< Yaƙub 2 >

1 Ya ku 'yan'uwana, muddin kuna rike da bangaskiyar ku ga Ubangijinmu Yesu Almasihu, Ubangijin daukaka, kada ku nuna bambanci ga wadansu mutane.
Ἀδελφοί μου, μὴ ἐν προσωπολημψίαις ἔχετε τὴν πίστιν τοῦ κυρίου ἡμῶν Ἰησοῦ Χριστοῦ τῆς δόξης;
2 Idan wani mutum ya halarci taron ku da zobban zinariya da tufafi masu kyau, wani matalauci kuma ya shigo da tufafi marasa tsabta.
ἐὰν γὰρ εἰσέλθῃ ⸀εἰςσυναγωγὴν ὑμῶν ἀνὴρ χρυσοδακτύλιος ἐν ἐσθῆτι λαμπρᾷ, εἰσέλθῃ δὲ καὶ πτωχὸς ἐν ῥυπαρᾷ ἐσθῆτι,
3 Sa'adda kuka kula da mai tufafi masu kyau nan, har kuka ce masa, “Idan ka yarda ka zauna a nan wuri mai kyau,'' mataulacin nan kuwa kuka ce masa, “Kai ka tsaya daga can,” ko kuwa, “Zauna a nan kasa a gaba na,”
⸂ἐπιβλέψητε δὲ ἐπὶ τὸν φοροῦντα τὴν ἐσθῆτα τὴν λαμπρὰν καὶ ⸀εἴπητε Σὺ κάθου ὧδε καλῶς, καὶ τῷ πτωχῷ εἴπητε· Σὺ στῆθι ⸂ἢ κάθου ἐκεῖ ὑπὸ τὸ ὑποπόδιόν μου,
4 Ashe ba kuna zartar da hukunci a tsakanin ku ba ke nan? Ba kun zama alkalai na mungayen tunani kenan ba?
⸀οὐδιεκρίθητε ἐν ἑαυτοῖς καὶ ἐγένεσθε κριταὶ διαλογισμῶν πονηρῶν;
5 Ku saurara, ya 'yan'uwana kaunatattu, ashe, Allah bai zabi matalautan duniyar nan su zama mawadata cikin bangaskiya ba, su kuma zama magada a cikin mulkin nan da ya yi wa masu kaunar sa alkawari ba?
ἀκούσατε, ἀδελφοί μου ἀγαπητοί. οὐχ ὁ θεὸς ἐξελέξατο τοὺς πτωχοὺς ⸂τῷ κόσμῳ πλουσίους ἐν πίστει καὶ κληρονόμους τῆς βασιλείας ἧς ἐπηγγείλατο τοῖς ἀγαπῶσιν αὐτόν;
6 Amma, kun wulakanta matalauta! Ashe, ba masu arzikin ne suke matsa maku ba? Ba su ne kuwa suke jan ku zuwa gaban shari'a ba?
ὑμεῖς δὲ ἠτιμάσατε τὸν πτωχόν. οὐχ οἱ πλούσιοι καταδυναστεύουσιν ὑμῶν, καὶ αὐτοὶ ἕλκουσιν ὑμᾶς εἰς κριτήρια;
7 Ba kuma sune ke sabon sunan nan mai girma da ake kiran ku da shi ba?
οὐκ αὐτοὶ βλασφημοῦσιν τὸ καλὸν ὄνομα τὸ ἐπικληθὲν ἐφʼ ὑμᾶς;
8 Duk da haka, idan kuka cika muhimmiyar shari'ar da nassi ya ce, “Ka kaunaci makwabcin ka kamar kanka,” to, madalla.
Εἰ μέντοι νόμον τελεῖτε βασιλικὸν κατὰ τὴν γραφήν Ἀγαπήσεις τὸν πλησίον σου ὡς σεαυτόν, καλῶς ποιεῖτε·
9 Amma in kun nuna bambanci, kun yi zunubi kenan, shari'a ta same ku da laifin keta umarni.
εἰ δὲ προσωπολημπτεῖτε, ἁμαρτίαν ἐργάζεσθε, ἐλεγχόμενοι ὑπὸ τοῦ νόμου ὡς παραβάται.
10 Duk wanda yake kiyaye dukan shari'a, amma ya yi tuntube a hanya daya kadai, ya sabi shari'a gaba daya ke nan.
ὅστις γὰρ ὅλον τὸν νόμον ⸂τηρήσῃ, πταίσῃ⸃ δὲ ἐν ἑνί, γέγονεν πάντων ἔνοχος.
11 Domin wanda ya ce, “Kada ka yi zina,” shi ne kuma ya ce, “Kada ka yi kisan kai.” Idan ba ka yi zina ba amma ka yi kisan kai, ai, ka zama mai taka shari'a kenan.
ὁ γὰρ εἰπών· Μὴ ⸀μοιχεύσῃςεἶπεν καί· Μὴ ⸀φονεύσῃς εἰ δὲ οὐ ⸂μοιχεύεις φονεύεις δέ, γέγονας παραβάτης νόμου.
12 Saboda haka, ku yi magana ku kuma yi aiki kamar wadanda za a hukunta ta wurin 'yantacciyar shari'a.
οὕτως λαλεῖτε καὶ οὕτως ποιεῖτε ὡς διὰ νόμου ἐλευθερίας μέλλοντες κρίνεσθαι.
13 Gama hukunci yana zuwa ba tare da jinkai ba ga wadanda ba su nuna jinkai. Jinkai ya yi nasara a kan hukunci.
ἡ γὰρ κρίσις ἀνέλεος τῷ μὴ ποιήσαντι ἔλεος κατακαυχᾶται ⸀ἔλεος κρίσεως.
