< Galatiyawa 1 >
1 Wannan Bulus manzo ne. Manzancina kuwa, bai zo daga mutane ba ko mutum, amma ta wurin Yesu Almasihu da Allah Uba wanda da ya tashe shi daga matattu.
2 Ni da dukan 'yan'uwa da nake tare da su a nan, ina rubuto maku ku iklisiyoyi da ke a Galatiya.
3 Alheri zuwa gare ku da salama daga Allah Ubanmu da kuma Ubangjinmu Yesu Almasihu,
4 wanda ya ba da kansa domin zunubanmu saboda ya kubutar da mu daga wannan mugun zamani, bisa ga nufin Allah da Ubanmu. (aiōn )
5 Daukaka ta tabbata a gare shi har abada abadin. (aiōn )
6 Na yi mamaki kwarai yadda kuka juya da sauri zuwa wata bishara daban. Na yi mamakin cewa kuna juyawa daga shi wanda ya kira ku ta wurin alherin Almasihu.
7 Ba wata bishara, amma akwai wadansu mutane da suke kawo maku rudani kuma suna so su gurbata bisharar Almasihu.
8 Amma, ko da mu ne ko mala'ika daga sama ya yi maku shelar wata bishara ta daban da wadda muka yi shelar ta, la'ananne ne.
9 Kamar yadda muka fadi maku a da, yanzu kuma ina sake fada, “Idan wani ya yi maku shelar wata bishara ta daban da wadda kuka karba, la'ananne ne.”
10 To yanzu ina neman shaidar mutane ne ko Allah? Ina neman in gamshi mutane ne? Idan har yanzu ina kokarin in gamshi mutane ne, ni ba bawan Almasihu ba ne.
11 Ina son ku sani fa 'yan'uwa, cewa bisharar da nake shelar ta ba daga mutane take ba.
12 Ban karbe ta daga mutum ba, ba ma wanda ya koyar mani A maimakon haka, ta wurin wahayin Yesu Almasihu ne zuwa gare ni.
13 Kun riga kun ji game da rayuwa ta a da cikin Yahudanci, yadda da nake da kwazon tsananta wa iklisiyar Allah fiye da misali kuma ina lalatar da ita.
14 Ina gaba-gaba cikin Yahudanci fiye da yawancin tsararrakina. A kwazo kuwa fiye da kima game da al'adun ubannina.
15 Amma ya gamshi Allah ya zabe ni daga cikin mahaifiyata. Ya kira ni ta wurin alherinsa.
16 Ya bayyana dansa a gareni, saboda in yi shelar sa cikin al'ummai. Nan da nan, ban nemi shawarar nama da jini ba
17 kuma ban tafi Urushalima ba wurin wadanda suka zama manzanni kafin ni. Maimakon haka sai na tafi Arebiya, daga nan sai na dawo Dimashku.
18 Bayan shekara uku na je Urushalima don in san Kefas, na zauna da shi na kwana goma sha biyar.
19 Amma ban ga ko daya daga cikin manzannin ba sai Yakubu kadai, dan'uwan Ubangiji.
20 Duba, a gaban Allah, ba karya nake yi ba cikin abin da na rubuta maku.
21 Daga nan sai na je lardin Suriya da Kilikiya.
22 Har a lokacin babu wanda ya san ni a fuska a iklisiyoyin Yahudiya da suke cikin Almasihu,
23 amma sai labari kawai suke ji, “Wanda a da yake tsananta mana yanzu yana shelar bangaskiyar da a da yake rusarwa.”
24 Suna ta daukaka Allah saboda ni.