< Yaƙub 5 >
1 Ku zo yanzu, ku da kuke masu arziki, ku yi ta kuka da kururuwa domin bakin ciki iri-iri da ke zuwa gare ku.
2 Arzikin ku ya rube, tufafinku kuma duk cin asu ne.
3 Zinariya da azurfarku sun yi tsatsa. Tsatsar su kuwa zai zama shaida a kanku. Zai cinye naman ku kamar wuta. Kun yi ajiyar dukiyarku domin ranakun karshe.
4 Duba, hakin ma'aikata yana kuka - hakin da kuka hana wa wadanda suka girbe maku gonaki. Kuma kukan masu girbin ya tafi ya kai ga kunnuwan Ubangiji mai Runduna.
5 Kun yi zama cikin annashuwa a duniya kuma kun tsunduma kanku. Kun sa zukatan ku sun yi kiba domin ranar yanka.
6 Kun hukunta kuma kun kashe adalin mutum. Bai kuwa yi tsayayya da ku ba.
7 Saboda haka ku yi hakuri, 'yan'uwa, har sai zuwan Ubangiji. Duba, yadda manomi ya kan jira kaka mai amfani daga gona. Da hakuri yake jiran ta har sai ta karbi ruwa na fari da na karshe.
8 Ku, ma, ku yi hakuri. Ku karfafa zukatan ku, domin zuwan Ubangiji ya yi kusa.
9 Kada ku yi gunaguni, 'Yan'uwana, game da juna, don kada a hukunta ku. Duba, mai shari'a na tsaye a bakin kofa.
10 Dauki misali, 'yan'uwa, daga shan wuya da hakurin annabawa, wadanda suka yi magana a cikin sunan Ubangiji.
11 Duba, mukan kira wadanda suka jimre masu albarka. Kun dai ji irin jimiri da Ayuba ya yi, kun kuma san nufin Ubangiji, yadda yake mai yawan tausayi da jinkai.
12 Fiye da komai duka, 'yan'uwana, kada ku yi rantsuwa, ko da sama, ko da kasa, ko da kowace irin rantsuwa ma. A maimakon haka bari “I” ya zama “I”, in kuwa kun ce “A'a”, ya zama “A'a”, don kada ku fada a cikin hukunci.
13 Akwai wanda ke fama a tsakanin ku? Sai ya yi addu'a, akwai wanda yake murna? Sai ya raira wakar yabo.
14 Akwai mara lafiya a tsakanin ku? Sai ya kira dattawan ikilisiya, sai su yi masa addu'a. Suna shafa masa mai a cikin sunan Ubangiji.
15 Addu'ar bangaskiya zai warkar da mara lafiyan, Ubangiji zai tashe shi. Idan ma ya yi zunubi, Allah zai gafarta masa.
16 Soboda haka, ku furta zunuban ku ga juna, kuna yi wa juna addu'a, don a warkar da ku. Addu'ar mai adalci tana da karfin aiki kwarai da gaske.
17 Iliya dan Adam ne kamar mu. Amma da ya nace da addu'a kada a yi ruwa, ba kuma yi ruwa a kasar ba har shekara uku da wata shida.
18 Sai Iliya ya sake yin addu'a. Sammai suka ba da ruwa, kasa kuma ta ba da amfanin ta.
19 Ya ku 'yan'uwana, idan wanin ku ya baude wa gaskiya, wani kuma ya dawo da shi,
20 wannan mutum ya sani cewa, duk wanda ya dawo da mai zunubi a hanya daga baudewar sa, zai cece shi daga mutuwa, kuma zai rufe dunbin zunubai.