< Ibraniyawa 11 >

1 Bangaskiya ita ce tabbatawar al'muran da muke begensu. Ita ce tabbatawar al'amuran da idanu basu gani.
Víra pak jest nadějných věcí podstata, a důvod neviditelných.
2 Domin ta wurin ta ne kakanninmu suka sami yardar Allah.
Pro ni zajisté svědectví došli předkové.
3 Ta wurin ta ne aka hallicci duniya da umarnin Allah, har ma abubuwan da ake gani ba'a yi su daga abubuwan da suka kasance ba. (aiōn g165)
Věrou rozumíme, že učiněni jsou věkové slovem Božím, takže z ničeho jest to, což vidíme, učiněno. (aiōn g165)
4 Ta dalilin bangaskiya ne Habila ya mikawa Allah hadaya da ta fi dacewa fiye da ta Kayinu. Don haka ne kuma aka yaba masa akan cewa shi adali ne. Ya sami yardar Allah sabili da sadakarsa da ya bayar. Don haka kuma, harwayau Habila yana magana, ko da shike ya rigaya ya mutu.
Věrou lepší obět Bohu obětoval Abel, nežli Kain, skrze kteroužto svědectví obdržel, že jest spravedlivý, jakž sám Bůh darům jeho svědectví vydal. A skrze tu víru, již umřev, ještě mluví.
5 Ta dalilin bangaskiya aka dauki Anuhu zuwa sama domin kar ya ga mutuwa. “Ba a same shi ba kuwa, domin Allah ya dauke shi.” Kamin a dauke shi an shaida da cewa ya faranta wa Allah zuciya.
Věrou Enoch přenesen jest, aby neviděl smrti, a není nalezen, proto že jej Bůh přenesl. Prvé zajisté, než jest přenesen, svědectví měl, že se líbil Bohu.
6 Zai yi wuya matuka a faranta wa Allah zuciya in ba tare da bangaskiya ba. Domin ya kamata dukkan wanda zai zo ga Allah, tilas ne ya bada gaskiya da kasancewar sa, kuma shi mai sakamako ne ga dukkan masu nemansa.
Bez víry pak nemožné jest líbiti se Bohu; nebo přistupující k Bohu věřiti musí, že jest Bůh, a těm, kteříž ho hledají, že odplatu dává.
7 Ta dalilin bangaskiya Nuhu, ya karbi sako daga Allah akan al'amuran da ba'a gani ba, ta wurin girmamawa da rawar jiki. ya gina jirgin ruwa domin ya ceci iyalan sa. Dalilin haka kwa, Allah ya hallakar da duniya, Nuhu kwa ya gaji adalci wadda ke bisa ga bangaskiya.
Věrou napomenut jsa od Boha Noé o tom, čehož ještě nebylo viděti, boje se, připravoval koráb k zachování domu svého; skrze kterýžto koráb odsoudil svět, a spravedlnosti té, kteráž jest z víry, učiněn jest dědicem.
8 Ta dalilin bangaskiya ne Ibrahim, sa'an da aka kira shi, ya yi biyayya sai ya tafi wurin da zai karba a matsayin gado. Ya kwa fita bai ma san inda za shi ba.
Věrou, povolán jsa Abraham, uposlechl Boha, aby odšel na to místo, kteréž měl vzíti za dědictví; i šel, nevěda, kam příjde.
9 Ta dalilin bangaskiya kuma ya zauna bare a kasar alkawari. Ya yi zama cikin Alfarwa tare da Ishaku da Yakubu, magadan alkawari guda tare da shi.
Věrou bydlil v zemi zaslíbené jako v cizí v staních přebývaje s Izákem a s Jákobem, spoludědici téhož zaslíbení.
10 Domin yana hangar birnin da ke da tushi, Birnin da mai zaiyanar sa da ginin sa shine Allah.
Nebo očekával města základy majícího, jehožto řemeslník a stavitel jest Bůh.
11 Ta dalilin bangaskiya, Ibrahim ya sami haihuwa ko da shike shi da matarsa Saratu sun yi nisa a cikin shekaru, kuma Saratu bakarariya ce, ta kuma wuce lokacin haihuwa. Tun da shike sun amince da wanda ya yi musu alkawari mai aminci ne.
Věrou také i Sára moc ku početí semene přijala, a mimo čas věku porodila, když věřila, že jest věrný ten, jenž zaslíbil.
