< Galatiyawa 2 >
1 Daga nan, bayan shekara goma sha hudu na koma Urushalima tare da Barnaba. Na kuma dauki Titus tare da ni.
2 Na koma ne domin Allah ya nuna mani in koma. Sai na gabatar masu shelar bisharan da nake yi a cikin al'ummai. (Amma a kebe na yi magana da wadanda aka dauka muhimman shugabanni). Na yi haka ne domin in tabbatar da cewa ba gudun banza nake yi ba, ko kuma na yi gudun banza.
3 Amma ko Titus wanda yake tare da ni, Baheline, ba wanda ya tilasta masa ya yi kaciya.
4 Wannan maganar ta taso ne daga 'yan'uwan karya da suka zo cikinmu a boye su ga 'yancin mu a cikin Yesu Almsihu. Sun yi marmarin su maishe mu bayi ga doka.
5 Ba mu mika kanmu biyayya gare su ba ko da na sa'a daya, domin gaskiyar bishara ta kasance babu canzawa domin ku.
6 Amma su wadanda a ke ganin su da muhimmanci ba su taimaka mani da komai ba. Ko su wanene su bai dame ni ba. Allah ba ya karbar wanda mutane suka fi so.
7 Maimakon haka, suka ga an danka mani shelar bishara ga wadanda ba su da kaciya. Kamar yadda aka ba Bitrus shelar bishara ga masu kaciya.
8 Gama Allah wanda yake yin aiki a cikin Bitrus domin manzanci zuwa ga masu kaciya, haka kuma yake aiki ciki na zuwa ga al'ummai.
9 Da Yakubu, Kefas, da Yahaya, wadanda a ke gani masu gina ikilisiya, suka fahimci alherin da aka ba ni, suka bamu hannun dama na zumunci ni da Barnaba, Sun yi haka ne kawai domin mu mu tafi zuwa wurin al'ummai, su kuma su je wurin masu kaciya.
10 Suna kuma so mu tuna da matalauta. Ni ma ina da aniyar yin haka.
11 Da Kefas ya kai Antakiya, na yi tsayayya da shi a gabansa domin shine ke da kuskure.
12 Da ma Kefas yana cin abinci tare da al'ummai kafin zuwan wasu mutane daga wurin Yakubu. Amma da wadannan mutane suka iso, sai ya dena kuma ya ware kansa daga al'umman. Yana jin tsoron wadannan mutanen da ke bukatar kaciya.
13 Hakannan ma sauran Yahudawa da suke tare da shi sun bi munafurcin sa. A sakamakon haka Barnaba ma ya bi munafurcin su.
14 Da na ga basu bin gaskiyar da take cikin bisharar, na gaya wa Kefas a gaban su duka, “Idan kai Bayahude ne kana rayuwar ka ta al'ummai a maimakon rayuwar Yahudawa, to ta yaya za ka tilasta wa al'ummai su yi zaman Yahudawa? “
15 Mu da muke Yahudawa daga haihuwa, ba ''Al'ummai masu zunubi ba.''
16 Ku sani fa, babu wanda za a baratar ta ayyukan shari'a. A maimakon haka an baratar da su ta wurin bangaskiya cikin Yesu Almasihu. Mun zo ga cikin Almasihu Yesu domin mu samu baratarwa ta bangaskiya cikin Almasihu, kuma ba ta ayyukan shari'a ba. Domin ta ayyukan shari'a babu wanda zai samu baratarwa.
17 Amma idan mun nemi Allah ya baratar da mu cikin Almasihu, mun samu kanmu masu zunubi kenan, Almasihu ya zama bawan zunubi ne? Ko kadan!
18 Idan na sake gina dogara ta a kan shari'a, dogarar da na juya wa baya, na nuna kai na mai karya shari'a kenan.
19 Ta wurin shari'a na mutu ga shari'a, domin in yi rayuwa irin ta Allah.
20 An giciye ni tare da Almasihu, ba nine ke rayuwa ba kuma, amma Almasihu ke rayuwa a cikina. Rayuwar da nake yi a yanzu a cikin jiki, ina yin ta ne, ta wurin bangaskiya ga dan Allah, wanda ya kaunace ni ya ba da kansa domina.
21 Ban yi watsi da alherin Allah ba, domin idan adalci ya wanzu ta wurin shari'a, ashe Almasihu ya mutu a banza kenan.