< Ibraniyawa 5 >
1 Kowanne babban firist, da yake an zabe shi ne daga cikin mutane, a kansa shi ya wakilci mutane ga al'amarin Allah, don ya mika sadakoki da kuma hadayu domin kawar da zunubai.
omnis namque pontifex ex hominibus adsumptus pro hominibus constituitur in his quae sunt ad Deum ut offerat dona et sacrificia pro peccatis
2 Yana kuma iya tafiyar da jahilai da sangartattu a cikin salihanci, tun da shi ke rarrauna ne shi ta ko'ina.
qui condolere possit his qui ignorant et errant quoniam et ipse circumdatus est infirmitate
3 Saboda haka, wajibi ne ya mika hadayu, ba saboda kawar da zunuban jama'a kadai ba, har ma da na kansa.
et propter eam debet quemadmodum et pro populo ita etiam pro semet ipso offerre pro peccatis
4 Ba wanda zai kai kansa wannan matsayi mai girma, sai dai Allah ya yi kiransa ga haka, kamar yadda aka kirayi Haruna.
nec quisquam sumit sibi honorem sed qui vocatur a Deo tamquam Aaron
5 Haka kuma, Almasihu, ba shi ya daukaka kansa ya zama Babban firist ba, sai dai wannan ne ya sa shi, wanda ya ce da shi, “Kai Dana ne; Yau na zama Uba a gare ka.''
sic et Christus non semet ipsum clarificavit ut pontifex fieret sed qui locutus est ad eum Filius meus es tu ego hodie genui te
6 Kamar dai yadda a wani wuri kuma ya ce, “Kai firist ne na har abada, bisa ga kwatancin Malkisadak.” (aiōn )
quemadmodum et in alio dicit tu es sacerdos in aeternum secundum ordinem Melchisedech (aiōn )
7 Almasihu, a lokacin zamansa a duniya, ya yi addu'o'i da roke-roke, tare da kuka mai tsanani, har da hawaye, ga wannan da yake da ikon cetonsa daga mutuwa, aka kuwa saurare shi saboda tsannin mika kansa.
qui in diebus carnis suae preces supplicationesque ad eum qui possit salvum illum a morte facere cum clamore valido et lacrimis offerens et exauditus pro sua reverentia
8 Ko da yake shi Da ne, ya koyi biyayya ta wurin wuyar da ya sha.
et quidem cum esset Filius didicit ex his quae passus est oboedientiam
9 Har ya kai ga kammala, sai ya zama tushe madawwami, ceto ga dukkan wadanda suke masa biyayya. (aiōnios )
et consummatus factus est omnibus obtemperantibus sibi causa salutis aeternae (aiōnios )
10 Gama Allah yana kiransa Babban firist, bisa ga kwatancin Malkisadak.
appellatus a Deo pontifex iuxta ordinem Melchisedech
11 Muna da abu da yawa da za mu fada a game da Yesu, amma zai yi wuyar bayani, da yake basirarku ta dushe.
de quo grandis nobis sermo et ininterpretabilis ad dicendum quoniam inbecilles facti estis ad audiendum
12 Ko da yake yanzu kam, ya kamata ku zama masu koyarwa, duk da haka, ashe, ba ku wuce wani ya sake koya muku jigajigan farko na Maganar Allah ba? har ya zamana sai an ba ku madara ba abinci mai tauri ba?
etenim cum deberetis magistri esse propter tempus rursum indigetis ut vos doceamini quae sint elementa exordii sermonum Dei et facti estis quibus lacte opus sit non solido cibo
13 To, duk wanda yake madara ce abincinsa, bai kware da maganar adalci ba, kamar jariri yake.
omnis enim qui lactis est particeps expers est sermonis iustitiae parvulus enim est
14 Amma abinci mai tauri, ai, na manya ne, wato wadanda hankalinsu ya horu yau da kullum, don su rarrabe nagarta da mugunta.
perfectorum autem est solidus cibus eorum qui pro consuetudine exercitatos habent sensus ad discretionem boni ac mali