< Galatiyawa 3 >
1 Ku Galatiyawa marasa wayo! Wanne mugun ido ya cuce ku? Ashe, ba Yesu Almasihu gicciyayye aka nuna a gaban idon ku ba?
O inconsiderate Galatians! who has deceived you, before whose eyes Jesus Christ crucified, was evidently represented among you?
2 Ina so in gane wannan daga wurin ku ne kawai. Kun karbi Ruhun ta wurin ayyukan doka ne ko ta wurin ba da gaskiya ga abin da kuka ji?
This, only, I wish to learn from you, did you receive the Spirit by works of law, or by obedience of faith?
3 Rashin wayonku ya yi yawa haka ne? Kun fara da Ruhu, sai kuma yanzu ku karasa a cikin jiki?
Are you so inconsiderate that, having begun in Spirit, you are now made perfect in flesh?
4 Kun fuskanci abubuwa da yawa a banza ne - har idan a banza ne?
Have you suffered so many things in vain? if, indeed, it is in vain?
5 To, shi wanda ya ba ku Ruhun, da ayyuka masu iko a tsakanin ku, ya yi ne ta wurin ayyukan shari'a ko ta wurin ji tare da bangaskiya?
He, then, who ministered to you the Spirit, and wrought miracles among you, did he these by works of law, or by a hearing of faith?
6 Ibrahim ''ya ba da gaskiya ga Allah, kuma an lisafta mashi wannan a matsayin adalci.''
even as Abraham believed God, and it was counted to him for righteousness;
7 Ta wannan hanya ku fahimta su wadanda suka ba da gaskiya, 'ya'yan Ibrahim ne.
know, therefore, that they who are of faith, the same are sons of Abraham.
8 Nassi ya riga ya hangi gaba cewa, ta wurin bangaskiya Allah zai baratar da Al'ummai. An yi wa Ibrahim shelar bishara tuntuni: ''A cikinka ne dukan al'ummai za su yi albarka.''
For the scripture, foreshowing that God would justify the nations by faith, formerly announced the gospel to Abraham, saying, "Surely in you shall all the nations be blessed."
9 Saboda haka, wadanda suka ba da gaskiya, masu albarka ne tare da Ibrahim wanda ke da bangaskiya.
Wherefore, they who are of faith are blessed with believing Abraham.
10 La'ana na kan wadanda sun dangana ga ayyukan shari'a. Gama a rubuce yake, ''La'ananne ne kowanne mutum da bai tsaya ga duk abin da ke a rubuce cikin littafin shari'a ba, ya kuma aikata shi duka.”'
But as many as are of works of law, are under the curse: for it is written, "Accursed is every one who continues not in all things which are written in the book of the law, to do them."
11 Yanzu a sarari yake, Allah ba ya baratar da kowa ta wurin shari'a, domin ''Mai adalci zai rayu ta bangaskiya.''
Besides, that by law no one is justified before God is manifest: "For the just by faith shall live."
12 Doka ba daga bangaskiya take ba, 'Amma a maimakon haka, “Shi wanda ke yin wadannan abubuwa cikin shari'a, zai yi rayuwa ta wurin shari'a.''
Now, the law is not of faith; but he who does these things, shall live by them.
13 Almasihu ya fanshe mu daga la'anar shari'a da ya zama la'ananne saboda mu. Kamar yadda yake a rubuce, ''La'ananne ne duk wanda aka sargafe a bisa itace.''
Christ has bought us off from the curse of the law, having become a curse for us: (for it is written, "Accursed is every one who is hanged on a tree": )
14 Dalilin shine, albarkan da ke bisan Ibrahim ta zo ga al'ummai cikin Almasihu Yesu, domin mu samu karban alkawarin Ruhu ta wurin bangaskiya.
that the blessing of Abraham might come on the nations through Christ Jesus; and that we might receive the promise of the Spirit through faith.
15 'Yan'uwa, ina magana bisa ga ka'idojin mutane. Idan mutane sun yi yarjejeniya, babu mai kawar da shi ko a kara shi.
