< Yohanna 2 >
1 Bayan kwana uku, akwai aure a Kana ta Galili, mahaifiyar Yesu kuma tana wurin.
2 An gayyaci Yesu da almajiransa zuwa auren.
3 Da ruwan inabin ya kare, maihafiyar Yasu tace masa, “basu da ruwan inabi.”
4 Yesu yace mata, “Mace, me yasa kika zo wurina? Lokaci na bai yi ba tukuna”.
5 Maihafiyarsa tace wa ma'aikatan, “Ku yi duk abin da yace maku.”
6 To akwai randunan ruwa na dutse guda shidda a wurin wadanda Yahudawa ke amfani da su domin al'adansu na tsarkakewa, kowace zata iya daukar durom guda.
7 Yesu yace masu, “Cika randunan da ruwa”. Sai suka cika randunan makil.
8 Sai yace wa ma'aikatan, “Ku diba daga ciki ku kai wa shugaban biki.” Sai suka yi hakannan.
9 Shugaban bikin ya dandana ruwan da ya zama ruwan inabin, amma bai san inda ya fito ba (amma ma'aikatan wadanda suka jawo ruwan sun sani). Sai ya kira ango
10 yace masa, “Kowane mutum yakan raba ruwan inabi mai kyau da farko, kafin mai arhar bayan an shanye mai kyaun. Amma kai ka ajiye mai kyaun sai yanzu.”
11 Wannan alama ta farko ce da Yesu yayi a Kana ta Galili, ya kuma bayyana daukakarsa, almajiransa kuma suka gaskata da shi.
12 Bayan wannan, Yesu, da mahaifiyarsa, da 'yan'uwansa da almajiransa suka tafi Kafarnahum, kuma suka zauna can wasu 'yan kwanaki.
13 To idin ketarewa na Yahudawa ya kusato, Yesu kuwa ya wuce zuwa Urushalima.
14 Ya iske wadanda suke sayar da shanu da tumaki da tantabaru, masu canjin kudi kuma na zaune a wurin.
15 Sai yayi tsumingiya da igiyoyi ya kore su duka daga cikin haikalin, duk da tumakin da shanun. Sai ya watsar da sulallan masu canjin kudin ya birkitar da teburansu.
16 Yace wa masu sayar da tantabaru, “Ku fitar da wadannan abubuwa daga nan. Ku daina maida gidan Ubana wurin kasuwanci.”
17 Almajiransa suka tuna a rubuce yake, “Himma domin gidanka za ta cinye ni.”
18 Sai shugabannin Yahudawa suka amsa suka ce masa, “Wace alama za ka nuna mana, da shike kana yin wadannan abubuwan?”
19 Yesu ya amsa, “Ku rushe wannan haikali, kuma a cikin kwana uku zan gina shi.”
20 Sai shugabanin Yahudawa suka ce, “An dauki shekaru arba'in da shidda kamin a gama gina wannan haikalin, za ka dau kwanaki uku kadai wajen gina shi?”
21 Amma yana nufin haikali na jikinsa ne.
22 Bayan da aka tashe shi daga matattu, sai almajiransa suka tuna ya fadi haka, suka kuma ba da gaskiya ga nassi da wannan kalami da Yesu ya fada.
23 Kuma, da yana Urushalima a idin ketarewa, a lokacin idin, mutane da yawa suka gaskata ga sunansa, sa'adda suka ga alamun da ya yi.
24 Amma Yesu bai yadda da su ba domin ya san su duka,
25 saboda baya bukatar wani ya shaida masa game da mutum, domin ya san abinda ke cikin sa.