< Yahuda 1 >
1 Yahuza, bawan Yesu Almasihu kuma dan'uwan Yakubu, zuwa ga kirayayyu, kaunatattu a cikin Allah Uba, kebabbu domin Yesu Kristi:
Juudaselt, Jeesuse Kristuse sulaselt ja Jaakobuse vennalt, Neile kutsutuile, kes on Jumalas Isas armastatud ja Jeesuses Kristuses hoitud:
2 bari jinkai da salama da kauna su ribabanya a gare ku.
Halastust ja rahu ja armastust olgu teil rohkesti!
3 Kaunatattu, ina iyakar kokari in rubuta maku game da ceton mu duka, ya zama dole in gargade ku sosai game da bangaskiya wadda aka mika wa masu bi sau daya tak ba kari.
Armsad, olles täis indu kirjutada teile meie ühisest päästest, leidsin vajalikuna kirjutada ja teid üles kutsuda võitlema usu eest, mis oli kord usaldatud Jumala pühale rahvale.
4 Don wasu mutane sun sadado sun shigo da sanda a asirce wadanda an rubuta game da hukuncin su tun da dadewa-mutane marasa imani, wanda suka canza alherin Allah zuwa lalata, kuma sun karyata makadaicin Shugaba da Ubangijinmu, Yesu Almasihu.
Sest teie sekka on imbunud mõningad inimesed, kes juba ammu on kirja pandud kohtu jaoks. Need on jumalakartmatud inimesed, kes meie Jumala armu kõlvatuseks moonutades salgavad ära meie ainsa valitseja ja meie Issanda Jeesuse Kristuse.
5 Ina so in tunashe ku-ko da shike kun rigaya kun san abin, da cewa Allah ya ceci wasu mutane daga kasar masar, amma daga baya ya hallaka wadanda basu ba da gaskiya ba.
Ja kuigi te seda kõike teate, tahan tuletada teile meelde, et Issand, kes rahva ühel korral päästis Egiptusest, hävitas teisel korral need, kes ei uskunud.
6 Kuma mala'iku wadanda ba su rike matsayin ikon su ba, amma suka bar wurin zaman su na ainihi-Allah ya tsare su a sarka na har'abada a cikin bakin duhu domin babban ranar shari'a. (aïdios )
Ja ingleid, kes ei hoidnud kinni oma kõrgest seisusest, vaid hülgasid oma eluaseme, on ta hoidnud pimeduses, seotuna igaveste ahelatega suure päeva kohtuks (aïdios )
7 Suna nan kamar Saduma da Gwamrata da kuma biranen da ke kewaye da su, wadanda suka ba da kansu ga fasikanci suna bin sha'awoyi wanda ba na dabi'a ba. Aka mai da su abin misalin wadanda suka sha wuta mara matuka. (aiōnios )
Nii nagu Soodom, Gomorra ja nende ümberkaudsed linnad, kes samal kombel hoorasid nagu need inglid ning ebaloomulikule ihale andusid, on hoiatavaks näiteks igavese tule karistusest. (aiōnios )
8 Haka kuma, wadannan masu mafarkan suna lalatar da jikinsu. Suna raina masu mulki, kuma suna fadar miyagun abubuwa a kan masu daukaka.
Aga samuti rüvetavad ka need unenägijad oma ihu, lükkavad tagasi taevase autoriteedi ja teotavad aukandjaid vaime.
9 Amma ko Mika'ilu babban mala'ika, a lokacin da yake jayyaya da muhawara da shaidan a kan gawar Musa, bai kuskura ya fadi wata kalmar hukunci a kansa ba. Maimakon haka ya ce, “Bari Ubangiji ya tsauta maka!''
Ometi peaingel Miikaelgi, kui ta vaidles sõnasõjas kuradiga Moosese surnukeha pärast, ei julgenud lausuda teotavat otsust, vaid ütles: „Issand sõidelgu sind!“
10 Amma waddannan mutane suna kawo batanci game da dukan abin da ba su gane ba. Wadannan mutane masu halin dabbobi ne, suna kwa jawo wa kansu hallaka kenan.
Need aga teotavad kõike, millest nad midagi ei taipa, aga millest nad oma ihu tungide kaudu kui arutud loomad aru saavad, selles nad hävitavad end.
11 Kaiton su! Domin sun bi hanyar Kayinu, kuma sun tsunduma cikin kuskuren Bal'amu domin samun riba. Suka hallaka cikin husuma irin ta Kora.
Häda neile, sest nad on läinud Kaini teed ja tormanud tasu eest Bileami eksitusse, ja Korahi kombel vastu hakates on toonud endale hukatuse!
12 Wadannan hatsari ne a boye cikin bukukuwan ku na kauna. Suna shagali ba kunya ba tsoro, suna ciyar da kansu kadai. Su holokon hadari ne marar ruwa, wanda iska ke korar sa. Su itatuwa ne shirim ba yaya, mattatu ribi biyu, tumbukakku tun daga saiwa.