14 Ina amfanin haka, 'yan'uwana, idan wani ya ce yana da bangaskiya, kuma ba shi da ayyuka? Wannan bangaskiyar ba za ta cece shi ba, ko za ta iya?
⸀Τίὄφελος, ἀδελφοί μου, ἐὰν πίστιν λέγῃ τις ἔχειν ἔργα δὲ μὴ ἔχῃ; μὴ δύναται ἡ πίστις σῶσαι αὐτόν;
15 Misali, idan wani dan'uwa ko 'yar'uwa ba su da tufa mai kyau ko suna rashin abincin yini.
⸀ἐὰνἀδελφὸς ἢ ἀδελφὴ γυμνοὶ ὑπάρχωσιν καὶ ⸀λειπόμενοιτῆς ἐφημέρου τροφῆς,
16 Misali, idan waninku kuma ya ce masu, “Ku tafi cikin salama, ku kasance da dumi ku koshi.” Idan baku ba su abubuwan da jiki ke bukata ba, ina amfanin wannnan?
εἴπῃ δέ τις αὐτοῖς ἐξ ὑμῶν· Ὑπάγετε ἐν εἰρήνῃ, θερμαίνεσθε καὶ χορτάζεσθε, μὴ δῶτε δὲ αὐτοῖς τὰ ἐπιτήδεια τοῦ σώματος, ⸀τίὄφελος;
17 Haka ma, bangaskiya ita kadai, ba tare da aikin da ya nuna ta ba, matacciya ce.
οὕτως καὶ ἡ πίστις, ἐὰν μὴ ⸂ἔχῃ ἔργα, νεκρά ἐστιν καθʼ ἑαυτήν.
18 To, wani zai ce, “Ai, kai kana da bangaskiya, ni kuwa ina da ayyuka.” Nuna mani bangaskiyar ka ba tare da ayyuka ba, ni kuma in nuna maka bangaskiya ta ta wurin ayyuka na.
Ἀλλʼ ἐρεῖ τις· Σὺ πίστιν ἔχεις κἀγὼ ἔργα ἔχω. δεῖξόν μοι τὴν πίστιν σου ⸀χωρὶςτῶν ⸀ἔργων κἀγώ ⸂σοι δείξω ἐκ τῶν ἔργων μου τὴν ⸀πίστιν
19 Ka gaskanta cewa Allah daya ne; ka yi daidai. Amma ko aljannu ma sun gaskata, kuma suna rawar jiki.
σὺ πιστεύεις ὅτι ⸂εἷς ἐστιν ὁ θεός; καλῶς ποιεῖς· καὶ τὰ δαιμόνια πιστεύουσιν καὶ φρίσσουσιν.
20 Kana so ka sani, kai marar azanci, cewa bangaskiya ba tare da ayyuka ba banza ce?
θέλεις δὲ γνῶναι, ὦ ἄνθρωπε κενέ, ὅτι ἡ πίστις χωρὶς τῶν ἔργων ⸀ἀργήἐστιν;
21 Ba an baratar da Ibrahim mahaifinmu ta wurin ayyuka ba, sa'adda ya mika Ishaku dansa a bisa bagadi?
Ἀβραὰμ ὁ πατὴρ ἡμῶν οὐκ ἐξ ἔργων ἐδικαιώθη, ἀνενέγκας Ἰσαὰκ τὸν υἱὸν αὐτοῦ ἐπὶ τὸ θυσιαστήριον;
22 Ka gani, ashe, bangaskiyar sa ta yi aiki da ayyukan sa, kuma da cewa ta wurin ayyuka bangaskiyar sa ta ginu sosai.
βλέπεις ὅτι ἡ πίστις συνήργει τοῖς ἔργοις αὐτοῦ καὶ ἐκ τῶν ἔργων ἡ πίστις ἐτελειώθη,
23 Nassi kuma ya cika da ya ce, “Ibrahim ya gaskata Allah, aka kuma lisafta masa ita a matsayin adalci.” Aka kuma kira shi abokin Allah.
καὶ ἐπληρώθη ἡ γραφὴ ἡ λέγουσα· Ἐπίστευσεν δὲ Ἀβραὰμ τῷ θεῷ, καὶ ἐλογίσθη αὐτῷ εἰς δικαιοσύνην, καὶ φίλος θεοῦ ἐκλήθη.
24 Kun ga, ta wurin ayyuka ne mutum yake samu baratarwa ba ta wurin bangaskiya kadai ba.
⸀ὁρᾶτεὅτι ἐξ ἔργων δικαιοῦται ἄνθρωπος καὶ οὐκ ἐκ πίστεως μόνον.
25 Ta wannan hanyar kuma, ba Rahab karuwar nan ta samu baratarwa ta wurin ayyuka, da ta marabci masu leken asirin nan ta fitar da su ta wata hanya dabam ba?
ὁμοίως δὲ καὶ Ῥαὰβ ἡ πόρνη οὐκ ἐξ ἔργων ἐδικαιώθη, ὑποδεξαμένη τοὺς ἀγγέλους καὶ ἑτέρᾳ ὁδῷ ἐκβαλοῦσα;
26 Kamar yadda jiki idan ba tare da ruhu ba matacce ne, haka kuma, bangaskiya ba tare da ayyuka ba matacciya ce.
ὥσπερ ⸀γὰρτὸ σῶμα χωρὶςπνεύματος νεκρόν ἐστιν, οὕτως καὶ ἡ πίστις ⸀χωρὶς ἔργων νεκρά ἐστιν.

< Yaƙub 2 >