< Yaƙub 3 >
1 Ba mutane dayawa za su zama masu koyarwa ba, 'yan'uwana. Mun san cewa za mu karbi hukunci mafi tsanani.
nolite plures magistri fieri fratres mei scientes quoniam maius iudicium sumitis
2 Domin mukan yi tuntube ta hanyoyi dayawa. Duk wanda bai yi tuntube ta hanyar kalmomi ba, shi mutum ne ginanne sosai, wanda ke iya kame dukan jikinsa.
in multis enim offendimus omnes si quis in verbo non offendit hic perfectus est vir potens etiam freno circumducere totum corpus
3 Idan muka sa linzami a bakunan dawakai, domin su yi mana biyayya, za mu iya sarrafa jikunan su gaba daya.
si autem equorum frenos in ora mittimus ad consentiendum nobis et omne corpus illorum circumferimus
4 Ku lura kuma da jiragen ruwa, ko da yake suna da girma sosai kuma iska mai karfi tana kora su, da karamin karfe ne matukin yake juya su inda ya so.
ecce et naves cum magnae sint et a ventis validis minentur circumferuntur a modico gubernaculo ubi impetus dirigentis voluerit
5 Haka kuma harshe dan karamin gaba ne a jiki, sai fahariyan manyan abubuwa. Ku lura yadda dan karamin wuta yake cinna wa babban jeji wuta.
ita et lingua modicum quidem membrum est et magna exultat ecce quantus ignis quam magnam silvam incendit
6 Harshe ma wuta ne, a cikin dukan gabobin mu, duniyar zunubai da aka sa cikin fannonin jikunan mu. Yana gurbata dukan jiki, ya kuma sa al'amurar rayuwa su kama da wuta. Shi kuwa gidan wuta ne yake zuga shi. (Geenna )
et lingua ignis est universitas iniquitatis lingua constituitur in membris nostris quae maculat totum corpus et inflammat rotam nativitatis nostrae inflammata a gehenna (Geenna )
7 Domin kowace irin dabbar jeji, tsunsu, da masu jan ciki, da hallittar teku, ana sarrafa su kuma dan Adam har ya sarrafa su ma.
omnis enim natura bestiarum et volucrum et serpentium etiam ceterorum domantur et domita sunt a natura humana
8 Amma game da harshe, babu wani a cikin 'yan Adam da ya iya sarrafa shi. Mugunta ne mara hanuwa, cike da dafi mai kisa.
linguam autem nullus hominum domare potest inquietum malum plena veneno mortifero
9 Da wannan harshe muke yabon Ubangiji da kuma Uba, da shi kuma muke la'antar mutane wandanda aka hallitta cikin kamanin Allah.
in ipsa benedicimus Dominum et Patrem et in ipsa maledicimus homines qui ad similitudinem Dei facti sunt
10 Bakin da ake sa albarka, da shi kuma ake la'antarwa. 'Yan'uwana, ai, wannan bai kamata ba.
ex ipso ore procedit benedictio et maledictio non oportet fratres mei haec ita fieri
11 Mabulbulan ruwa ba zai iya bubbugowa da ruwan dadi da na zartsi tare ba, ko zai iya?
numquid fons de eodem foramine emanat dulcem et amaram aquam
12 ''Yan'uwana, itacen baure ba zai iya yin zaitun ba, zai iya? Ko kuwa gonar inabi ya yi baure? Haka kuma, ruwan zartsi ba zai iya bayar da ruwan dadi ba.
numquid potest fratres mei ficus olivas facere aut vitis ficus sic neque salsa dulcem potest facere aquam
13 Ina mai hikima da fahimta a cikin ku? Bari wannan mutumin, ta kyakkyawan zaman sa ya nuna aikin da halin tawali'u da hikima ke sawa.
quis sapiens et disciplinatus inter vos ostendat ex bona conversatione operationem suam in mansuetudine sapientiae
14 Amma in kuna da matsanancin kishi da kazamin buri a cikin zuciyar ku, kada ku yi fahariya da karya game da gaskiya.
quod si zelum amarum habetis et contentiones in cordibus vestris nolite gloriari et mendaces esse adversus veritatem
15 Wannan hikima ba irin wadda take saukowa daga sama ba ce, a maimakon haka, ta duniya ce, mara ruhaniya, ta aljanu.
non est ista sapientia desursum descendens sed terrena animalis diabolica
16 Domin duk inda kishi da kazamin buri suke, a nan ake samun hargitsi da kowanne irin aikin mugunta.
ubi enim zelus et contentio ibi inconstantia et omne opus pravum
17 Amma hikiman nan ta sama, da farko dai tsattsarka ce, mai lumana ce, kamila ce, mai saukin kai, mai tsananin jinkai, mai yawan alheri, mara gajiya, sahihiya kuma.
quae autem desursum est sapientia primum quidem pudica est deinde pacifica modesta suadibilis plena misericordia et fructibus bonis non iudicans sine simulatione
18 Kuma 'ya'yan adalci wanda ake shukawa a cikin salama a tsakanin wadanda ke kulla zumunci.
fructus autem iustitiae in pace seminatur facientibus pacem