< Galatiyawa 5 >
1 Saboda 'yanci ne Almasihu ya yantar da mu. Sai ku dage kada ku sake komawa cikin kangin bauta.
2 Duba, ni Bulus, ina gaya maku cewa idan an yi maku kaciya, Almasihu ba zai zama da amfani a gare ku ba a kowace hanya.
3 Haka kuma, na shaida ga ko wanda mutum wadda aka yi masa kaciya ya zama dole ya yi biyayya da dukan shari'a.
4 Kun rabu da Almasihu, dukanku wadanda aka “baratar” ta wurin shari'a. Kun fadi daga alheri.
5 Domin ta wurin Ruhu, cikin bangaskiya, muna jira gabagadi na adalci.
6 A cikin Almasihu kaciya ko rashin kaciya ba shi da ma'ana. Bangaskiya kadai mai aiki ta wurin kauna ita ce mafi muhimmanci.
7 Da kuna tsere da kyau, wanene ya tsayar da ku daga yin biyayya da gaskiya?
8 Rinjayarwa da ke sa yin wannan, ba daga wanda ya kira ku ba ne
9 Ai karamin yisti shi yake sa dukan kulli ya kumbura.
10 Ina da wannan gabagadin game da ku cikin Ubangiji cewa ba za ku yi tunani a wata hanya daban ba. Shi wanda ya rikita ku zai sha hukunci ko wanene shi.
11 'Yan'uwa, idan har yanzu wa'azin kaciya nake yi, don me har yanzu ake tsananta mani? Inda haka ne dutsen sanadin tuntube game da gicciye da ya ragargaje.
12 Ina fata wadanda suke badda ku su maida kansu babani.
13 'Yan'uwa, domin Allah ya kira ku zuwa ga yanci, kada dai ku mori yancin nan ya zama zarafi domin jiki. A maimakon haka ta wurin kauna ku yi wa juna hidima.
14 Saboda dukan shari'a ta cika ne a cikin doka guda daya; “Ka kaunaci makwabcinka kamar kanka.”
15 Amma idan kuna cizo da hadiye juna, ku lura kada ku hallakar da junanku.
16 Na ce, ku yi tafiya cikin Ruhu, ba za ku cika sha'awoyin jiki ba.
17 Domin jiki yana gaba mai karfi da Ruhu, Ruhu kuma yana gaba da jiki. Domin wadannan akasin juna suke. Sakamakon shine ba za ku iya yin abin da kuke so ba.
18 Amma idan Ruhu ne ke bishe ku, ba ku karkashin shari'a.
19 Yanzu ayyukan jiki a bayyane suke. Sune al'amuran lalata, rashin tsarki, sha'awoyi,
20 bautar gumaka, sihiri, yawan fada, jayayya, kishi, zafin fushi, gasa, tsattsaguwa, hamayya,
21 hassada, buguwa, buguwa da tarzoma, da dai sauran irin wadannan abubuwa. Na gargade ku, kamar yadda a da na gargade ku, cewa wadanda suke aikata wadannan abubuwa ba za su gaji mulkin Allah ba.
22 Amma 'ya'yan Ruhu kauna ne, farinciki, salama, hakuri, kirki, nagarta, bangaskiya,
23 tawali'u, da kamun kai. Babu wata shari'a da ke gaba da wadannan abubuwa.
24 Wadanda suke na Almasihu Yesu sun giciye halin jiki tare da marmarin sa da miyagun sha'awoyi.
25 Idan muna zaune cikin Ruhu, mu yi tafiya da Ruhu.
26 Kada mu zama masu girman kai, ko muna cakunar juna, ko muna kishin juna.