< Yaƙub 1 >

1 Yakubu, bawan Allah, da kuma Ubangiji Yesu Almasihu, zuwa ga kabilun nan goma sha biyu da suke warwatse: ina gaishe ku.
Jakob, Guds og den Herre Jesu Kristi tjener, hilser de tolv stammer som er spredt omkring i landene.
2 Ku dauke su duka da farin ciki, 'yan'uwana, duk sa'adda kuke fuskantar jarabobi.
Akt det for bare glede, mine brødre, når I kommer i allehånde fristelser,
3 Ku sani cewa gwajin banskiyar ku ta kan haifi jimiri.
da I vet at prøvelsen av eders tro virker tålmodighet;
4 Bari jimiri ya cika aikin sa, domin ku kai ga cikakken girma kuma ku kammalu, domin kada ku rasa komai.
men tålmodigheten må føre til fullkommen gjerning, forat I kan være fullkomne og hele og ikke mangle noget.
5 Amma idan waninku yana bukatar hikima, sai ya roki Allah, wanda yake bayarwa a yalwace, ba tare da gori ba ga duk wanda ya roke shi, zai kuwa ba shi.
Men dersom nogen av eder mangler visdom, da bede han Gud, han som gir alle villig og uten onde ord, og den skal gis ham.
6 Amma fa sai ya roka da banskiya ba tare da shakka ba, don mai shakka kamar rakumin ruwan teku yake, wanda iska take korarwa tana tunkudawa.
Men han bede i tro, uten å tvile; for den som tviler, ligner havsbølgen, som drives og kastes av vinden.
7 Tilas ne wannan mutum kada ya yi tunanin zai karbi wani abu a wurin Ubangiji.
For ikke må det menneske tro at han skal få noget av Herren,
8 Irin wannan mutumin mai zuciya biyu ne, mara tsai da hankali a dukan hanyoyin sa.
slik en tvesinnet mann, ustø på alle sine veier.
9 Bari dan'uwa matalauci ya yi takama da matsayin sa babba,
Men den ringe bror rose sig av sin høihet,
10 amma mutum mai arziki kuma a kaskantaccen matsayin sa, gama zai shude kamar furen ciyawa na jeji.
og den rike av sin ringhet; for han skal forgå som blomst på gress;
11 Domin rana na bullowa da zafi mai konarwa kuma ya busar da ciyawa. Furen ya fadi, kuma kyaun sa ya lalace. Haka ma, mai arziki zai bushe yana cikin tsakiyar tafiyarsa.
solen gikk op med sin brand og tørket gresset bort, og blomsten på det falt av, og dets fagre skikkelse blev ødelagt; således skal og den rike visne bort på sine veier.
12 Albarka ta tabbata ga mutum mai jurewa da gwaji. Domin in ya jure gwajin, zai sami rawanin rai, wanda aka yi alkawarin sa ga wadanda ke kaunar Allah.
Salig er den mann som holder ut i fristelse; for når han har stått sin prøve, skal han få livsens krone, som Gud har lovt dem som elsker ham.
13 Kada wani ya ce idan aka gwada shi, ''Wannan gwaji daga wurin Allah ne,'' domin ba a gwada Allah da mugunta, shi kan sa kuwa ba ya gwada kowa.
Ingen si når han fristes: Jeg fristes av Gud. For Gud fristes ikke av det onde, og selv frister han ingen.
14 Amma kowanne mutum yakan sami gwaji daga muguwar sha'awar sa, wadda take janye shi kuma ta rinjaye shi.
Men hver fristes idet han drages og lokkes av sin egen lyst;
15 Bayan da muguwar sha'awar ta dauki ciki, sai ta haifi zunubi. Kuma bayan da zunubi ya yi girma, yakan haifi mutuwa.
derefter, når lysten har undfanget, føder den synd; men når synden er blitt fullmoden, føder den død.
16 Kada fa ku yaudaru, 'yan'uwana kaunatattu.
Far ikke vill, mine elskede brødre!
17 Kowace kyakkyawar baiwa, da kowace cikakkiyar baiwa daga sama take. Ta sauko ne daga wurin Uban haskoki. Wanda babu sauyawa ko wata alamar sakewa kamar yadda inuwa ke yi.
All god gave og all fullkommen gave kommer ovenfra, fra lysenes Fader, hos hvem det ikke er forandring eller skiftende skygge.
18 Allah ya zabi ya haife mu ta wurin maganar gaskiya, domin mu zama kamar nunar fari na dukan halittar sa.
Efter sin vilje har han født oss ved sannhets ord, forat vi skal være en førstegrøde av hans skapninger.
19 Kun san wannan, 'yan'uwana kaunatattu: bari kowanne mutum ya yi hanzarin kasa kunne, da jinkirin yin magana, da kuma jinkirin yin fushi.
I vet det jo, mine elskede brødre! Men hvert menneske være snar til å høre, sen til å tale, sen til vrede;
20 Domin fushin mutum ba ya aikata adalcin Allah.
for manns vrede virker ikke det som er rett for Gud.
21 Saboda haka, sai ku yar da kowanne irin aikin kazanta da yalwar mugunta. A cikin tawali'u ku karbi dassashiyar maganar, wadda ke iya ceton rayukan ku.
Avlegg derfor all urenhet og all levning av ondskap, og ta med saktmodighet imot det ord som er innplantet i eder, og som er mektig til å frelse eders sjeler!
22 Ku zama masu aikata maganar, kada ku zama masu jin ta kawai, kuna yaudarar kanku.
Men vær ordets gjørere, og ikke bare dets hørere, idet I dårer eder selv.
23 Domin duk wanda ya ke mai jin maganar ne kawai, ba mai aikatawa ba, kamar mutum yake mai duba fuskarsa a madubi.
For dersom en er ordets hører og ikke dets gjører, da ligner han en mann som ser på sitt naturlige åsyn i et speil:
24 Yakan dubi kansa sai ya tafi, nan da nan kuwa sai ya manta da kamannin sa.
han så på sig selv og gikk bort, og glemte straks hvordan han så ut.
25 Amma duk mai duba shari'ar da bin ka'idar nan ta 'yanci, ya kuma nace biyayya da ita, ba zai zama kamar wanda zai ji ya manta ba, wannan mutum zai zama da albarka a cikin abin da yake yi.
Men den som skuer inn i frihetens fullkomne lov og holder ved med det, så han ikke blir en glemsom hører, men gjerningens gjører, han skal være salig i sin gjerning.
26 Idan wani yana zaton shi mai addini ne, amma bai kame bakinsa ba, yana yaudarar zuciyarsa ne, addinin mutumin nan na banza ne.
Dersom en mener at han er en gudsdyrker, og ikke holder sin tunge i tømme, men dårer sitt eget hjerte, hans gudsdyrkelse er forgjeves.
27 Addini sahihi kuma marar aibi a gaban Allahnmu da Ubanmu, shine a kula da gwauraye da marayu a cikin kuntatar su, kuma mutum ya kebe kansa ya zama marar aibi daga duniya.
En ren og usmittet gudsdyrkelse for Gud og Faderen er dette: å se til farløse og enker i deres trengsel, å holde sig selv uplettet av verden.

< Yaƙub 1 >