Nemad on teie armastussöömaaegadel häbiplekid, kes kartmatult teiega koos pidutsedes iseennast nuumavad. Nad on veeta pilved, mida tuul ringi kannab, viljatud sügispuud, kahekordselt surnud, juurtega üles kistud,
13 Su rakuman teku ne masu hauka, suna fahariya cikin kumfar kunyar su. Su kamar taurari ne masu tartsatsi. Wadanda aka tanada wa duhu baki kirin na har abada. (aiōn )
metsikud merelained, mis vahutavad välja oma häbi, ekslevad tähed, kelle jaoks on määratud pilkane pimedus igaveseks ajaks. (aiōn )
14 Ahnuhu, mutum na bakwai daga Adamu, ya yi anabci game da su cewa, “Duba, Ubangiji zai zo da tsarkakan sa dubun dubbai.
Nendest on prohvetlikult kõnelenud Eenok, Aadama järglane seitsmendas sugupõlves: „Vaata, Issand tuleb mitmekümne tuhande pühaga
15 Domin ya zartar da hukunci a kan dukan kowa, ya kuma cakune dukan marasa da'a a cikin dukan ayyukan su na rashin da'a wanda suka aikata a hanyar da bata cancanta ba, da kuma kalmomi masu kaifi da masu zunubi suka fada game da shi.”
pidama kohut kõigi üle ja karistama igaüht kõikide nende jumalakartmatute tegude eest, mida nad on teinud, ja kõikide ränkade sõnade eest, mida jumalakartmatud patused on tema vastu rääkinud.“
16 Wadannan masu cecekuce ne, masu gunaguni, wadanda ke bin sha'awar su ta mugunta, masu tinkaho da fahariya, masu bambadanci domin ribar kansu.
Need on rahulolematud saatuse üle nurisejad, kes elavad oma himude järgi ja kelle suu räägib kiitlevaid sõnu, ja nad meelitavad inimesi omakasu pärast.
17 Amma ku, kaunatattu, ku tuna da kalmomin da manzannin Yesu Almasihunmu suka gaya maku tun da.
Teie aga, armsad, pidage meeles, mida meie Issanda Jeesuse Kristuse apostlid ennustasid;
18 Sun ce maku, “A cikin kwanaki na karshe, za a samu masu ba'a, wadanda ke bin sha'awoyin su na rashin ibada,”
kui nad teile ütlesid: „Viimsel ajal tuleb pilkajaid, kes elavad oma jumalakartmatute himude järgi.“
19 Wadannan mutane masu haddasa tsatsaguwa ne, kuma su yan duniya ne, ba su kuma da Ruhu.
Need on inimesed, kes tekitavad lõhenemisi, maised hinged, kellel ei ole Vaimu.
20 Amma ku, kaunatattu, ku gina kanku a cikin mafificiyar bangaskiyar ku mai daraja, kuma kuna addu'a a cikin Ruhu Mai Tsarki.
Teie aga, armsad, rajage endid oma kõige pühamale usule ja palvetage Pühas Vaimus,
21 Ku rike kanku a cikin kaunar Allah, kuna kuma jiran jinkan Ubangijinmu Yesu Almasihu wanda ke kawo rai na har abada. (aiōnios )
ja hoidke endid nõnda Jumala armastuses ja oodake meie Issanda Jeesuse Kristuse halastust igaveseks eluks. (aiōnios )
22 Ku nuna jinkai ga masu shakku. Ceci wadansu ta wurin fizge su daga wuta.
Halastage nende peale, kes kahtlevad;
23 Ga wadansu kuma ku nuna jinkai da rawar jiki, kuyi kyamar koda tufafin jikinsu ma.
päästke nad, tõmmake nad tulest välja; teiste peale halastage kartuses, vihates lihaliku loomuse poolt rüvetatud riideidki.
24 Yanzu, zuwa ga wanda yake da iko ya hana ku tuntube, ya kuma sa ku tsaya a gaban madaukakiyar kasancewarsa, marasa abin zargi da kuma murna mai yawa,
Ent temale, kes suudab teid takistada komistamast ja asetada laitmatuna oma kirkuse palge ette ülevoolavas rõõmus,
25 zuwa ga Allah makadaici mai ceton mu ta wurin Yesu Almasihu Ubangijinmu, daukaka, da girma, da mulki, da iko su kasance, kamin dukan lokuta, yanzu, da har abada. Amin. (aiōn )
ainsale Jumalale, meie Päästjale, Jeesuse Kristuse, meie Issanda läbi, olgu au, auhiilgus, võimus ja meelevald enne ajastuid, nüüd ja igavesti! Aamen. (aiōn )