< Afisawa 5 >

1 Saboda haka ku zama masu koyi da Allah, kamar kaunatattun 'ya'yansa.
Buďtež tedy následovníci Boží, jakožto synové milí.
2 Ku yi zama cikin kauna kamar yadda Almasihu ya kaunace mu, ya kuma mika kansa sadaka da hadaya ga Allah dominmu, hadaya mai kanshi abin karba ga Allah.
A choďtež v lásce, jakož i Kristus miloval nás, a vydal sebe samého za nás, dar a obět Bohu u vůni rozkošnou.
3 Fasikanci ko kowacce irin kazamta, ko kazamar lalata kada a ambace su a tsakaninku, don haka ya dace ga masu bi.
Smilstvo pak a všeliká nečistota, neb lakomství, aniž jmenováno buď mezi vámi, jakož sluší na svaté,
4 Kada a ambaci batsa, maganar wauta ko alfasha wadanda ba su dace ba. Maimakon haka, mu zama masu godiya.
A tolikéž mrzkost, ani bláznové mluvení, ani šprýmování, kteréžto věci jsou nenáležité, ale raději ať jest díků činění.
5 Domin wannan kun sani cewa ba fasiki, ko mara tsarki, ko mai hadama wato mai bautar gumaka zai sami gado cikin mulkin Almasihu da Allah.
Víte zajisté o tom, že žádný smilník aneb nečistý, ani lakomec, (jenž jest modloslužebník, ) nemá dědictví v království Kristově a Božím.
6 Kada kowa ya rude ku da maganganun wofi. Saboda wadannan abubuwa ne fushin Allah ke zuwa kan kangararrun 'ya'ya.
Žádný vás nesvoď marnými řečmi; nebo pro takové věci přichází hněv Boží na syny nepoddané.
7 Kada ku yi tarayya tare da su.
Nebývejtež tedy účastníci jejich.
8 Domin da ku duhu ne, amma yanzu ku haske ne cikin Ubangiji. Sai ku yi tafiya kamar 'ya'yan haske.
Byli jste zajisté někdy temnosti, ale již nyní jste světlo v Pánu. Jakožto synové světla choďte,
9 Saboda amfanin haske shine dukan alheri, adalci da gaskiya.
(Nebo ovoce Ducha záleží ve vší dobrotě, a spravedlnosti, a v pravdě, )
10 Kuna bidar abin da Ubangiji ke murna da shi.
O to stojíce, což by se dobře líbilo Pánu.
11 Kada ku sa hannu ga ayyuka marasa amfani da ayyukan duhu amma gara a tone su.
A neobcujte s skutky neužitečnými tmy, ale raději je trescete.
12 Don abubuwan da suke yi a boye abin kunya ne a bayyana su.
Nebo což se tajně děje od nich, mrzko jest o tom i mluviti.
13 Dukan abu, idan haske ya bayyana su, za a gan su.
Všecko pak, což bývá trestáno, od světla bývá zjeveno; nebo to, což všecko zjevuje, světlo jest.
14 Domin duk abin da aka bayyana ya zama haske. Saboda haka aka ce, “Ka farka, kai mai barci, ka tashi daga cikin matattu; Almasihu kuwa zai haskaka bisanka”.
Protož praví: Probuď se ty, jenž spíš, a vstaň z mrtvých, a zasvítíť se tobě Kristus.
15 Saboda haka, ku maida hankali yadda kuke rayuwar ku, ba kamar mutane marasa hikima ba amma kamar masu hikima.
Viztež tedy, kterak byste opatrně chodili, ne jako nemoudří, ale jako moudří,
16 Ku yi lura yadda kuke amfani da lokaci don kwanakin miyagu ne.
Vykupujíce čas; nebo dnové zlí jsou.
17 Kada ku zama wawaye. Maimakon haka, ku fahimci ko menene nufin Ubangiji.
Protož nebývejte neopatrní, ale rozumějící, která by byla vůle Páně.
