< Afisawa 2 >

1 Amma da ku matattu ne cikin zunubanku da laifofinku.
And whanne ye weren deed in youre giltis and synnes,
2 A cikinsu kuka yi rayuwa bisa ga al'amuran duniyan nan. Kuka biye wa mai sarautar ikokin sararin sama, wannan ruhun ne da ke aiki cikin kangararrun 'ya'ya. (aiōn g165)
in which ye wandriden sum tyme aftir the cours of this world, aftir the prince of the power of this eir, of the spirit that worchith now in to the sones of vnbileue; (aiōn g165)
3 Da can dukanmu muna cikin wadannan marasa bada gaskiya. Muka biye wa mugun burin jikinmu. Muna aikata halin mutuntaka da na tunaninmu. Bisa ga dabi'a 'ya'ya ne wadanda sun cancanci fushin Allah, kamar wadansu.
in which also we `alle lyueden sum tyme in the desiris of oure fleisch, doynge the willis of the fleisch and of thouytis, and we weren bi kynde the sones of wraththe, as othere men;
4 Amma Allah mai yalwar jinkai ne, sabili da matukar kauna da ya kaunace mu.
but God, that is riche in merci, for his ful myche charite in which he louyde vs,
5 Sa'anda muke matattu cikin zunubai, ya kawo mu cikin sabon rai tare da Almasihu. Ta wurin alheri aka cece mu.
yhe, whanne we weren deed in synnes, quikenede vs togidere in Crist, bi whos grace ye ben sauyd, and ayen reiside togidere,
6 Allah ya tashe mu tare ya kuma sa muka zauna tare a matsayi guda cikin Almasihu Yesu.
and made togidere to sitte in heuenli thingis in Crist Jhesu;
7 Ya yi wannan domin a zamanai masu zuwa ya nuna mana matukar yalwar arzikin alherinsa ta wurin Yesu. Yana nuna mana wannan ta wurin alherinsa. (aiōn g165)
that he schulde schewe in the worldis aboue comynge the plenteuouse ritchessis of his grace in goodnesse on vs in Crist Jhesu. (aiōn g165)
8 Domin ta wurin alheri aka cece ku ta wurin bangaskiya, wannan ba daga gare ku ba ne, kyauta ce ta Allah.
For bi grace ye ben sauyd bi feith, and this not of you; for it is the yifte of God,
9 Ba daga ayyuka ba, Saboda wannan dalili kada kowa ya yi fahariya.
not of werkis, that no man haue glorie.
10 Gama mu aikin hannuwansa ne, halitattu cikin Almasihu Yesu domin mu yi kyawawan ayyuka, wadanda tun da Allah ya tanada, mu yi rayuwa a cikinsu.
For we ben the makyng of hym, maad of nouyt in Crist Jhesu, in good werkis, whiche God hath ordeyned, that we go in tho werkis.
11 Saboda haka ku tuna da ku al'ummai ne a dabi'ar jiki. Ana kiranku “marasa kaciya”, abin da ake kira kaciya cikin jiki wadda hannayen mutane ke yi.
For which thing be ye myndeful, that sumtyme ye weren hethene in fleisch, which weren seid prepucie, fro that that is seid circumcisioun maad bi hond in fleisch;
12 Gama a lokacin nan a rabe kuke da Almasihu. Ku bare ne ga mutanen Isra'ila. Ku baki ne ga wa'adodi na al'kawarai. Ba ku da tabbaci a kan gobe. Ba ku da Allah a cikin duniya.
and ye weren in that time with out Crist, alienyd fro the lyuyng of Israel, and gestis of testamentis, not hauynge hope of biheest, and with outen God in this world.
13 Amma yanzu a cikin Almasihu Yesu ku da da kuke nesa da Allah, an kawo ku kusa da shi ta wurin jinin Almasihu.
But now in Crist Jhesu ye that weren sum tyme fer, ben maad nyy in the blood of Crist.
14 Gama shine salamar mu. Domin ya mai da biyun daya. Cikin jikinsa ne ya rushe katangar gaba da ta raba mu da juna.
For he is oure pees, that made bothe oon, and vnbyndynge the myddil wal of a wal with out morter, enmytees in his fleisch;
15 Wato ya kawar da shari'a mai umarnai da sharudda, domin ya halitta sabon mutum daya a cikinsa. Yin haka ya kawo salama.
and auoidide the lawe of maundementis bi domes, that he make twei in hym silf in to a newe man,
16 Ya yi haka domin ya sulhunta mutum biyu cikin jiki daya ga Allah ta wurin gicciye. Ta wurin gicciye ya kashe gabar da ke tsakaninsu.
makynge pees, to recounsele bothe in o bodi to God bi the cros, sleynge the enemytees in hym silf.
17 Yesu ya zo ya yi maku shelar salama ku da kuke nesa da ku na kusa.
And he comynge prechide pees to you that weren fer, and pees to hem that weren niy;
18 Domin ta wurin Yesu dukanmu biyu cikin Ruhu daya muna da hanya zuwa wurin Uba.
for bi hym we bothe han niy comyng in o spirit to the fadir.
19 Sabo da haka yanzu ku al'ummai, ko daya, ba bare ba ne. Maimakon haka ku abokai ne tare da kebabbun Allah, abokan aiki.
Therfor now ye ben not gestis and straungeris, but ye ben citeseyns of seyntis, and houshold meine of God;
20 Wadanda an gina su bisa tushen manzanni da annabawa. Almasihu Yesu da kansa shine mafificin dutsen ginin.
aboue bildid on the foundement of apostlis and of profetis, vpon that hiyeste corner stoon, Crist Jhesu;
21 A cikinsa dukan ginin ya hade tare, suna kuma girma kamar haikali cikin Ubangiji.
in whom ech bildyng maad waxith in to an hooli temple in the Lord.
22 A cikinsa ne kuma ake gina ku gaba daya kun zama mazaunin Allah a cikin Ruhu.
In whom also `be ye bildid togidere in to the habitacle of God, in the Hooli Goost.

< Afisawa 2 >