< Yohanna 14 >
1 “Kada zuciyarku ta bachi. Kun gaskata da Allah, sai kuma ku gaskata da ni.
2 A gidan Ubana akwai wurin zama dayawa. Da ba haka ba, da na fada maku, domin zan tafi in shirya maku wuri.
3 In kuwa na je na shirya maku wuri, zan dawo in karbe ku zuwa wurina domin inda nake kuma ku kasance.
4 Kun san hanya inda zan tafi.”
5 Toma ya ce wa Yesu, “Ubangiji, bamu san inda za ka tafi ba, yaya za mu san hanyar?”
6 Yesu ya ce masa, “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne rai; Ba mai zuwa wurin Uba sai ta wurina.
7 Da kun san ni, da kun san Ubana kuma. Amma daga yanzu kun san shi, kuma kun gan shi.”
8 Filibus ya ce wa Yesu, “Ubangiji, ka nuna mana Uban, wannan za ya ishe mu.”
9 Yesu ya ce masa, “Ina tare da ku da dadewa, amma har yanzu baka san ni ba, Filibus? Duk wanda ya gan ni, ya ga Uban. Yaya za ka ce, 'Nuna mana Uban'?
10 Baka gaskata cewa Ina cikin Uban, Uban kuma yana ciki na ba? Maganganun da nake fada maku, ba da ikona nake fadi ba, amma Uban ne da yake zaune a ciki na yake yin ayyukansa.
11 Ku gaskata ni cewa ina cikin Uban, Uban kuma na ciki na, ko kuwa ku bada gaskiya domin ayyukan kansu.
12 “Lalle hakika, ina gaya maku, duk wanda ya gaskata ni zai yi ayyukan da nake yi, kuma zai yi ayyuka fiye da wadannan, domin zan tafi wurin Uba.
13 Duk abinda kuka roka da sunana, zan yi shi domin a daukaka Uban cikin Dan.
14 Idan kuka roke ni komai cikin sunana, zan yi shi.
15 “Idan kuna kaunata, za ku kiyaye dokokina.
16 Sa, annan zan yi addu'a ga Uba, zai kuwa baku wani mai ta'aziya domin ya kasance tare daku har abada. (aiōn )
17 Ruhun gaskiya. Wanda duniya ba zata iya karba ba, domin bata gan shi ba, ko ta san shi. Amma ku kun san shi, domin yana tare da ku, zai kuma kasance a cikin ku.
18 Ba zan barku ku kadai ba; zan dawo wurin ku.
19 Sauran dan gajeren lokaci, duniya kuma ba zata ka ra gani na ba, amma ku kuna gani na. Saboda ina raye, kuma zaku rayu.
20 A wannan rana zaku sani ina cikin Ubana, ku kuma kuna ciki na, ni ma ina cikin ku.
21 Shi wanda yake da dokokina yake kuma bin su, shine ke kauna ta, kuma shi wanda ke kauna ta Ubana zai kaunace shi, Ni ma kuma zan kaunace shi in kuma bayyana kaina gare shi.”
22 Yahuza (ba Iskariyoti ba) ya ce ma Yesu, “Ubangiji, meyasa za ka bayyana kanka a gare mu, ba ga duniya ba?”
23 Yesu ya amsa ya ce masa,”Kowa yake kauna ta, zai kiyaye maganata. Ubana kuwa zai kaunace shi, za mu zo wurinsa mu zauna tare da shi.
24 Shi wanda baya kauna ta, ba ya kiyaye maganganuna. Maganar da kuke ji ba daga gareni take ba, amma daga Uba wanda ya aiko ni take.
25 Na fada maku wadannan abubuwa, sa'adda nake tare da ku.
26 Saidai, mai ta'aziyar- Ruhu Mai Tsarki wanda Uba zai aiko cikin sunana, zai koya maku kome, kuma zai tunashe ku dukan abinda na fada maku.
27 Na bar ku da salama; ina ba ku salamata. Ba kamar yadda duniya ke bayarwa Nake bayarwa ba. Kada zuciyarku ta baci, kuma kada ku tsorata.
28 Kun ji dai na fada maku, 'zan tafi, kuma Zan dawo gare ku'. Idan kuna kaunata, za ku yi farinciki domin za ni wurin Uban, gama Uban ya fi ni girma.
29 Yanzu na fada maku kafin ya faru, domin idan ya faru, ku gaskata.
30 Ba zan kara magana mai yawa da ku ba, domin mai mulkin duniyan nan yana zuwa. Bashi da iko a kai na,
31 amma domin duniya ta san cewa ina kaunar Uban, Ina yin daidai abinda Uban ya Umarce ni. Mu tashi mu tafi daga nan.