< Ibraniyawa 10 >
1 Domin shari'a hoto ce na kyawawan abubuwan da ke zuwa, ba ainihin siffar wadannan abubuwa ba. Wadanda ke gusowa kusa da Allah ba za su taba ingantuwa ta wurin hadayu da firistoci ke mikawa shekara da shekaru ba.
For the law, having a shadow of the good to come, not the very image of the things, can never with the same sacrifices year by year, which they offer continually, make perfect those who draw near.
2 In ba haka ba, ba sai a dena mika hadayun ba? Bisa ga wannan al'amari, inda sun tsarkaka sau daya tak da masu sujada ba su san menene zunubi ba.
Or else would not they have ceased to be offered, because the worshipers, having been once cleansed, would have had no more consciousness of sins?
3 Amma wadannan hadayun sun zama matuni ne na zunubi shekara biye da shekara.
But in those sacrifices there is a yearly reminder of sins.
4 Domin ba shi yiwuwa jinin bijimai da awakai su kawar da zunubai.
For it is impossible that the blood of bulls and goats should take away sins.
5 Yayin da Almasihu ya zo duniya, ya ce, “Ba hadayu da sadakoki kake marmari ba. Maimakon haka, ka shirya mini jiki domin hadaya.
Therefore when he comes into the world, he says, “You did not desire sacrifice and offering, but you prepared a body for me.
6 Baka murna domin sadakoki da hadayu na konawa domin zunubi.
You had no pleasure in whole burnt offerings and sacrifices for sin.
7 Sai na ce, 'Duba, gani na zo in yi nufinka, kamar yadda aka rubuta akaina.'''
Then I said, ‘Behold, I have come (in the scroll of the book it is written of me) to do your will, O God.’”
8 Da fari Yace ''ba hadayu, ko sadakoki, ko kuma hadaya ta konawa domin zunubi kake bukata ba. Ba ka kuwa jin dadinsu.'' Wadannan sune hadayun da ake bayarwa bisa ga shari'a.
Previously saying, “Sacrifices and offerings and whole burnt offerings and sacrifices for sin you did not desire, neither had pleasure in them” (those which are offered according to the law),
9 Sa'annan sai ya ce ''gani na zo domin in aikata nufinka.” Ya kawar da hidimar farko domin ya kafa hidima ta biyu.
then he has said, “Behold, I have come to do your will.” He takes away the first, that he may establish the second,
10 A hidima ta biyu, an kebe mu ga Allah ta wurin nufinsa ta wurin hadayar jikin Yesu Almasihu bugu daya ba kari.
by which will we have been sanctified through the offering of the body of Jesus Christ once for all.
11 Haka, kowanne firist ya ke tsayawa kulliyomi domin ya yi hidima ga Allah. A kullum yana mika hadayu, iri daya, koda shike ba za su taba kawar da zunubai ba.
Every priest indeed stands day by day serving and offering often the same sacrifices, which can never take away sins,
12 A ta wata hanya kuma, Almasihu ya mika hadaya sau daya tak domin zunubai har abada, ya zauna a hannun dama na Allah.
but he, when he had offered one sacrifice for sins forever, sat down on the right hand of God,
13 Yana jiran har a maida makiyansa matashin sawayensa.
from that time waiting until his enemies are made the footstool of his feet.
14 Domin ta wurin hadaya guda dayan nan ya kammala har abada ga wadanda suka sadaukar da kansu ga Allah.
For by one offering he has perfected forever those who are being sanctified.
15 Kuma Ruhu mai Tsarki ya shaida mana. Abu na farko yace,
The Holy Spirit also testifies to us, for after saying,
16 “Wannan shi ne alkawarin da zan yi da su a bayan kwanakin nan,' inji Ubangiji Zan sa dokokina a cikin zukatansu, kuma zan rubuta su a lamirinsu.
“This is the covenant that I will make with them after those days,” says the Lord, “I will put my laws on their heart, I will also write them on their mind;” then he says,
17 Ba zan sake tunawa da zunubansu da kurakuransu ba.''
“I will remember their sins and their iniquities no more.”
18 Yanzu fa duk in da aka sami gafara domin wadannan abubuwa, babu wata hadaya domin zunubi.
Now where remission of these is, there is no more offering for sin.
