< Yohanna 10 >

1 “Hakika, Hakika, ina ce maku, wanda bai shiga ta kofa zuwa garken tumaki ba, amma ya haura ta wata hanya, wannan mutum barawo ne da dan fashi.
" Sandelig, sandelig, siger jeg eder, den, som ikke går ind i Fårefolden gennem Døren, men stiger andensteds over, han er en Tyv og en Røver.
2 Wanda ya shiga ta kofa shine makiyayin tumakin.
Men den, som går ind igennem Døren, er Fårenes Hyrde.
3 Mai gadin kofar zai bude masa. Tumakin suna jin muryarsa, ya na kuma kiran tumakinsa da sunayensu, ya kuma kai su waje.
For ham lukker Dørvogteren op, og Fårene høre hans Røst; og han kalder sine egne Får ved Navn og fører dem ud.
4 Bayanda ya kawo su duka a waje, yana tafiya a gabansu, sai tumakin su bi shi, domin sun san muryarsa.
Og når han har ført alle sine egne Får ud, går han foran dem; og Fårene følge ham, fordi de kende hans Røst.
5 Ba za su bi bako ba amma sai dai su guje shi, domin basu san muryar baki ba.”
Men en fremmed ville de ikke følge, men de ville fly fra ham, fordi de ikke kende de fremmedes Røst."
6 Yesu ya yi masu magana da wannan misali, amma basu gane wadannan abubuwa da yake gaya masu ba.
Denne Lignelse sagde Jesus til dem; men de forstode ikke, hvad det var, som han talte til dem.
7 Sai Yesu ya ce masu kuma, “Hakika, Hakika, Ina ce maku, Ni ne kofar tumaki.
Jesus sagde da atter til dem: "Sandelig, sandelig, siger jeg eder, jeg er Fårenes Dør.
8 Dukan wadanda suka zo kamin ni barayi ne da yan fashi, amma tumakin ba su ji su ba.
Alle de, som ere komne før mig, ere Tyve og Røvere; men Fårene hørte dem ikke.
9 Ni ne kofa, In kowa ya shiga ta wurina, zai sami ceto, zai shiga ya fita ya kuma sami wurin kiwo.
Jeg er Døren; dersom nogen går ind igennem mig, han skal frelses; og han skal gå ind og gå ud og finde Føde.
10 Barawo ba ya zuwa sai don ya yi sata, ya kashe, ya kuma hallakar. Na zo ne domin su sami rai su kuma same shi a yalwace.
Tyven kommer ikke uden for at stjæle og slagte og ødelægge; jeg er kommen, for at de skulle have Liv og have Overflod.
11 Ni ne makiyayi mai kyau. Makiyayi mai kyau yana bada ransa domin tumakinsa.
Jeg er den gode Hyrde; den gode Hyrde sætter sit Liv til for Fårene.
12 Wanda yake dan sako kuma, ba makiyayi ba, wanda ba shine mai tumakin ba, in ya ga kyarkeci na zuwa sai ya saki tumakin ya gudu. Sai kyarkecin ya dauke su ya kuma warwatsa su.
Men Lejesvenden, som ikke er Hyrde, hvem Fårene ikke høre til ser Ulven komme og forlader Fårene og flyr, og Ulven røver dem og adspreder dem,
13 Ya gudu domin shi mai aikin kudi ne kuma bai damu da tumakin ba.
fordi han er en Lejesvend og ikke bryder sig om Fårene.
14 Nine makiyayi mai kyau, na kuma san nawa, nawa kuma sun san ni.
Jeg er den gode Hyrde, og jeg kender mine, og mine kende mig,
15 Uban ya san ni, ni ma na san Uban, na kuma bada raina domin tumakin.
ligesom Faderen kender mig, og jeg kender Faderen; og jeg sætter mit Liv til for Fårene.
16 Ina da wadansu tumaki wadanda ba na wannan garken ba. Wadannan, kuma, dole in kawo su, su ma za su ji muryata saboda za su zama garke daya da makiyayi daya.
Og jeg har andre Får, som ikke høre til denne Fold; også dem bør jeg føre, og de skulle høre min Røst; og der skal blive een Hjord, een Hyrde.
17 Domin wannan ne Uban yake kauna ta: Na bada raina domin in same shi kuma.
Derfor elsker Faderen mig, fordi jeg sætter mit Liv til for at tage det igen.
18 Babu wanda zai dauke shi daga wurina, amma ina bayar da shi da kaina. Ina da ikon bada shi, ina da iko in dauke shi kuma. Na karbi wannan umarnin daga wurin Ubana.”
Ingen tager det fra mig, men jeg sætter det til af mig selv. Jeg har Magt til at sætte det til, og jeg har Magt til at tage det igen. Dette Bud modtog jeg af min Fader."
19 Tsattsaguwa ta sake tashi tsakanin Yahudawa domin wadannan kalmomin.
Der blev atter Splid iblandt Jøderne for disse Ords Skyld.
20 Dayawa a cikinsu suka ce, yana da aljani, kuma mahaukaci ne. Don me ku ke sauraronsa?”
Og mange af dem sagde: "Han er besat og raser, hvorfor høre I ham?"