18 Kuma Kada ku bugu da ruwan inabi, don yana iya lalata rayuwa. Maimakon haka, ku cika da Ruhu Mai Tsarki.
A neopíjejte se vínem, v němžto jest prostopášnost, ale naplněni buďte Duchem svatým,
19 Kuna magana da junanku cikin zabura da wakoki da wakokin ruhaniya, kuna rairawa da yabo da zuciyarku ga Ubangiji.
Mluvíce sobě vespolek v žalmích, a v chvalách, a v písničkách duchovních, zpívajíce a plésajíce v srdcích vašich Pánu,
20 Kullum kuna ba da gaskiya domin dukan abubuwa cikin sunan Ubangiji Yesu ga Allah Uba.
Díky činíce vždycky ze všeho ve jménu Pána našeho Jezukrista Bohu a Otci,
21 Kuna sarayadda kanku ga juna cikin girmama Almasihu.
Poddáni jsouce jedni druhým v bázni Boží.
22 Mata, ku yi biyayya ga mazan ku kamar ga Ubangiji.
Ženy mužům svým poddány buďte jako Pánu.
23 Domin miji shine shugaban matarsa kamar yadda Almasihu yake shugaban ikilisiya. Shine kuma mai ceton jiki.
Nebo muž jest hlava ženy, jako i Kristus jest hlava církve, a onť jest Spasitel těla.
24 Amma kamar yadda ikilisiya take biyayya ga Almasihu, haka kuma dole mata suyi ga mazajen su cikin kowanne abu.
A tak jakož církev poddána jest Kristu, tak i ženy mužům svým ať jsou poddány ve všem.
25 Mazaje, ku kaunaci matanku kamar yadda Almasihu ya kaunaci ikilisiya har ya ba da kansa dominta,
Muži milujte ženy své, jako i Kristus miloval církev, a vydal sebe samého za ni,
26 Ya yi wannan domin ya tsarkake ta. Ya wanke mu da ruwan wanki ta wurin kalma.
Aby ji posvětil, očistiv ji obmytím vody v slovu,
27 Ya yi wannan domin ya mika ma kansa ikilisiya mai daraja, ba tare da tabo ko cikas ko wani abu kamar wadannan, amma ta zama da tsarki da kuma mara aibi.
Aby ji sobě postavil slavnou církev, nemající poskvrny, ani vrásky, neb cokoli takového, ale aby byla svatá a bez úhony.
28 Hakannan kuma, mazaje su kaunaci matansu kamar jikunnansu. Wanda yake kaunar matarsa yana kaunar kansa.
Takť jsou povinni muži milovati ženy své jako svá vlastní těla. Kdo miluje ženu svou, sebeť samého miluje.
29 Ba wanda ya taba kin jikinsa. Amma, yakan ciyadda shi yana kaunarsa, kamar yadda Almasihu ya kaunaci ikilisiya.
Žádný zajisté nikdy těla svého neměl v nenávisti, ale krmí a chová je, jakožto i Pán církev.
30 Domin mu gabobin jikinsa ne.
Neboť jsme údové těla jeho, z masa jeho a z kostí jeho.
31 “Domin wannan mutum zai rabu da ubansa da uwarsa ya manne wa matarsa, su biyu su zama nama daya”.
A protoť opustí člověk otce i matku, a připojí se k manželce své, i budouť dva jedno tělo.
32 Wannan asirin gaskiyar, da girma yake, amma ina magana ne game da Almasihu da ikilisiyarsa.
Tajemství toto veliké jest, ale já pravím o Kristu a o církvi.
33 Duk da haka, kowannenku dole ya kaunaci matarsa kamar kansa, matar kuma dole ta girmama mijinta.
Avšak i vy, jeden každý z vás, manželku svou tak jako sám sebe miluj. Žena pak ať se bojí muže svého.

< Afisawa 5 >