< Yohanna 13 >

1 Kamin bukin idin ketarewa, sa'adda Yesu ya san lokaci ya yi da zai tashi daga wannan duniya zuwa wurin Uba, da yake ya kaunaci nasa wadanda ke duniya- ya kaunace su har karshe.
Lyahanu pili Mukiti we Paseka niuseni kuliwa Jesu chabezi kuti inakoyakwe chiyasika yakuzwa hanuhansi ni kuya kwa Tayo - sina habakusuni bakwe bamuchisi - ababasaki kutwala kumamanisinzo.
2 Iblis ya rigaya ya sa a zuciyar Yahuza Iskariyoti dan Saminu, ya bashe da Yesu.
Lyahanu satani chababiketi kale mwinkulo ya Judasi Iskariota mwana a Simon, kuti abeteke Jesu.
3 Ya san cewa Uba ya bada kome a hannunsa, kuma ya zo daga wurin Allah, kuma zai koma wurin Allah.
Chabakwi kuti Tayo chabahele kale zintu zonso mumayanza akwe imi chabakazwile kwe Ireeza ni chabakubola kwe Ireeza.
4 Ya tashi daga cin abincin, ya tube tufafinsa, ya dauki tawul ya lullube kansa da shi.
Abazimani hamulalilo ni kuzwisa chizwanto chakwe chahewulu. Linu chahinda kataulo ni kukalisumina iye mwine.
5 Sa'an nan ya zuba ruwa a bangaji, ya fara wanke kafafun almajiran, yana shafe su da tawul din da ya lullube jikinsa da shi.
Linu chachunka mezi mukasuba ni kutanga kusaza matenda abarutwana bakwe ni kubapemula ni taulo yabalizingelete.
6 Ya zo wurin Bitrus Saminu, sai Bitrus ya ce masa,”Ubangiji, za ka wanke mani kafa?”
Chakeza kwa Simoni Pitirosi, imi Pitorosi chawamba kwali, “Simwine, mosaze matende angu na?”
7 Yesu ya amsa ya ce, “Abin da nake yi ba za ka fahimce shi yanzu ba, amma daga baya za ka fahimta.”
Jesu chetaba ni chati kwali, “Chinitenda kwanko kese uchizuwisise hanu, kono kokachizuwisise mwinako inza.”
8 Bitrus ya ce masa, “Ba za ka taba wanke mani kafa ba.” Yesu ya amsa masa ya ce, “In ban wanke maka ba, ba ka da rabo da ni”. (aiōn g165)
Pitorosi chawamba kwali, “Kense usanze matende angu.” Jesu chamwitaba, “Heba kanikusazi, kawina chemba kwangu.” (aiōn g165)
9 Bitrus ya ce masa, “Ubangiji, ba kafafuna kadai za ka wanke ba, amma da hannayena da kaina.”
Simoni Pitirosi chawamba kwali, “Simwine, kanzi unisazi bulyo kumatende, kono nikumayanza angu ni mutwi wangu.”
10 Yesu ya ce masa, “Duk wanda ya yi wanka ba ya da bukata, sai dai a wanke kafafunsa, amma shi tsarkakakke ne baidaya; ku tsarkakakku ne, amma ba dukanku ba.”
Jesu chawamba kwali, “Uzo yosazwa kena chasaka, hensi kusazwa kumatende, kono ujolwele neza; ujololwe, kono isini umwi ni umwi.”
11 (Don Yesu ya san wanda zai bashe shi, shiyasa ya ce, “Ba dukanku ne ke da tsarki ba.”)
(Mukuti Jesu abezi yese namubeteke; chinji abawambi, “Kahena kutimubonse mujolola.)”
12 Bayan Yesu ya wanke masu kafafu, ya dauki tufafinsa ya zauna kuma, ya ce masu, “Kun san abin da na yi muku?
Linu Jesu hamana kubasaza matende abo ni kuhinda zizwato zakwe ni kwikala hansi hape, chawamba kubali, “Kana mwizi chinatenda kwenu?