19 Saboda haka, yan'uwa, ba mu da shakkar shigowa wurin nan mafi tsarki ta wurin jinin Yesu.
Having therefore, brothers, boldness to enter into the holy place by the blood of Jesus,
20 Wannan ita ce sabuwar rayayyar hanya da ya bude mana ta wurin labulen, wato ta wurin jikinsa.
by the way which he dedicated for us, a new and living way, through the veil, that is to say, his flesh,
21 Saboda muna da babban firist a gidan Allah.
and having a great priest over God’s house,
22 Bari mu matso kusa da sahihiyar zuciya, da kuma cikakken gabagadi cikin bangaskiya, da zuciyarmu wadda aka tsarkake daga mummunan tunani, da kuma jikunanmu wankakku da ruwa mai tsabta.
let’s draw near with a true heart in fullness of faith, having our hearts sprinkled from an evil conscience and having our body washed with pure water,
23 Bari mu rike da karfi shaidar bangaskiyar begenmu, ba tare da raurawa ba, domin Allahn, da ya yi alkawari, mai aminci ne.
let’s hold fast the confession of our hope without wavering; for he who promised is faithful.
24 Bari mu kuma yi lura yadda za mu iza juna ga kauna da ayyuka masu dacewa.
Let’s consider how to provoke one another to love and good works,
25 Kada mu fasa zumunci da juna, kamar yadda wadansu sukan yi. A maimakon haka, bari mu karfafa juna a kulluyomin, kamar yada kuke ganin kusantowar ranan nan.
not forsaking our own assembling together, as the custom of some is, but exhorting one another, and so much the more as you see the Day approaching.
26 Saboda idan mun ci gaba da zunubin ganganci bayan mun rigaya mun sami wannan sanin gaskiyar, hadayar irin wannan zunubi bata samuwa.
For if we sin willfully after we have received the knowledge of the truth, there remains no more a sacrifice for sins,
27 Maimakon haka, sai fargabar babban tsoron hukunci, da kuma wuta mai zafi, da zata cinye makiyan Allah.
but a certain fearful expectation of judgment, and a fierceness of fire which will devour the adversaries.
28 Dukkan wanda ya ki bin dokar Musa zai mutu ba tausayi ta wurin shaidu biyu ko uku.
A man who disregards Moses’ law dies without compassion on the word of two or three witnesses.
29 Wanne irin hukunci kuke tsammani ya dace ga wadanda suka raina Dan Allah, duk wadanda suka maida jinin alkawarin nan kamar ba tsarkakakke ba, wanda ta wurin jinin nan ne aka kebe shi ga Allah- wadanda suka wulakantar da Ruhun alheri?
How much worse punishment do you think he will be judged worthy of who has trodden under foot the Son of God, and has counted the blood of the covenant with which he was sanctified an unholy thing, and has insulted the Spirit of grace?
30 Domin mun san wanda yace, “Ramako nawa ne; Zan yi sakayya.'' Sa'annan kuma, “Ubangiji zai hukumta jama'arsa.”
For we know him who said, “Vengeance belongs to me. I will repay,” says the Lord. Again, “The Lord will judge his people.”
31 Abin tsoro ne a fada cikin hannuwan Allah mai rai!
It is a fearful thing to fall into the hands of the living God.
32 Amma ku tuna da kwanakin baya, bayan da ku ka sami haske, yadda kuka jure babban fama cikin wahala.
But remember the former days, in which, after you were enlightened, you endured a great struggle with sufferings:
33 Aka kunyatar da ku a gaban jama'a, ta wurin ba'a da cin mutunci, kuna kuma dandana irin azabar da wadansu suka shiga ciki.
partly, being exposed to both reproaches and oppressions, and partly, becoming partakers with those who were treated so.
34 Domin kuna da tausayi ga wadanda suke kurkuku, da farin ciki, kun amince da kwace na dukiyarku da aka yi, kun mallaki madauwamiyar mallaka mafi kyau. Dominn kun ji tausayina sa'adda na ke a kurkuku.
For you both had compassion on me in my chains and joyfully accepted the plundering of your possessions, knowing that you have for yourselves a better possession and an enduring one in the heavens.
35 Don haka kada ku yarda gabagadinku, wanda ke da babban sakamako.
Therefore do not throw away your boldness, which has a great reward.
36 Domin kuna bukatar hakuri don ku sami abin da Allah ya alkawarta, bayan kun aikata nufinsa.
For you need endurance so that, having done the will of God, you may receive the promise.
37 “Domin a dan karamin lokaci, mai zuwan nan zai zo ba zai yi jinkiri ba.
“In a very little while, he who comes will come and will not wait.
38 Adalina kuwa zai rayu ta wurin bangaskiya. In kuwa ya ja da baya, ba zan yi farin ciki dashi ba.”
But the righteous one will live by faith. If he shrinks back, my soul has no pleasure in him.”
39 Amma mu bama cikin wadanda suka ja da baya zuwa hallaka. Maimakon haka, muna cikin wadanda suke da bangaskiya domin kula da rayukanmu.
But we are not of those who shrink back to destruction, but of those who have faith to the saving of the soul.