Brethren, I speak after the manner of men: no one sets aside, or alters a man's Will, after it is ratified.
16 Yanzu fa, an fada alkawaran nan ne ga Ibrahim da zuriyarsa. Bai ce, ''ga zuriya ba'' da manufar masu yawa; amma a maimakon haka ga daya kadai, ''ga zuriyar ka,'' wanda shine Almasihu.
Now, to Abraham were the promises spoken, and to his seed. He does not say, "And in seeds," as concerning many; but as concerning one person, "And in your see," who is Christ.
17 Yanzu na fadi wannan. Shari'a, wadda ta zo shekaru 430 daga baya, ba ta kawar da alkawarin da Allah ya tabbatar da shi ba tun a baya.
Wherefore, this I affirm, that the Will which was before ratified by God concerning Christ, the law, which was made four hundred and thirty years after can not annul, so as to abolish the promise.
18 Domin idan da gadon ya zo ta dalilin shari'a ne, da ba za ya zo kuma ta dalilin alkawari ba. Amma Allah ya ba da shi ga Ibrahim kyauta ta wurin alkawari.
Besides, if the inheritance be by law, it is no longer by promise. But God bestowed it freely on Abraham by promise.
19 Me ya sa kenan aka ba da shari'a? An kara ta ne saboda laifuffuka, har sai zuriyar Ibrahim din nan ta zo ga wadanda aka yi masu alkawarinta. An kaddamar da ikon shari'ar ta wurin mala'iku, ta hannun matsakaici.
Why, then, the law? It was added on account of transgression, till the seed should come to whom it was promised; being ordained by messengers, in the hand of a Mediator;
20 Yanzu dai matsakanci yana nufin mutum fiye da daya, duk da haka Allah daya ne.
and the Mediator is not one party; but God is one party.
21 Shari'a tana tsayayya da alkawaran Allah kenan? Ko kadan! Domin idan da an ba da shari'a da ke iya bayar da rai, babu shakka da adalci ya zo ta wurin wannan shari'a.
Is the law, then, contrary to the promise of God? By no means. For if there had been a law given, which was able to make alive, certainly righteousness would have been by law.
22 A maimakon haka, nassi ya kulle abubuwa duka a karkashin zunubi. Allah ya yi wannan domin alkawarin sa na ceton mu ta wurin bangaskiya cikin Yesu Almasihu ya samu a ba da shi ga wadanda suka gaskanta.
But the scripture has shut up together all under sin, that the promise by faith of Jesus Christ might be given to them that believe.
23 Amma kafin bangaskiya cikin Almasihu ta zo, an kulle mu kuma aka tsare mu da shari'a har zuwa ga wahayin bangaskiya.
Wherefore, before faith came, we were kept in durance under law, shut up together to the faith, which should afterward be revealed.
24 Daga nan shari'a ta zama mana jagora har sai da Almasihu ya zo, domin mu samu baratarwa ta wurin bangaskiya.
So that the law has become our instructor to Christ, that we might be justified by faith.
25 Yanzu da bangaskiya ta zo, ba mu kuma a karkashin jagora.
But faith being come, we are no longer under this instructor.
26 Domin dukanku 'ya'yan Allah ne ta wurin bangaskiya cikin Almasihu Yesu.
For you are all the sons of God through the faith by Christ Jesus.
27 Dukanku da aka yi wa baftisma cikin Almasihu, kun suturce kanku da Almasihu.
Besides, as many of you have been immersed into Christ, have put on Christ.
28 Babu Bayahude ko Baheline, bawa ko 'yantacce, babu na miji ko mace, domin dukanku daya ne cikin Almasihu Yesu.
There is neither Jew nor Greek, there is neither bondman nor freeman, there is neither male nor female; for you are all one in Christ Jesus.
29 Idan ku na Almasihu ne, ku zuriyar Ibrahim ne kenan, magada bisa ga alkawarin.
And if you are Christ's, certainly you are Abraham's seed, and heirs according to the promise.