13 kuna kirana, 'Malam, da Ubangiji,' kun fadi daidai, don haka Nake.
Munisupa 'Muluti' ni 'Simwine,' imi uwamba chishiyeme, kakuti linu njime.
14 Idan ni Ubangiji da kuma mallam, na wanke maku kafafu, ya kamata kuma ku wanke wa junan ku kafafu.
Heba njime linu, Simwine ni Muluti, nashanza matende enu, nemwe mulishanze matende enu zumwi ni zumwi.
15 Gama na baku misali, saboda ku yi yadda na yi maku.
Mukuti chinamiha mutala kokuti nenwe mutende bobulyo munamitendela.
16 Lalle hakika ina gaya muku, bawa ba ya fi mai gidansa girma ba; dan aike kuma ba ya fi wanda ya aiko shi girma ba.
Ikumbya line, niwamba kwenu, mubeleki kena mukando kwafumwe; kapa mutumiwa kubamukando kuwamutuma.
17 Idan kun san wadannan abubuwa, ku masu albarka ne idan kun aikata su.
Heba nimwiziba izizintu, mufuyoletwe heba nimuzitenda.
18 Ba ina magana akan dukanku ba; Na san wadanda na zaba. Amma domin Nassi ya cika: 'Shi Wanda ya ci gurasata, ya tayar mani'.
Kaniwambi mubonse; niziabo banibaketi — kono iñolo linani kwizuzilizwa; 'Iye ulya chikwa changu unilaha mulezele.'
19 Ina fada maku wannan yanzu tun kafin haka ta faru domin sa'adda ta faru, ku gaskata Ni ne.
Nimiwambila inzohahanu pili niziseni kutendahala, linukuti hazitendahala, nimuzumine kuti Njime.
20 Hakika, hakika, Ina gaya maku, wanda ya karbi wanda na aiko, Ni ya karba, wanda kuma ya karbe ni, ya karbi wanda ya aiko ni.
Ikumbya line, nimiwambila, yotambula yese unatuma, watambulame, imi yotambula ime, utambula iye yabanitumi.”
21 Bayan Yesu ya fadi haka, ya damu a ruhu, ya yi shaida ya ce, “Lalle hakika, ina gaya muku cewa daya daga cikinku zai bashe ni.”
Linu Jesu hawamba inzo, chabakatazehete muluhuho, chaha bupaki mi chati, “Ikumbya line, niwamba kwenu kuti zumwi kwenu kanibeteke.”
22 Almajiran suka kalli juna, suna juyayin ko akan wa yake magana.
Barutwana chibalilola, nibabilelete kuti uwambani.
23 Daya daga cikin almajiransa, wanda Yesu yake kauna, yana a teburi, jingine a kirjin Yesu.
Zumwi wabarutwana, wabakusaka hahulu Jesu, abakushendeme hetafule nazendamine hachizuba cha Jesu.
24 Siman Bitrus ya ce wa almajirin, “ka fada mana ko akan wa ya ke magana.”
Simoni Pitorosi chalolela konzo murutwana ni kuwamba, “Tuwambile njeni unzo yowamba zakwe.”
25 Sai ya sake jingina a kirjin Yesu, ya ce masa, “Ubangiji, wanene?”
Linu chazendamina hachizuba cha Jesu ni kuwamba kwali, “Simwine, njeni unzo?”
26 Sannan Yesu ya amsa, “Shine wanda zan tsoma gutsuren gurasa in ba shi.” Sannan bayan ya tsoma gurasar, sai ya ba Yahuza Dan Siman Iskariyoti.
Linu Jesu chamwitaba, “Njiyena yesenihe chikwa chinansunsa.” Chobulyo hamana kunsunsa chikwa, chachiha Judasi mwana Simon Iskariota.
