< Ibraniyawa 9 >

1 To ko da alkawarin farko ma ya na da wurin sujada da kuma ka'idojin sujada a nan duniya.
И первый завет имел постановление о Богослужении и святилище земное;
2 Domin a cikin alfarwar akwai daki da aka shirya, daki na waje wanda ake kira wuri mai tsarki. A wannan wuri akwai kebabbun fitilu, akwai teburi da kuma gurasa.
Ибо устроена была скиния первая, в которой был светильник, и трапеза, и предложение хлебов, которая называется “святое”.
3 Kuma bayan labule na biyun akwai wani daki, wanda ake kira wuri mafi tsarki.
За второю же завесою была скиния, называемая “святое святых”.
4 Yana da bagadin zinariya domin turare. Yana kuma da akwatin alkawarin, wanda aka lailaye shi gaba daya da zinariya. A cikinsa a kwai kaskon zinariya dake dauke da manna, da sandar Haruna wadda tayi toho, da kuma allunan duwatsu na alkawarin.
Имевшая золотую кадильницу и обложенный со всех сторон золотом ковчег завета, где были золотой сосуд с манною, жезл Ааронов расцветший и скрижали завета,
5 A sama da akwatin alkawarin akwai siffofin kerubobi masu daukaka da suke wa marfin jinkai inuwa, wadanda yanzu ba zamu iya yin bayani akansu ba daki daki.
А над ним херувимы славы, осеняющие очистилище; о чем не нужно теперь говорить подробно.
6 Bayan an shirya wadannan abubuwa, firistocin alfarwar sukan shiga daki na wajen alfarwar akai akai suna aikin hidimominsu.
При таком устройстве, в первую скинию всегда входят священники совершать Богослужение;
7 Amma babban firist din ne kadai yake shiga daki na biyun, sau daya tak a shekara, kuma tilas sai tare da jinin hadaya domin kansa, da kuma domin laifuffukan mutane da a kayi ba dagangan ba.
А во вторую однажды в год один только первосвященник, не без крови, которую приносит за себя и за грехи неведения народа.
8 Ruhu Mai Tsarki yana nuna cewar ba'a riga an bayyana hanyar zuwa wuri mafi Tsarki ba muddin alfarwar nan ta farko na a tsaye.
Сим Дух Святой показывает, что еще не открыт путь во святилище, доколе стоит прежняя скиния.
9 Wannan ya zama bayani ne game da lokacin yanzu. Da kyaututtuka da hadayu dukka da ake mikawa basu iya sun kammala lamirin mai yin sujadar ba.
Она есть образ настоящего времени, в которое приносятся дары и жертвы, не могущие сделать в совести совершенным приносящего,
10 Abinci ne da abin sha kawai wadanda aka hada da bukukuwan wanke wanke dabam dabam. Wadannan duka tsare tsare ne da aka shirya a dinga yi a zahiri har sai an shirya sabuwar ka'ida.
И которое с яствами и питиями, и различными омовениями и обрядами, относящимися до плоти, установлены были только до времени исправления.
11 Almasihu yazo a matsayin babban firist na abubuwa masu kyau da suka zo, ta wurin alfarwa babba, kammalalla kuma mafi tsarki wadda ba hannuwan mutane suka gina ba, wadda ba ta wannan duniyar aka halicce ta ba. Amma almasihu ya zo a matsayin babban firist na abubuwa masu kyau da ke zuwa.
Но Христос, Первосвященник будущих благ, пришел с большею и совершеннейшею скиниею, нерукотворенною, то есть, не такового устроения,
12 Ba ta jinin awaki da 'yan, maruka bane, amma Almasihu da jininsa ya shiga wuri mafi tsarki sau daya tak domin kowa dukka ya karbo mana fansa ta har abada. (aiōnios g166)
И не с кровью козлов и тельцов, но со Своею Кровию, однажды вошел во святилище и приобрел вечное искупление. (aiōnios g166)
13 To idan jinin awaki da na bajimai da yayyafa tokar karsana bisa wadanda suka bata tsarkinsu yana tsarkake su ya wanke jikkunansu.
