< Yaƙub 4 >
1 Me ke kawo gaba da rashin jituwa a tsakanin ku? Ba yana tasowa ne daga muguwar sha'awa da ke yaki a cikin ku ba?
2 Kuna sha'awa, kuma ba ku da shi. Kuna kisa da kyashi, kuma ba za ku iya samu ba. Kuna danbe da fada. Har wa yau baku samu ba domin baku tambaya ba.
3 Kun roka kuma ba a baku ba saboda kuna roko ta hanya mara kyau, kuna so ku yi amfani da shi domin miyagun sha'awoyin ku.
4 Ku mazinata! Baku sani ba, abokantaka da duniya, tawaye ne ga Allah? Don haka duk wanda ya shiga abokantaka da duniya ya zama magabcin Allah.
5 Ko kuna zaton nassi ya fadi haka a banza ne, “Ruhun nan da ke a cikinmu yana da kishi matuka?”
6 Amma Allah ya bayar da karin alheri, shi ya sa nassi ya ce, “Allah yana gaba da mai girman kai, Amma yana ba da alheri ga mai tawaliu.”
7 Saboda haka ku mika kan ku ga Allah. Ku yi tsayayya da shaidan, zai kuma guje maku.
8 Ku matso kusa da Allah, shi kuma za ya matsa kusa da ku. Wanke hannayen ku, ku masu zunubi, ku tsabtace zukatan ku, ku masu zuciya biyu.
9 Ku yi bakin ciki, makoki, da kuka! Ku mayar da dariyar ku ta koma bakin ciki, farin cikinku kuma zuwa ga bakin ciki.
10 Ku kaskantar da kanku a gaban Ubangiji, shi kuma za ya daukaka ku.
11 Kada ku rika zargin juna, 'yan'uwa. Wanda ya ke zargin dan'uwa ko shari'anta dan'uwansa, yana zargin shari'a kuma yana hukunta shari'a. Idan ka hukunta shari'a, ya nuna ba ka biyayya da shari'ar, amma mai hukunci.
12 Mai ba da shari'a da yin hukunci daya ne. Shine mai iya ceto kuma ya hallakar. Kai wanene, da ke hukunta makwafcin ka?
13 Saurara, ku da kuke cewa, “Yau ko gobe za mu tafi wancan birnin mu yi shekara guda a wurin, muna kasuwanci, mu kuma yi riba.”
14 Wa ya san abin da zai faru gobe, kuma yaya rayuwan ka zai kasance? Kai kamar hazo ne mai bayyana bayan dan lokaci kadan ya bace.
15 Maimakon haka, sai ka ce, “Idan Ubangiji ya nufa, za mu rayu kuma mu yi wannan ko wancan.”
16 Amma yanzu kana fahariya da shirye shiryen ka na takama. Irin wannan fahariya, mugunta ce.
17 Saboda haka ga wanda ya san abin da ya kamata ya aikata amma bai yi ba, ya zama zunubi a gare shi.