27 To bayan gurasar, sai shaidan ya shige shi, sai Yesu ya ce masa, “Abinda kake yi, ka yi shi da sauri.”
Imi linu, hakumana chikwa, Satani chamwinjila, linu Jesu chawamba kwali, “Chosakaku tenda, uchitende kakuhwela.”
28 Babu wani a teburin da ya san dalilin dayasa ya fada masa wannan.
Kakwina nanga umwina kubabalikwikele naye hetafule yabezi kuti chizi hawamba inzo kwali.
29 Wadansu sun yi tsamanin cewa, tun da Yahuza ne ke rike da jakkar kudi, Yesu ya ce masa, “Ka sayi abinda muke bukata don idin”, ko kuma ya bada wani abu domin gajiyayyu.
Bamwi chiba hupula kuti, mukuti Judasi ibali iye yabakubika masheleni, chingi Jesu abawambi kwali, “Ukawule zisakahala kuti tube nanzo hamukiti,” kapa uwola kukaha zimwi kubanjebwe.
30 Bayan Yahuza ya karbi gurasar, sai ya fita nan da nan. Da daddare ne kuwa.
Judasi hamana kutambula chikwa, chazwila hanze hahobulyo. Chi ibali masiku.
31 Bayan Yahuza ya tafi, Yesu ya ce, “Yanzu an daukaka Dan mutum, kuma an daukaka Allah a cikinsa.
Inako Judasi hayenda hanze, Jesu chati, “Hanu Mwana wa Muntu cholumbekwa, imi Ireeza kalumbekwe chebakalyakwe.
32 Allah zai daukaka shi a cikin kansa, kuma zai daukaka shi nan da nan.
Ireeza kamulumbeke iye kalwake mwine, imi kamulumbeke hahanubulyo.
33 'Ya'ya kanana, ina tare da ku na wani gajeren lokaci. Zaku neme ni, kuma kamar yadda na fadawa Yahudawa, 'in da zan tafi ba za ku iya zuwa ba.' Yanzu kuma na fada maku wannan.
Bahwile banini, nichina nanwe mukuti kuchina kanakozana bulyo. Kamuningane, imi sinamuni bawambili majuda, 'Kuniya kamuwoli kwizako.' Nahanu nichi wamba inzi kwenu hape.
34 Ina baku sabuwar doka, ku kaunaci juna; kamar yadda na kaunace ku, haka kuma ku kaunaci juna.
Nimiha mulao muhya, kuti musake umwi ni umwi; sina munibakumisakila, linu musake umwi ni umwi hape.
35 Ta haka kowa zai san ku almajiraina ne, idan kuna kaunar juna.”
Chenzi umwi ni umwi kezibe kuti mubarutwana bangu, heba ni mulisuni zumwi ku zumwi.
36 Siman Bitrus ya ce masa, “Ubangiji, ina za ka?” Yesu ya amsa ya ce, “Inda za ni, ba zaka iya bi na ba yanzu, amma zaka bini daga baya.”
Simoni Pitorosi chawamba kwali, “Simwine, ukaya kuhi?” Jesu abamwitaba, “Kuniya, kowoli kunichilila hanu, kono konichilele inako yiza.”
37 Bitrus ya ce masa, “Ubangiji, don me ba zan iya binka a yanzu ba? Zan bada raina domin ka.”
Pitorosi chati kwali, “Simwine, chinzi hanisawoli kukwichilila? Kanilifungule buhalo bwangu bakeñi chanko.”
38 Yesu ya amsa ya ce, “Za ka bada ranka domina? Lalle hakika, ina gaya maka, kafin zakara ya yi cara zaka yi musu na sau uku.”
Jesu chetaba, “Uwola kulifungula buhalo bwanko ibaka lyangu? Ikumbya line, Nikuwambila, munkombwe niuseni kulila kobe chonisampwile totatwe.”

< Yohanna 13 >