< Galatiyawa 4 >
1 Ina cewa muddin magaji yaro ne, babu bambancin sa da bawa, ko da yake shine mai mallakan dukan kadarorin.
2 A maimakon haka, yana karkashin masu jagora da amintattu har sai lokacin da mahaifinsa ya ajiye.
3 Hakannan mu ma, lokaci da muke yara, an rike mu cikin kangi na tushin ka'idojin wannan duniya.
4 Amma da lokacin ya yi daidai, Allah ya aiko da dansa, haihuwar mace, haihuwar karkashin shari'a.
5 Ya yi haka ne domin ya fanshi wadanda ke a karkashin shari'a, domin mu karbi diyanci a matsayin 'ya'ya.
6 Domin ku 'ya'ya ne, Allah ya aiko da Ruhun Dansa cikin zuciyarmu, Ruhun wanda ke kirar, “Abba, Uba.”
7 Saboda wannan dalilin kai ba kuma bawa ba ne amma da. Idan kai da ne, hakannan kuma kai ma magaji ne ta wurin Allah.
8 Duk da haka a da, da ba ku san Allah ba, bayi ne ku ga alloli wadanda ainihi ba alloli ba ne ko kadan.
9 Amma yanzu da kuka san Allah, ko kuma, yanzu da Allah ya san ku, me ya sa kuke sake komawa zuwa ga tushen ka'idodin nan mara karfi da amfani? Kuna so ku sake komawa zaman bayi kuma daga farko?
10 Kuna kiyaye ranaku na musamman, sabobin watanni, lokatai, da shekaru.
11 Ina ji maku tsoro. Ina tsoro cewa kamar na yi aiki cikinku a wofi.
12 Ina rokon ku 'yan'uwa, ku zama kamar yadda nake, domin ni ma na zama kamar ku. Ba ku yi mani laifin komai ba.
13 Amma kun sani cewa saboda rashin lafiya ne na yi maku shelar bishara da farko.
14 Ko da yake halin da nake ciki cikin jiki a zahiri ya sa ku cikin gwaji, ba ku raina ni ba ko kuma kuka watsar da ni. A maimakon haka, kun karbe ni kamar mala'ikan Allah, kamar ni Almasihu Yesu ne da kansa.
15 Saboda haka, yanzu ina murnar taku? Domin ina shaidar ku, idan mai yiwuwa ne, da kun kwakulo idanunku, kun ba ni.
16 To kenan, na zama makiyin ku ne saboda na gaya maku gaskiya?
17 Suna neman ku da himma ba domin wani alheri ba ne. Suna so su raba ni da ku domin ku bi su.
18 Yana da kyau ko yaushe a yi himma domin dalilai masu kyau, ba kuma kawai sa'adda ina tare da ku ba.
19 'Ya'yana kanana, sabili da ku ina cikin zafin nakuda kuma sai Almasihu ya samu kafuwa cikinku.
20 Da ma a ce ina tare da ku yanzu in canza muryata, domin ina damuwa a kanku kwarai.
21 Ku gaya mani, ku da kuke marmarin ku zo karkashin shari'a, ba ku ji abin da shari'ar ta ce ba?
22 A rubuce yake cewa, Ibrahim yana da 'ya'ya maza biyu, daya dan baiwa ne, dayan kuma dan 'yantaciyar mace ne.
23 Abin lura anan, dan baiwar an haife shi ta hanyar mutuntaka ne, amma dan 'yantaciyar macen, an haife shi ta wurin alkawari ne.
24 Ana iya bayyana abubuwan nan a hanyar kwatanci kamar haka, wadannan mata na kama da alkawarai ne guda biyu. Dayan alkawarin daga dutsen Sinayi ne. Ta haifi 'ya'ya da ke bayi ne su. Ita ce Hajaratu.
25 Yanzu fa, Hajaratu ita ce dutsen Sinayi da ke Arebiya. Misali ce na Urushalima na yanzu, domin tana cikin bauta tare da 'ya'yanta.
26 Amma Urushalima da ke bisa 'yantacciya ce, ita ce mahaifiyarmu.
27 Kamar yadda yake a rubuce, “Ki yi murna, ke bakarariya, ke da ba ki taba haihuwa ba. Ki yi shewa na farinciki, ke da ba ki dandana haihuwan da ba. Domin 'ya'yan bakarariya da yawa suke, fiye da ta mace mai miji.”
28 Yanzu fa, 'yan'uwa, kamar yadda Ishaku yake, haka muke, wato 'ya'yan alkawari.
29 A lokacin can, shi wanda aka haife shi ta hanyar mutuntaka ya tsananta wa wanda aka haife shi ta hanyar Ruhu. Haka yake har yanzu.
30 Amma menene nassi ya ce? “Ka kori baiwar nan tare da danta. Domin dan baiwar nan ba za ya ci gado tare da dan macen nan da ke 'yantacciya ba.”
31 Saboda haka 'yan'uwa, mu ba 'ya'yan baiwa ba ne, a maimakon haka, mu 'ya'yan macen nan ne da ke 'yantacciya.