< Yohanna 20 >

1 To da sassafe ranar farko ta mako, da sauran duhu, Maryamu Magadaliya ta zo kabarin, ta tarar an kawar da dutsen daga kabarin.
Now on the first day of the week, Mary Magdalene went early, while it was still dark, to the tomb, and saw that the stone had been taken away from the tomb.
2 Sai ta ruga da gudu zuwa wurin Saminu Bitrus tare da almajirin nan da Yesu ke kauna, tace masu, “Sun dauke Ubangiji daga kabarin, bamu kuwa san inda aka sa shi ba.”
Therefore she ran and came to Simon Peter and to the other disciple whom Jesus loved, and said to them, “They have taken away the Lord out of the tomb, and we do not know where they have laid him!”
3 Sai Bitrus tare da almajirin nan suka fita, kuma suka tafi kabarin,
Therefore Peter and the other disciple went out, and they went toward the tomb.
4 dukansu suka ruga da gudu tare, amma daya almajirin ya riga Bitrus isowa kabarin,
They both ran together. The other disciple outran Peter and came to the tomb first.
5 Sai ya sunkuya ya leka ciki, ya ga likkafanin lillin a wurin, amma fa bai shiga ciki ba.
Stooping and looking in, he saw the linen cloths lying there; yet he did not enter in.
6 Sai Saminu Bitrus ya iso daga bayansa sai ya shiga kabarin, ya tarar da likkafanin lillin a ajiye.
Then Simon Peter came, following him, and entered into the tomb. He saw the linen cloths lying,
7 sai fallen kuma da yake kansa. Ba'a ajiye tare da likkafanin ba amma aka linkeshi aka ajiye shi daban.
and the cloth that had been on his head, not lying with the linen cloths, but rolled up in a place by itself.
8 Sai almajirin nan da ya riga isa kabarin shi ma ya shiga ya gani, sai ya ba da gaskiya.
So then the other disciple who came first to the tomb also entered in, and he saw and believed.
9 Har ya zuwa wannan lokacin basu san nassin daya ce zai tashi daga matattu ba.
For as yet they did not know the Scripture, that he must rise from the dead.
10 Sai almajiran suka sake komawa gida kuma.
So the disciples went away again to their own homes.
11 Amma Maryamu tana tsaye a bakin kabarin tana kuka. Yayin da take kuka, sai ta sunkuya ta leka cikin kabarin.
But Mary was standing outside at the tomb weeping. So as she wept, she stooped and looked into the tomb,
12 Sai ta ga mala'iku guda biyu cikin fararen kaya zaune, daya ta wurin kai daya kuma ta wurin kafafu inda aka kwantar da Yesu.
and she saw two angels in white sitting, one at the head and one at the feet, where the body of Jesus had lain.
13 Sukace mata, “Uwargida don me kike kuka? Sai tace masu, “Domin sun dauke Ubangijina, ban kuwa san inda suka ajiye shi ba.
They asked her, “Woman, why are you weeping?” She said to them, “Because they have taken away my Lord, and I do not know where they have laid him.”
14 Bayan ta fadi haka, ta juya sai ta ga Yesu tsaye a wurin. Amma bata san cewa Yesu bane,
When she had said this, she turned around and saw Jesus standing, and did not know that it was Jesus.
15 Yesu yace mata, “Uwargida, me yasa kike kuka? Wa kuma kike nema? Domin tana zaton shine mai kula da lambun, sai tace masa, “Maigida in kaine ka dauke shi, gaya mani inda ka sa shi, ni kuwa in dauke shi.”
Jesus said to her, “Woman, why are you weeping? Who are you looking for?” She, supposing him to be the gardener, said to him, “Sir, if you have carried him away, tell me where you have laid him, and I will take him away.”
16 Yesu yace mata, “Maryamu”. Sai ta juya, tace masa da Armaniyanci “Rabboni!” wato mallam.
Jesus said to her, “Mary.” She turned and said to him, “Rabboni!” which is to say, “Teacher!”
17 Yesu yace mata, kada ki taba ni, domin har yanzu ban hau wurin Uba ba tukuna, amma kije wurin 'yan'uwana kice masu, zan je wurin Ubana da Ubanku, Allahna da kuma Allahnku”.