12 Sabo da haka, ta wurin mutumin nan daya, wanda ya ke kamar matacce ne, aka haifi zuriya mai dimbin yawa, su ka yawaita kamar taurari a sama kamar yashi a bakin teku, wanda ba shi kidayuwa.
A protož i z jednoho, a to již téměř umrtveného, rozplozeno jest potomků množství veliké, jako jest množství hvězd nebeských, a jako písek nesčíslný, kterýž jest na břehu mořském.
13 Dukkan su kuwa suka mutu a cikin bangaskiya ba tare da sun karbi alkawarin ba. Maimakon haka, sun hango, kuma sun marabcesu daga nesa, sai suka amince su baki ne kuma matafiya ne a duniya.
Podle víry zemřeli ti všickni, nevzavše zaslíbení, ale zdaleka je viděvše, jim i věřili, i je vítali, a vyznávali, že jsou hosté a příchozí na zemi.
14 Gama wadanda suka yi furci haka sun nuna a fili cewa suna bidar kasa ta kansu.
Nebo ti, kteříž tak mluví, zjevně to prokazují, že vlasti hledají.
15 Da kamar suna tunanin kasar da suka fita daga ciki, da sun sa mi damar komawa.
A jistě, kdyby se byli na onu rozpomínali, z kteréž vyšli, měli dosti času zase se navrátiti.
16 Amma kamar yadda yake, sun bukaci kasa mafi dacewa, wato, wadda take a sama. Saboda haka ne Allah bai ji kunyar a kira shi Allahnsu ba, da shike ya shirya birni dominsu.
Ale oni lepší vlasti žádají, to jest nebeské. Protož i sám Bůh nestydí se slouti jejich Bohem; nebo jim připravil město.
17 Ta dalilin bangaskiya ne Ibrahim, sa'adda aka yi masa gwaji, akan ya mika Ishaku dansa hadaya.
Věrou obětoval Abraham Izáka, byv pokoušín, a to jednorozeného obětoval ten, kterýž byl zaslíbení přijal,
18 Shi ne kuwa makadaicin dansa, wanda aka yi alkawari da cewa, “Ta wurinsa ne za a kira zuriyarka.”
K němuž bylo řečeno: V Izákovi nazváno bude tobě símě,
19 Ibrahim ya yi tunani da cewa Allah na da ikon tada Ishaku ko daga cikin matattu ma, haka kuwa yake a misalce, daga matattun ne ya sake karbarsa.
Tak o tom smýšleje, že jest mocen Bůh i z mrtvých vzkřísiti; odkudžto jej jako z mrtvých vzkříšeného přijal.
20 Ta dalilin bangaskiya ne kuma Ishaku ya albarkaci Yakubu da Isuwa game da abubuwan da ke zuwa a gaba.
Věrou o budoucích věcech požehnání dal Izák Jákobovi a Ezau.
21 Dalilin bangaskiya ne Yakubu, sa'adda yake bakin mutuwa, ya albarkaci 'ya'yan Yusufu dukkansu biyu. Yakubu ya yi ibada, yana tokare a kan sandarsa.
Věrou Jákob, umíraje, každému z synů Jozefových požehnání dával, a poklonil se podepřev se na vrch hůlky své.
22 Ta dalilin bangaskiya Yusufu, sa'adda karshensa ya kusa, ya yi magana game da fitar 'ya'yan Isra'ila daga Masar har ya umarce su game da kasussuwansa.
Věrou Jozef, dokonávaje, o vyjití synů Izraelských zmínku učinil, a o kostech svých poručil.
23 Ta dalilin bangaskiya Musa, sa'adda aka haife shi, iyayensa suka 'boye shi kimanin watanni uku domin kyakkyawan yaro ne shi, kuma basu ji tsoron dokar sarki ba.
Věrou Mojžíš, narodiv se, ukryt byl za tři měsíce od rodičů svých, protože viděli krásné pacholátko, a nebáli se rozkazu královského.
24 Ta dalilin bangaskiya ne kuma Musa, sa'adda ya girma, yaki a kira shi 'dan diyar Fir'auna.
Věrou Mojžíš, dorostlý již jsa, odepřel slouti synem dcery faraonovy,
25 A maimakon haka, ya amince ya sha azaba tare da jama'ar Allah, a kan shagali da annashuwar zunubi na karamin lokaci.
Vyvoliv sobě raději protivenství trpěti s lidem Božím, nežli časné a hříšné pohodlí míti,
26 Ya fahimci cewa wulakanci domin bin Almasihu babbar wadata ce fiye da dukiyar Masar. Gama ya kafa idanunsa a kan sakamakon da ke gaba.