Ибо, если кровь тельцов и волов и пепел телицы чрез окропление освящает оскверненных, дабы чисто было тело,
14 To balle kuma jinin Almasihu, wanda ta wurin Ruhu madawwami ya mika kansa hadaya marar aibi ga Allah, wanda yake wanke lamirinmu daga matattun ayyuka domin muyi bautar Allah mai rai? (aiōnios g166)
То кольми паче кровь Христова, Который Духом Святым принес Себя непорочного Богу, очистит совесть нашу от мертвых дел, для служения Богу живому и истинному! (aiōnios g166)
15 Domin wannan dalili, Almasihu shine magamin sabon alkawari. Wannan kuwa ya kasance ne domin anyi mutuwar da ta 'yantar da wadanda ke karkashin tsohon alkawari daga sakamakon zunubansu, saboda wadanda Allah ya kira su karbi alkawarin gadonsu madawwami. (aiōnios g166)
И потому Он есть Ходатай нового завета, дабы вследствие смерти Его, бывшей для искупления от преступлений, сделанных в первом завете, призванные к вечному наследию получили обетованное. (aiōnios g166)
16 Gama duk inda wani ya rubuta wasiyya ya bari, dole ne a tabbatar da mutuwar wanda yayi wasiyyar nan.
Ибо, где завещание, там необходимо, чтобы последовала смерть завещателя,
17 Gama sai inda akayi mutuwa ake amfani da wasiyya, amma ba ta da amfani idan wanda ya rubuta ta yana nan da rai.
потому что завещание действительно после умерших; оно не имеет силы, когда завещатель жив.
18 Ko alkawari na farko bai tabbata ba sai tare da jini.
Почему и первый завет был утвержден не без крови.
19 Gama bayan Musa ya bada dukkan dokoki da ke cikin shari'ar ga dukkan mutanen, sai ya dauki jinin 'yan marukan da awakin, tare da ruwa, da jan yadi, da reshen itacen doddoya mai soso, ya yayyafa bisa mutanen da kuma littafin dokokin.
Ибо Моисей, произнесши все заповеди по закону пред народом, взял кровь козлов и тельцов с водою и шерстью червленою и иссопом и окропил как самую книгу, так и весь народ,
20 Daga nan yace, “Wannan ne jinin alkawarin da Allah ya bayar da dokoki gareku.”
Говоря: “это кровь завета, который заповедал вам Бог”.
21 Ta haka kuma, ya yayyafa jinin bisa alfarwar da dukkan kayayyakin da ke cikinta wanda ake hidimar firistanci da su.
Также окропил кровью и скинию и все сосуды Богослужебные.
22 Kuma bisa ga shari'a, kusan komai da jini ake tsarkake shi. Idan babu zubar da jini to babu gafarar zunubi.
Да и все почти по закону очищается кровью, и без пролития крови не бывает прощения.
23 Saboda haka ya zama tilas wadannan kayayyaki na kwaikwayon abubuwan dake cikin sama a tsarkake su da hadayar dabbobi. Duk da haka abubuwa na sama dole a tsarkake su da hadaya mafi kyau.
Итак образы небесного должны были очищаться сими, самое же небесное лучшими сих жертвами.
24 Domin Almasihu bai shiga cikin wuri mafi tsarki da aka yi da hannuwa ba, wanda kwaikwayo ne kawai na abin da ke na gaske. Maimakon hakan, ya shiga cikin samaniya da kanta, sa'an nan yaje gaban Allah domin mu.
Ибо Христос вошел не в рукотворное святилище, по образу истинного устроенное, но в самое небо, чтобы предстать ныне за нас пред лице Божее,
25 Bai je wurin don ya mika kansa sau da yawa, kamar yadda firist din alfarwa yake yi ba, wanda yake shiga wuri mafi tsarki kowacce shekara da jinin wata dabba.
И не для того, чтобы многократно приносить Себя, как первосвященник входит во святилище каждогодно с чужою кровью;
26 Idan haka ne, to dole ke nan ya sha wahala akai akai tun farkon duniya. Amma yanzu sau daya ne tak aka bayyana shi a karshen zamanai domin ya kauda zunubi ta wurin mika hadayar kansa. (aiōn g165)
Иначе надлежало бы Ему многократно страдать от начала мира. Он же однажды, к концу веков, явился для уничтожения греха жертвою Своею. (aiōn g165)
27 Kamar yadda aka kaddara wa kowa ya mutu sau daya tak, kuma bayan haka sai shari'a.
И как человекам положено однажды умереть, а потом суд,
28 Haka kuma Almasihu, wanda aka mika shi sau daya tak domin ya dauke zunuban mutane da yawa, zai kuma bayyana karo na biyu, ba domin yin aikin kawar da zunubi ba, amma domin ceton wadanda suke jiran zuwansa da hakuri.
Так и Христос, однажды принесши Себя в жертву, чтобы подьять грехи многих, во второй раз явится не для очищения греха, а для ожидающих Его во спасение.

< Ibraniyawa 9 >