< Kolossiyawa 3 >
1 Idan dai Allah ya tashe ku tare da Almasihu, ku nemi abubuwan da ke sama, inda Almasihu ke zaune a hannun dama na Allah.
Εἰ οὖν συνηγέρθητε τῷ Χριστῷ, τὰ ἄνω ζητεῖτε, οὗ ὁ Χριστός ἐστιν ἐν δεξιᾷ τοῦ θεοῦ καθήμενος·
2 Yi tunanin a kan abubuwan da ke sama, ba a kan abubuwan da ke kasa ba.
τὰ ἄνω φρονεῖτε, μὴ τὰ ἐπὶ τῆς γῆς,
3 Gama ku kun mutu, ranku kuma yana boye tare da Almasihu cikin Allah.
ἀπεθάνετε γάρ, καὶ ἡ ζωὴ ὑμῶν κέκρυπται σὺν τῷ Χριστῷ ἐν τῷ θεῷ·
4 Sa'anda Almasihu ya bayyana, wanda shine ranku, sa'anan ku kuma zaku bayyana tare da shi cikin daukakarsa.
ὅταν ὁ Χριστὸς φανερωθῇ, ἡ ζωὴ ⸀ὑμῶν τότε καὶ ὑμεῖς σὺν αὐτῷ φανερωθήσεσθε ἐν δόξῃ.
5 Ku kashe sha'awacce-sha'awaccen da suke a duniya - zina da fasikanci, rashin tsarki, muguwar sha'awa, mummunar buri, da kuma kwadayi, wadda shine bautar gumaka.
Νεκρώσατε οὖν τὰ ⸀μέλητὰ ἐπὶ τῆς γῆς, πορνείαν, ἀκαθαρσίαν, πάθος, ἐπιθυμίαν κακήν, καὶ τὴν πλεονεξίαν ἥτις ἐστὶν εἰδωλολατρία,
6 Saboda wandannan abubuwa ne fushin Allah ke zuwa a kan marasa biyayya.
διʼ ἃ ἔρχεται ἡ ὀργὴ τοῦ θεοῦ ⸂ἐπὶ τοὺς υἱοὺς τῆς ἀπειθείας·
7 A cikin wadannan abubuwa ne kuka yi rayuwa a da da kuke zauna a cikinsu.
ἐν οἷς καὶ ὑμεῖς περιεπατήσατέ ποτε ὅτε ἐζῆτε ἐν ⸀τούτοις
8 Amma yanzu dole ku kawar da wadannan - zafin rai, fushi, mugayen manufofi, zage-zage, da kazamar magana daga bakinku.
νυνὶ δὲ ἀπόθεσθε καὶ ὑμεῖς τὰ πάντα, ὀργήν, θυμόν, κακίαν, βλασφημίαν, αἰσχρολογίαν ἐκ τοῦ στόματος ὑμῶν·
9 Kada ku yi wa juna karya, domin kun tube tsohon mutumin da ayyukansa,
μὴ ψεύδεσθε εἰς ἀλλήλους· ἀπεκδυσάμενοι τὸν παλαιὸν ἄνθρωπον σὺν ταῖς πράξεσιν αὐτοῦ,
10 kun kuma yafa sabon mutum, wanda ake sabontawa cikin sani bisa ga surar wannan da ya hallice shi.
καὶ ἐνδυσάμενοι τὸν νέον τὸν ἀνακαινούμενον εἰς ἐπίγνωσιν κατʼ εἰκόνα τοῦ κτίσαντος αὐτόν,
11 A nan ne inda babu Baheline da Bayahude, mai kaciya da marar kaciya, bare, baubawa, ko Basikitiye, bawa ko yantacce, amma Almasihu shine duka, yana kuma cikin duka.
ὅπου οὐκ ἔνι Ἕλλην καὶ Ἰουδαῖος, περιτομὴ καὶ ἀκροβυστία, βάρβαρος, Σκύθης, δοῦλος, ἐλεύθερος, ἀλλὰ ⸀τὰπάντα καὶ ἐν πᾶσιν Χριστός.
12 A matsayin ku na zababbun Allah, masu tsarki da kaunatattu sai ku yafa jinkai, ayyukan kirki, saukin kai, kamewa da hakuri.
Ἐνδύσασθε οὖν ὡς ἐκλεκτοὶ τοῦ θεοῦ, ἅγιοι καὶ ἠγαπημένοι, σπλάγχνα οἰκτιρμοῦ, χρηστότητα, ταπεινοφροσύνην, πραΰτητα, μακροθυμίαν,
13 Yi hakuri da juna. Ku yi wa juna alheri. Idan wani na da damuwa da wani, ku gafarta kamar yadda Ubangiji ya gafarta maku.
