< Yohanna 16 >

1 “Na fada maku wannan ne domin kada kuyi tuntube.
"Dette har jeg talt til eder, for at I ikke skulle forarges.
2 Zasu fitar da ku daga majami'u. Amma, sa'a tana zuwa, wadda idan wani ya kasheku, zai yi zaton aikin Allah yake yi.
De skulle udelukke eder af Synagogerne, ja, den Tid skal komme, at hver den, som slår eder ihjel, skal mene, at han viser Gud en Dyrkelse.
3 Za suyi haka ne kuwa domin ba su san Uban ko ni ba.
Og dette skulle de gøre, fordi de hverken kende Faderen eller mig.
4 Na fada maku wadannan abubuwa ne domin in lokacin da zasu faru yayi, ku tuna na fada maku.” Ban fada maku wadannan abubuwa ba tun da farko, domin ina tare da ku.
Men dette har jeg talt til eder, for at I, når Timen kommer, skulle komme i Hu, at jeg har sagt eder det; men dette sagde jeg eder ikke fra Begyndelsen, fordi jeg var hos eder.
5 Yanzu kuwa za ni wurin wanda ya aiko ni, duk da haka a cikinku, ba wanda ya tambaye ni, 'Ina za ka?'
Men nu går jeg hen til ham, som sendte mig, og ingen af eder spørger mig: Hvor går du hen?
6 Amma saboda na fada maku wadannan abubuwa, bakin ciki ya cika zuciyarku.
Men fordi jeg har talt dette til eder, har Bedrøvelsen opfyldt eders Hjerte.
7 Amma ina gaya maku gaskiya: zai fi ye maku in na tafi. Domin in ban tafi ba, Mai Ta'aziyya ba zai zo gare ku ba, in kuwa na tafi, zan aiko shi gare ku.
Men jeg siger eder Sandheden: Det er eder gavnligt, at jeg går bort, thi går jeg ikke bort, kommer Talsmanden ikke til eder; men går jeg bort, så vil jeg sende ham til eder.
8 Idan kuwa ya zo, Mai Ta'aziyyar zai fadarkar da duniya a kan zunubi, da adalci, da kuma hukunci.
Og når han kommer, skal han overbevise Verden om Synd og om Retfærdighed og om Dom.
9 Game da zunubi, domin basu gaskata da ni ba,
Om Synd, fordi de ikke tro på mig;
10 Game da adalci, domin za ni wurin Uba, kuma ba za ku sake ganina ba,
men om Retfærdighed, fordi jeg går til min Fader, og I se mig ikke længer;
11 game da hukunci kuma, domin an yanke wa mai mulki duniyan nan hukunci.
men om Dom, fordi denne Verdens Fyrste er dømt.
12 “Akwai abubuwa da yawa da zan gaya maku, amma ba za ku iya fahimta a yanzu ba.
Jeg har endnu meget at sige eder; men I kunne ikke bære det nu.
13 Saboda haka, sa'adda Ruhu na gaskiya ya zo, zai bishe ku a cikin dukan gaskiyar, domin ba zai yi magana don kansa ba, sai dai duk abin da ya ji, shi zai fada, zai kuma sanar da ku al'amuran da zasu faru.
Men når han, Sandhedens Ånd, kommer, skal han vejlede eder til hele Sandheden; thi han skal ikke tale af sig selv, men hvad som helst han hører, skal han tale, og de kommende Ting skal han forkynde eder.
14 Zai daukaka ni, domin zai dauko abubuwa dake nawa ya sanar da ku.
Han skal herliggøre mig; thi han skal tage af mit og forkynde eder.
15 Duk abinda Uba yake da shi, nawa ne. Domin wannan ne nace zai dauko abubuwa da yake nawa ya sanar da ku.
Alt, hvad Faderen har, er mit; derfor sagde jeg, at han skal tage af mit og forkynde eder.
16 “Bayan dan lokaci kadan, ba zaku kara ganina kuma ba. bayan dan lokaci kadan kuma, zaku gan ni.”
Om en liden Stund skulle I ikke se mig længer, og atter om en liden Stund skulle I se mig."
17 Sai wadansu almajiransa sukace wa juna, “Me nene wannan da yake fadi mana, 'Bayan dan lokaci kadan ba zaku gan ni ba, bayan dan lokaci kadan kuma zaku gan ni?' da kuma, ' zan tafi wurin Uba'?”
Da sagde nogle af hans Disciple til hverandre: "Hvad er dette, som han siger os: Om en liden Stund skulle I ikke se mig, og atter om en liden Stund skulle I se mig, og: Jeg går hen til Faderen?"
18 Saboda haka sukace, “Me nene wannan da yake fada, 'Bayan dan lokaci kadan'? Bamu san abinda yake fada mana ba.”
De sagde altså: "Hvad er dette, han siger: Om en liden Stund? Vi forstå ikke, hvad han taler."