21 Wadansu suka ce, wadannan ba kalmomin wanda yake da aljani ba ne. Ko mai aljani zai iya bude idanun makaho?”
Andre sagde: "Dette er ikke Ord af en besat; mon en ond Ånd kan åbne blindes Øjne?"
22 Sai lokacin idin Tsarkakewa a Urushalima ya zo.
Men Tempelvielsens Fest indtraf i Jerusalem. Det var Vinter;
23 A lokacin damuna ne, Yesu kuwa yana tafiya a shirayi cikin haikalin Sulaimanu.
og Jesus gik omkring i Helligdommen, i Salomons Søjlegang.
24 Sai Yahudawa suka zagaye shi suka ce masa, “Har yaushe ne za ka bar mu cikin shakka? In kai ne Almasihun, ka gaya mana dalla-dalla.”
Da omringede Jøderne ham og sagde til ham: "Hvor længe holder du vor Sjæl i Uvished? Dersom du er Kristus, da sig os det rent ud!"
25 Yesu ya ce masu, “Na gaya maku, amma baku gaskata ba. Ayyukan da nake yi a cikin sunan Ubana, su ke yin shaida a kaina.
Jesus svarede dem: "Jeg har sagt eder det, og I tro ikke. De Gerninger, som jeg gør i min Faders Navn, de vidne om mig;
26 Duk da haka baku gaskata ba domin ku ba tumakina ba ne.
men I tro ikke, fordi I ikke ere af mine Får.
27 Tumakina suna jin murya ta; Na san su, suna kuma bi na.
Mine Får høre min Røst, og jeg kender dem, og de følge mig,
28 Ina ba su rai na har abada; ba za su taba mutuwa ba, babu wanda zai kwace su daga hannu na. (aiōn g165, aiōnios g166)
og jeg giver dem et evigt Liv, og de skulle i al Evighed ikke fortabes, og ingen skal rive dem ud af min Hånd. (aiōn g165, aiōnios g166)
29 Ubana, wanda ya bani su, ya fi kowa girma, kuma ba mai iya kwace su daga hannun Uban.
Min Fader, som har givet mig dem, er større end alle; og ingen kan rive noget af min Faders Hånd.
30 Ni da Uban daya ne.”
Jeg og Faderen, vi ere eet."
31 Sai Yahudawa suka dauki duwatsu kuma domin su jajjefe shi.
Da toge Jøderne atter Sten op for at stene ham.
32 Yesu ya amsa masu, “Na nuna maku kyawawan ayyuka masu yawa daga wurin Uban. Saboda wane daga cikin wadannan ayyukan kuke jefe ni?”
Jesus svarede dem: "Mange gode Gerninger har jeg vist eder fra min Fader; for hvilken af disse Gerninger stene I mig?"
33 Sai Yahudawa suka amsa masa, “ba don wani aiki mai kyau muke son mu jefe ka ba, amma don sabo, domin kai, mutum ne, amma kana mayar da kanka Allah.”
Jøderne svarede ham: "For en god Gerning stene vi dig ikke, men for Gudsbespottelse, og fordi du, som er et Menneske, gør dig selv til Gud."
34 Yesu ya amsa masu, “Ba a rubuce yake a shari'arku ba, 'Na ce, “ku alloli ne”'?”
Jesus svarede dem: "Er der ikke skrevet i eders Lov: Jeg har sagt: I ere Guder?
35 In ya kira su alloli, su wadanda maganar Allah ta zo gare su (kuma ba za a iya karya nassi ba),
Når den nu har kaldt dem Guder, til hvem Guds Ord kom (og Skriften kan ikke rokkes),
36 kuna gaya wa wanda Uban ya kebe ya kuma aiko cikin duniya, 'Kana sabo', domin Na ce, 'Ni dan Allah ne'?
sige I da til den, hvem Faderen har Helliget og sendt til Verden: Du taler bespotteligt, fordi jeg sagde: Jeg er Guds Søn?
37 In ba na aikin Ubana, kada ku gaskata ni.
Dersom jeg ikke gør min Faders Gerninger, så tror mig ikke!
38 Amma, idan ina yin su, ko ba ku gaskata da ni ba, ku gaskata da ayyukan saboda ku sani, ku kuma gane cewa Uban yana ciki na, ni kuma ina cikin Uban.”
Men dersom jeg gør dem, så tror Gerningerne, om I end ikke ville tro mig, for at I kunne indse og erkende, at Faderen er i mig, og jeg i Faderen."
39 Suka sake kokarin kama shi, amma ya yi tafiyarsa, ya fita daga hannunsu.
De søgte da atter at gribe ham; og han undslap af deres Hånd.
40 Ya yi tafiyarsa kuma har gaba da kogin Urdun zuwa inda Yahaya ke yin baftisma ada, ya kuma zauna a wurin.
Og han drog atter bort hinsides Jordan til det Sted, hvor Johannes først døbte, og han blev der.
41 Mutane masu yawa suka zo wurinsa, suka ce,”Hakika Yahaya bai yi wasu alamu ba, amma dukan abubuwan da Yahaya ya ce game da wannan mutum gaskiya ne.”
Og mange kom til ham, og de sagde: "Johannes gjorde vel intet Tegn; men alt, hvad Johannes sagde om denne, var sandt."
42 Mutane dayawa suka bada gaskiya gare shi a wurin.
Og mange troede på ham der.

< Yohanna 10 >