ἀνεχόμενοι ἀλλήλων καὶ χαριζόμενοι ἑαυτοῖς ἐάν τις πρός τινα ἔχῃ μομφήν· καθὼς καὶ ὁ ⸀κύριοςἐχαρίσατο ὑμῖν οὕτως καὶ ὑμεῖς·
14 Fiye da wadanan abubuwa duka, ku kasance da kauna, wanda itace cikakkiyar kammalla.
ἐπὶ πᾶσιν δὲ τούτοις τὴν ἀγάπην, ⸀ὅἐστιν σύνδεσμος τῆς τελειότητος.
15 Bari salamar Almasihu ta mallaki zukatanku. Sabili da wannan salama ce aka kiraye ku cikin jiki daya. Ku yi godiya.
καὶ ἡ εἰρήνη τοῦ ⸀Χριστοῦβραβευέτω ἐν ταῖς καρδίαις ὑμῶν, εἰς ἣν καὶ ἐκλήθητε ἐν ἑνὶ σώματι· καὶ εὐχάριστοι γίνεσθε.
16 Ku bar maganar Almasihu ta zauna a cikinku a yalwace. Da dukan hikima, ku koyar, ku kuma gargadi juna da zabura, wakoki, da wakokin yabo na ruhaniya. Kuna rairawa tare da godiya cikin zukatanku ga Allah.
ὁ λόγος τοῦ Χριστοῦ ἐνοικείτω ἐν ὑμῖν πλουσίως ἐν πάσῃ σοφίᾳ· διδάσκοντες καὶ νουθετοῦντες ἑαυτοὺς ⸀ψαλμοῖς ⸀ὕμνοις ᾠδαῖς πνευματικαῖς ⸀ἐνχάριτι, ᾄδοντες ἐν ⸂ταῖς καρδίαις ὑμῶν τῷ ⸀θεῷ
17 Kuma duk abin da zaku yi cikin magana ko aiki ku yi duka cikin sunan Ubangiji Yesu. Kuna yin godiya ga Allah Uba ta wurinsa.
καὶ πᾶν ⸂ὅ τι ⸀ἐὰνποιῆτε ἐν λόγῳ ἢ ἐν ἔργῳ, πάντα ἐν ὀνόματι κυρίου Ἰησοῦ, εὐχαριστοῦντες τῷ ⸀θεῷπατρὶ διʼ αὐτοῦ.
18 Mata, ku yi biyayya ga mazajenku, yadda yakamata a cikin Ubangiji.
Αἱ γυναῖκες, ὑποτάσσεσθε ⸀τοῖςἀνδράσιν, ὡς ἀνῆκεν ἐν κυρίῳ.
19 Mazaje, ku kaunaci matayenku, kada ku muzguna masu.
οἱ ἄνδρες, ἀγαπᾶτε τὰς γυναῖκας καὶ μὴ πικραίνεσθε πρὸς αὐτάς.
20 Yaya, ku yi wa iyayen ku biyayya cikin dukan komai, domin wannan yana faranta wa Ubangiji rai.
Τὰ τέκνα, ὑπακούετε τοῖς γονεῦσιν κατὰ πάντα, τοῦτο γὰρ ⸂εὐάρεστόν ἐστιν ἐν κυρίῳ.
21 Ku Ubanni, kada ku cakuni 'ya'yanku domin kada su karaya.
οἱ πατέρες, μὴ ἐρεθίζετε τὰ τέκνα ὑμῶν, ἵνα μὴ ἀθυμῶσιν.
22 Bayi, ku yi wa iyayengijinku na jiki biyayya cikin kowane abu, ba tare da bautan ganin ido ba don faranta wa mutane rai, amma da sahihiyar zuciya. Ji tsoron Ubangiji.
οἱ δοῦλοι, ὑπακούετε κατὰ πάντα τοῖς κατὰ σάρκα κυρίοις, μὴ ἐν ⸀ὀφθαλμοδουλίαις ὡς ἀνθρωπάρεσκοι, ἀλλʼ ἐν ἁπλότητι καρδίας, φοβούμενοι τὸν ⸀κύριον
23 Duk abin da kuke yi, ku yi aiki daga zuci domin Ubangiji ba domin mutane ba.
⸀ὃἐὰν ποιῆτε, ἐκ ψυχῆς ἐργάζεσθε, ὡς τῷ κυρίῳ καὶ οὐκ ἀνθρώποις,
24 Kun san cewa, zaku karbi sakamako na gado daga wurin Ubangiji. Domin Ubangiji Almasihu kuke bauta wa.
εἰδότες ὅτι ἀπὸ κυρίου ⸀ἀπολήμψεσθετὴν ἀνταπόδοσιν τῆς κληρονομίας· ⸀τῷκυρίῳ Χριστῷ δουλεύετε·
25 Domin kowa ya yi rashin adalci zai karbi sakamakon rashin adalcin da ya yi, kuma babu son kai.
ὁ ⸀γὰρἀδικῶν κομίσεται ὃ ἠδίκησεν, καὶ οὐκ ἔστιν προσωπολημψία.