19 Yesu kuwa ya ga suna so su tambaye shi, sai ya ce masu, “Wato kuna tambayar juna ne abinda nake nufi da cewa, “Bayan dan lokaci kadan ba zaku gan ni ba, bayan dan lokaci kadan kuma zaku gan ni'?
Jesus vidste, at de vilde spørge ham, og han sagde til dem: "I spørge hverandre om dette, at jeg sagde: Om en liden Stund skulle I ikke se mig, og atter om en liden Stund skulle I se mig.
20 Hakika, hakika, ina gaya maku, zaku yi kuka da makoki, amma duniya za ta yi farin ciki, zaku cika da bakin ciki, amma bakin cikinku zai koma farin ciki.
Sandelig, sandelig, siger jeg eder, I skulle græde og jamre, men Verden skal glæde sig; I skulle være bedrøvede, men eders Bedrøvelse skal blive til Glæde.
21 Mace takan ji zafi lokacin da take nakuda don lokacin haihuwa ya zo. Amma da zarar ta haifi jinjirin nan, ba ta kara tunawa da zafin, domin ta na fariciki an haifi mutum a duniya.
Når Kvinden føder, har hun Bedrøvelse, fordi hendes Time er kommen; men når hun har født Barnet, kommer hun ikke mere sin Trængsel i Hu af Glæde over, at et Menneske er født til Verden.
22 To yanzu dai kuna bakin ciki, amma zan sake ganinku, kuma ba wanda zai iya kwace maku wannan farin ciki.
Også I have da vel nu Bedrøvelse, men jeg skal se eder igen, og eders Hjerte skal glædes, og ingen tager eders Glæde fra eder.
23 A rannan, ba zaku tambaye ni komai ba. Hakika hakika, ina gaya maku, komai kuka roki Uba a cikin sunana zai ba ku shi.
Og på den Dag skulle I ikke spørge mig om noget. Sandelig, sandelig, siger jeg eder, hvad som helst I bede Faderen om, skal han give eder i mit Navn.
24 Harwa yau, ba ku roki komai cikin sunana ba. Ku roka, zaku karba, domin farin cikin ku ya zama cikakke.”
Hidindtil have I ikke bedt om noget i mit Navn; beder, og I skulle få, for at eders Glæde må blive fuldkommen.
25 “Na fada maku wadannan abubuwa cikin karin magana. Amma sa'a tana zuwa da ba zan kara fada maku komai ba cikin karin magana, amaimakon haka zan gaya maku komai a sarari game da Uba.
Dette har jeg talt til eder i Lignelser; der kommer en Time, da jeg ikke mere skal tale til eder i Lignelser, men frit ud forkynde eder om Faderen.
26 A ranar nan, zaku yi roko a cikin sunana kuma bance maku zan yi addu'a ga Uba a madadinku ba,
På den Dag skulle I bede i mit Navn, og jeg siger ikke til eder, at jeg vil bede Faderen for eder;
27 domin Uba da kansa yana kaunarku, domin kun kaunace ni, kun kuma gaskata daga wurin Uban na fito.
thi Faderen selv elsker eder, fordi I have elsket mig og troet, at jeg er udgået fra Gud.
28 Daga wurin Uban na fito, kuma na shigo duniya. Har wa yau, kuma zan bar duniya in koma wurin Uba.”
Jeg udgik fra Faderen og er kommen til Verden; jeg forlader Verden igen og går til Faderen."
29 Almajiransa sukace, duba, “Yanzu kake magana a sarari, ba cikin karin magana ba!
Hans Disciple sige til ham: "Se, nu taler du frit ud og siger ingen Lignelse.
30 Yanzu mun sani ka san komai, ba sai wani ya tambaye ka ba. Ta haka muka gaskata daga wurin Allah ka fito.”
Nu vide vi, at du ved alle Ting og ikke har nødig, at nogen spørger dig; desårsag tro vi, at du er udgået fra Gud."
31 Yesu ya amsa masu yace, “Ashe, yanzu kun gaskata?
Jesus svarede dem: "Nu tro I!
32 Duba, sa'a na zuwa, I, sa'ar ta yi, da za a warwatsa ku, kowa ya koma gidansa, kuma ku bar ni ni kadai. Duk da haka kuwa ba ni kadai nake ba, domin Ubana yana tare da ni.
Se, den Time kommer, og den er kommen, da I skulle adspredes hver til sit og lade mig alene; dog, jeg er ikke alene, thi Faderen er med mig.
33 Na fada maku wannan ne domin a ciki na ku sami salama. A duniya kuna shan tsanani, amma ku karfafa: na yi nasara da duniya,”
Dette har jeg talt til eder, for at I skulle have Fred i mig. I Verden have I Trængsel; men værer frimodige, jeg har overvundet Verden."

< Yohanna 16 >