Jesus said to her, “Do not hold me, for I have not yet ascended to my Father; but go to my brothers and tell them, ‘I am ascending to my Father and your Father, to my God and your God.’”
18 Maryamu Magadaliya ta je tace wa almajiran, “Na ga Ubangiji” Ta kuma ce ya fada mata wadannan abubuwa.
Mary Magdalene came and told the disciples that she had seen the Lord, and that he had said these things to her.
19 Da yamma a wannan rana, a rana ta farko ta mako, almajiran suna kulle a daki saboda tsoron Yahudawa, Yesu yazo ya tsaya a tsakaninsu, yace “Salama Agareku”.
When therefore it was evening on that day, the first day of the week, and when the doors were locked where the disciples were assembled, for fear of the Jews, Jesus came and stood in the middle and said to them, “Peace be to you.”
20 Bayan ya fadi haka, sai ya nuna masu hannuwansa da kuibinsa. Da almajiran suka ga Ubangiji, sai suka yi farin ciki.
When he had said this, he showed them his hands and his side. The disciples therefore were glad when they saw the Lord.
21 Yesu ya sake ce masu, “salama agareku. “Kamar yadda Uba ya aiko ni, haka Ni ma na aike ku”.
Jesus therefore said to them again, “Peace be to you. As the Father has sent me, even so I send you.”
22 Da Yesu ya fadi haka, sai ya hura masu lumfashinsa, yace masu, “Ku karbi Ruhu Mai Tsarki.
When he had said this, he breathed on them, and said to them, “Receive the Holy Spirit!
23 Duk wanda kuka gafarta wa zunubai, an gafarta masa; kowa kuka rike zunubansa, an rikesu.”
If you forgive anyone’s sins, they have been forgiven them. If you retain anyone’s sins, they have been retained.”
24 Toma, daya daga cikin sha biyun, wanda ake kira Dan Tagwai, baya tare dasu lokacin da Yesu ya bayyana.
But Thomas, one of the twelve, called Didymus, was not with them when Jesus came.
25 Sauran almajiran sukace masa “Mun ga Ubangiji”. Sai yace masu, “In ban ga gurbin kusoshi a hannuwansa ba, in sa yatsana a gurbin kusoshin ba, in kuma sa hannuna cikin kuibinsa ba, ba zan bada gaskiya ba.
The other disciples therefore said to him, “We have seen the Lord!” But he said to them, “Unless I see in his hands the print of the nails, put my finger into the print of the nails, and put my hand into his side, I will not believe.”
26 Bayan kwana takwas har wa yau almajiran na cikin gida, Toma ma na tare dasu, kofofin suna kulle, sai ga Yesu a tsakaninsu yace, “Salama agareku”.
After eight days, again his disciples were inside and Thomas was with them. Jesus came, the doors being locked, and stood in the middle, and said, “Peace be to you.”
27 Sa'an nan yace wa Toma, “Iso nan da yatsanka, dubi hannuwana. Miko hannunka kuma kasa a kuibina, kada ka zama marar bada gaskiya, sai dai, mai bada gaskiya”.
Then he said to Thomas, “Reach here your finger, and see my hands. Reach here your hand, and put it into my side. Do not be unbelieving, but believing.”
28 Toma ya amsa yace “Ya Ubangijina da Allahna!”
Thomas answered him, “My Lord and my God!”
29 Yesu yace masa, “Wato saboda ka gan ni, ka bada gaskiya? Albarka ta tabbata ga wadanda basu gani ba, amma kuwa sun bada gaskiya.
Jesus said to him, “Because you have seen me, you have believed. Blessed are those who have not seen and have believed.”
30 Yesu yayi wadansu alamu da yawa dabam dabam a gaban almajiransa, wadanda ba'a rubuta a littafin nan ba.
Therefore Jesus did many other signs in the presence of his disciples, which are not written in this book;
31 Amma an rubuta wadannan ne, domin ku bada gaskiya Yesu shine Almasihu, Dan Allah, ta wurin gaskatawa kuma ku sami rai cikin sunansa.
but these are written that you may believe that Jesus is the Christ, the Son of God, and that believing you may have life in his name.

< Yohanna 20 >