, καὶ τὸ στόμα αὐτῶν λαλεῖ ὑπέρογκα, θαυμάζοντες πρόσωπα ὠφελείας χάριν.
17 Amma ku, kaunatattu, ku tuna da kalmomin da manzannin Yesu Almasihunmu suka gaya maku tun da.
Ὑμεῖς δέ, ἀγαπητοί, μνήσθητε τῶν ῥημάτων τῶν προειρημένων ὑπὸ τῶν ἀποστόλων τοῦ κυρίου ἡμῶν Ἰησοῦ Χριστοῦ·
18 Sun ce maku, “A cikin kwanaki na karshe, za a samu masu ba'a, wadanda ke bin sha'awoyin su na rashin ibada,”
ὅτι ἔλεγον ⸀ὑμῖν ⸂Ἐπʼ ἐσχάτου χρόνου ἔσονται ἐμπαῖκται κατὰ τὰς ἑαυτῶν ἐπιθυμίας πορευόμενοι τῶν ἀσεβειῶν.
19 Wadannan mutane masu haddasa tsatsaguwa ne, kuma su yan duniya ne, ba su kuma da Ruhu.
οὗτοί εἰσιν οἱ ἀποδιορίζοντες, ψυχικοί, πνεῦμα μὴ ἔχοντες.
20 Amma ku, kaunatattu, ku gina kanku a cikin mafificiyar bangaskiyar ku mai daraja, kuma kuna addu'a a cikin Ruhu Mai Tsarki.
ὑμεῖς δέ, ἀγαπητοί, ⸂ἐποικοδομοῦντες ἑαυτοὺς τῇ ἁγιωτάτῃ ὑμῶν πίστει, ἐν πνεύματι ἁγίῳ προσευχόμενοι,
21 Ku rike kanku a cikin kaunar Allah, kuna kuma jiran jinkan Ubangijinmu Yesu Almasihu wanda ke kawo rai na har abada. (aiōnios g166)
ἑαυτοὺς ἐν ἀγάπῃ θεοῦ τηρήσατε προσδεχόμενοι τὸ ἔλεος τοῦ κυρίου ἡμῶν Ἰησοῦ Χριστοῦ εἰς ζωὴν αἰώνιον. (aiōnios g166)
22 Ku nuna jinkai ga masu shakku. Ceci wadansu ta wurin fizge su daga wuta.
καὶ οὓς μὲν ⸀ἐλεᾶτε ⸂διακρινομένους,
23 Ga wadansu kuma ku nuna jinkai da rawar jiki, kuyi kyamar koda tufafin jikinsu ma.
οὓς δὲ σῴζετε ἐκ πυρὸς ἁρπάζοντες, οὓς δὲ ἐλεᾶτε ἐν φόβῳ⸃, μισοῦντες καὶ τὸν ἀπὸ τῆς σαρκὸς ἐσπιλωμένον χιτῶνα.
24 Yanzu, zuwa ga wanda yake da iko ya hana ku tuntube, ya kuma sa ku tsaya a gaban madaukakiyar kasancewarsa, marasa abin zargi da kuma murna mai yawa,
Τῷ δὲ δυναμένῳ φυλάξαι ⸀ὑμᾶςἀπταίστους καὶ στῆσαι κατενώπιον τῆς δόξης αὐτοῦ ἀμώμους ἐν ἀγαλλιάσει
25 zuwa ga Allah makadaici mai ceton mu ta wurin Yesu Almasihu Ubangijinmu, daukaka, da girma, da mulki, da iko su kasance, kamin dukan lokuta, yanzu, da har abada. Amin. (aiōn g165)
⸀μόνῳθεῷ σωτῆρι ἡμῶν ⸂διὰ Ἰησοῦ Χριστοῦ τοῦ κυρίου ἡμῶν ⸀δόξαμεγαλωσύνη κράτος καὶ ἐξουσία ⸂πρὸ παντὸς τοῦ αἰῶνος καὶ νῦν καὶ εἰς πάντας τοὺς αἰῶνας· ἀμήν. (aiōn g165)

< Yahuda 1 >