Větší sobě pokládaje zboží nad Egyptské poklady pohanění Kristovo; nebo prohlédal k hojné odplatě.
27 Ta dalilin bangaskiya Musa ya bar Masar. Bai ji tsoron fushin sarki ba, ya jure kamar yana ganin wannan da ba a iya ganinsa
Věrou opustil Egypt, neboje se hněvu královského; nebo jako by viděl Neviditelného, tak se utvrdil.
28 Ta dalilin bangaskiya ya yi idin ketarewa da kuma yayyafa jini, domin kada mai hallaka 'ya'yan fari ya taba 'ya'yan fari na Isra'ila.`
Věrou slavil hod beránka a vylití krve, aby ten, jenž hubil prvorozené, nedotekl se jich.
29 Ta dalilin bangaskiya suka haye baharmaliya kamar bushashiyar kasa. Sa'adda Masarawa su ka yi kokarin hayewa, bahar din ta hadiye su.
Věrou přešli moře červené jako po suchu; o čež pokusivše se Egyptští, ztonuli.
30 Ta dalilin bangaskiya ganuwar Yeriko ta fadi, bayan sun kewaya ta har kwana bakwai.
Věrou zdi Jericha padly, když je obcházeli za sedm dní.
31 Ta dalilin bangaskiya Rahab karuwan nan bata hallaka tare da marasa biyayya ba, don ta saukar da masu leken asirin kasa a gidanta, ta kuma sallame su lafiya.
Věrou Raab nevěstka nezahynula s neposlušnými, pokojně přijavši špehéře.
32 Me kuma za mu ce? Gama lokaci zai kasa mini idan zan yi magana game da Gidiyon, Barak, Samson, Yefta, Dauda, Sama'ila, da annabawa.
A coť mám více praviti? Nepostačíť mi zajisté čas k vypravování o Gedeonovi, a Barákovi, a Samsonovi a Jefte, a Davidovi, a Samuelovi, a prorocích.
33 Ta dalilin bangaskiya suka ci nasara kan kasashe, suka yi aikin adalci, sa'annan suka karbi alkawura. Suka rufe bakin zakuna,
Kteříž skrze víru vybojovávali království, činili spravedlnost, docházeli zaslíbení, zacpávali ústa lvům,
34 suka kashe karfin wuta, suka tsira daga bakin takobi, suka sami warkaswa daga cutattuka, suka zama jarumawan yaki, sa'annan suka ci nasara akan rundunar sojojin al'ummai.
Uhašovali moc ohně, utekli ostrosti meče, zmocněni bývali v mdlobách, silní učiněni v boji, vojska zaháněli cizozemců.
35 Mata kuwa suka karbi matattunsu da aka tayar daga mutuwa. Aka azabtar da wadansu, ba su nemi yancin kansu ba, domin suna begen tashi daga mattatu.
Ženy přijímaly mrtvé své vzkříšené. Jiní pak roztahováni jsou, neoblíbivše sobě vysvobození, aby lepšího dosáhli vzkříšení.
36 Wadansu kuwa suka sha ba'a da duka da bulala, har ma da sarka da kurkuku.
Jiní pak posměchy a mrskáním trápeni, ano i vězeními a žaláři.
37 A ka jejjefe su. Aka tsaga su kashi biyu da zarto. A ka karkashe su da takobi. Su na yawo sanye da buzun tumakai da na awaki, suka yi hijira, suka takura, suka wulakantu.
Kamenováni jsou, sekáni, pokoušíni, mečem zmordováni; chodili v kožích ovčích a kozelčích, opuštěni, souženi, a zle s nimi nakládáno,
38 Duniya ma ba ta dauke su a matsayin komai ba. Suka yi ta yawo a jazza, da duwatsu, da kogwanni, da kuma ramummuka.
Jichžto nebyl svět hoden, po pustinách bloudíce, i po horách, a jeskyních, i v doupatech země.
39 Ko da yake mutanen nan amintattun Allah ne domin bangaskiyarsu, basu karbi cikar alkawarin ba tukunna.
A ti všickni svědectví dosáhše skrze víru, neobdrželi zaslíbení,
40 Domin Allah ya shirya mana wani abu mafi kyau ba kuwa za su kammala ba sai tare da mu.
Protože Bůh něco lepšího nám obmýšlel, aby oni bez nás nepřišli k dokonalosti.

< Ibraniyawa 11 >