< Ibraniyawa 4 >
1 Saboda haka, sai muyi lura kwarai don kada wani ya kasa kai ga shiga hutun da aka alkawarta maku na Allah.
Let us fear therefore, lest haply, a promise being left of entering into his rest, any one of you should seem to have come short of it.
2 Don mun ji albishir game da hutun Allah kamar yadda aka fada masu. Amma wancan sakon bai anfana ga wadanda suka ji ba tare da sun bada gaskiya ga sakon ba.
For indeed we have had good tidings preached unto us, even as also they: but the word of hearing did not profit them, because they were not united by faith with them that heard.
3 Ai mu, wadanda muka gaskata-mune zamu shiga wannan hutun, kamar yadda ya ce, “Yadda na yi rantsuwa cikin fushina, baza su shiga hutu na ba.” Ya fadi hakan, ko da yake ya gama aikin hallittarsa tun daga farkon duniya.
For we which have believed do enter into that rest; even as he hath said, As I sware in my wrath, They shall not enter into my rest: although the works were finished from the foundation of the world.
4 Domin yayi fadi a wani wuri game da rana ta bakwai, “Allah ya huta a rana ta bakwai daga dukkan ayyukansa.”
For he hath said somewhere of the seventh [day] on this wise, And God rested on the seventh day from all his works;
5 Ya sake cewa, “Baza su taba shiga hutu na ba.”
and in this [place] again, They shall not enter into my rest.
6 Saboda haka, tun da hutun Allah na kebe domin masu su shiga, kuma tun da Isra'ilawa da yawa wadanda suka ji sakon nan mai kyau game da hutunsa ba su shiga ba saboda rashin biyayya,
Seeing therefore it remaineth that some should enter thereinto, and they to whom the good tidings were before preached failed to enter in because of disobedience,
7 Allah ya sake shirya wata rana da ake kira, “Yau.” Ya sa wannan rana sa'adda yayi magana ta wurin Dauda, wanda ya ce tun da dadewa da aka fara fada, “Yau idan kun ji muryarsa, kada ku taurare zukatanku.”
he again defineth a certain day, saying in David, after so long a time, Today, as it hath been before said, Today if ye shall hear his voice, Harden not your hearts.
8 Don idan Joshua ya ba su hutu, da Allah ba zai sake magana a kan wata rana ba.
For if Joshua had given them rest, he would not have spoken afterward of another day.
9 Saboda haka, akwai hutun asabar kebabbe ga mutanen Allah.
There remaineth therefore a sabbath rest for the people of God.
10 Don shi wanda ya shiga hutun Allah shi kansa ma ya huta daga ayyukansa, kamar yadda Allah yayi da nasa.
For he that is entered into his rest hath himself also rested from his works, as God did from his.
11 Saboda haka muyi marmarin shiga wancan hutun, don kada kowa ya fadi ga irin rashin biyayyar da suka yi.
Let us therefore give diligence to enter into that rest, that no man fall after the same example of disobedience.
12 Maganar Allah kuwa rayayyiyace, kuma mai ci, fiye da takobi mai kaifi-biyu. Takan ratsa har tsakanin rai da ruhu, kuma tana kaiwa bargo. Takan iya bincika tunanin zuciya da manufarta.
For the word of God is living, and active, and sharper than any two-edged sword, and piercing even to the dividing of soul and spirit, of both joints and marrow, and quick to discern the thoughts and intents of the heart.
13 Babu halittaccen abu da ke boye a idon Allah. Sai dai, kome a sarari yake, kuma a bayyane yake a idonsa wanda lallai ne zamu bada lissafin kanmu a gare shi.
And there is no creature that is not manifest in his sight: but all things are naked and laid open before the eyes of him with whom we have to do.
14 Da yake muna da babban firist wanda ya ratsa sammai, Yesu Dan Allah, sai mu riki bangaskiyarmu da karfi.
Having then a great high priest, who hath passed through the heavens, Jesus the Son of God, let us hold fast our confession.
15 Domin babban firist namu ba marar tausayi ga kasawarmu bane, amma wanda aka jarraba ne ta ko wanne hali irin yadda aka yi mana, sai dai ba'a same shi da zunubi ba.
For we have not a high priest that cannot be touched with the feeling of our infirmities; but one that hath been in all points tempted like as [we are, yet] without sin.
16 Sai mu zo wurin kursiyin alheri gabagadi, domin a yi mana jinkai mu kuwa sami alherin da zai taimake mu a lokacin bukata.
Let us therefore draw near with boldness unto the throne of grace, that we may receive mercy, and may find grace to help [us] in time of need.