< Ibraniyawa 8 >
1 Yanzu abin da muke kokarin cewa shine: Muna da babban firist wanda ke zaune a hannun dama na kursiyi mai martaba dake sammai.
2 Shi kuwa bawa ne a wannan wuri mai tsarki, haikali na gaskiya wanda Allah ya shirya ba wani bil'adama ba.
3 Kowanne babban firist kuwa yana mika bayebaye da hadayu. Don haka ya kamata a sami abin hadaya.
4 Da a ce Almasihu yana duniya ba zai zama firist ba ko kadan.
5 Domin a kwai masu mika hadaya bisa ga shari'a. Suna hidimar misalin abubuwan da suke inuwar sama. Kamar yadda Allah ya yi wa Musa gargadi yayin da ya ke shirin gina Alfarwa: ''Duba'' Allah ya ce, ''kayi komai bisa ga salon da aka koya maka a bisa dutse.”
6 Amma yanzu hidimar da Almasihu ya karba ta dara tasu dukka, domin kuwa shine matsakancin muhimmin alkawari, wanda aka kammala a kan muhimman alkawura.
7 Domin kuwa idan alkawarin fari ba shi da laifi babu anfanin neman alkawari na biyu.
8 Da Allah ya sami laifi akan mutane, sai ya ce ''Zan sake sabon alkawari da gidan Isra'ila da kuma gidan Yahuza.
9 kuma ba zai zama kamar yadda nayi da kakanninku ba, kamar yadda na rike su a hannu har Na fidda su daga kasar Masar. Basu kuma ci gaba da Alkawarina ba, ni kuwa na yi watsi da su,'' inji Ubangiji.
10 Gama wanna shine alkawarin da zan yi da gidan Isra'ila bayan wadannan kwanaki, Inji Ubangiji. Zan sa shari'a ta a bakinsu in kuma rubuta ta a zuciyarsu, Zan kuma zama Allah a garesu, su kuma su zama jama'ata.
11 Ba za su kuma koyar da makwabta ko yan'uwansu cewa, ''ku san Ubangiji'' gama dukkanin su za su san ni, daga karami har zuwa babba.
12 Zan kuma nuna tausayi ga ayyukan su na rashin adalci, ba kuma zan kara tunawa da zunubansu ba.
13 A kan fadin ''sabo'' ya mayar da alkawarin fari tsoho. Wannan kuma da aka ambata tsoho na shirin bacewa.