< Ayyukan Manzanni 9 >

1 Amma Shawulu, ya cigaba da maganganun tsoratarwa har ma da na kisa ga almajiran Ubangiji, ya tafi wurin babban firist
Saul pak ještě dychtě po pohrůžkách a po mordu proti učedlníkům Páně, šel k nejvyššímu knězi,
2 kuma ya roke shi wasiku zuwaga majami'un da ke Dimashku, domin idan ya sami wani da ke na wannan hanya, maza ko mata, ya kawo su Urushalima a daure.
A vyžádal od něho listy do Damašku do škol, nalezl-li by tam té cesty které muže nebo ženy, aby svázané přivedl do Jeruzaléma.
3 Yayin da yana tafiya, ya kasance da ya iso kusa da Dimashku, nan da nan sai ga wani haske daga sama ya haskaka kewaye da shi;
A když byl na cestě, stalo se, že již přibližoval se k Damašku. Tedy pojednou rychle obklíčilo jej světlo s nebe.
4 Sai ya fadi a kasa kuma yaji wata murya na ce da shi, ''Shawulu, Shawulu, me yasa kake tsananta mani?''
A padna na zem, uslyšel hlas řkoucí: Saule, Saule, proč mi se protivíš?
5 Shawulu ya amsa, ''Wanene kai, Ubangiji?'' Ubangiji ya ce, ''Nine Yesu wanda kake tsanantawa;
A on řekl: I kdo jsi, Pane? A Pán řekl: Já jsem Ježíš, jemuž ty se protivíš. Tvrdoť jest tobě proti ostnům se zpěčovati.
6 amma ka tashi, ka shiga cikin birnin, kuma za a gaya maka abinda lallai ne kayi.
A on třesa se a boje se, řekl: Pane, co chceš, abych činil? A Pán k němu: Vstaň a jdi do města, a bude tobě povědíno, co bys ty měl činiti.
7 Mutanen da ke tafiya tare da Shawulu suka tsaya shiru sun rasa abin fada, suna sauraron muryar, amma ba su ga kowa ba.
Ti pak muži, kteříž šli za ním, stáli, ohromeni jsouce, hlas zajisté slyšíce, ale žádného nevidouce.
8 Shawulu ya tashi daga kasa, kuma daga ya bude idanunsa, baya ganin komai; sai suka kama hannuwansa suka yi masa jagora suka kawo shi cikin birnin Dimashku.
I vstal Saul z země, a otevřev oči své, nic neviděl. Tedy pojavše ho za ruce, uvedli jej do Damašku.
9 Har kwana uku ba ya kallo, kuma ba ya ci balle sha.
I byl tu za tři dni nevida, a nejedl nic, ani nepil.
10 Akwai wani almajiri a Dimashku mai suna Hananiya; sai Ubangiji ya yi magana da shi cikin wahayi, ya ce, ''Hananiya.'' Sai ya ce, ''Duba, gani nan Ubangiji.''
Byl pak jeden učedlník apoštolský v Damašku, jménem Ananiáš. I řekl k němu Pán u vidění: Ananiáši. A on řekl: Aj, já, Pane.
11 Ubangiji ya ce masa, ''Tashi, ka tafi titin da ake kira Mikakke, kuma a gidan wani mai suna Yahuza ka tambaya mutum daga Tarsus mai suna Shawulu; gama yana addu'a;
A Pán k němu: Vstaň a jdi do ulice, kteráž slove Přímá, a hledej v domě Judově Saule, jménem Tarsenského. Nebo aj, modlí se,
12 kuma ya gani cikin wahayi mutum mai suna Hananiya na shigowa kuma ya daura masa hannu, domin idanunsa su bude.''
A viděl u vidění muže, Ananiáše jménem, an jde k němu, a vzkládá naň ruku, aby zrak přijal.
13 Amma Hananiya ya amsa, ''Ubangiji, na ji labari daga wurin mutane da yawa game da mutumin nan, da irin muguntar da ya aikata ga tsarkakan mutanenka da ke Urushalima.
I odpověděl Ananiáš: Pane, slyšel jsem od mnohých o tom muži, kterak mnoho zlého činil svatým tvým v Jeruzalémě.
14 An bashi izini daga babban firist domin ya kama dukan wanda ke kira bisa sunanka.''
A i zdeť má moc od předních kněží, aby jímal všecky, kteříž vzývají jméno tvé.
15 Amma Ubangiji ya ce masa, ''Jeka, gama shi zababben kayan aiki na ne, wanda zai yada sunana ga al'ummai da sarakuna da 'ya'yan Isra'ila;
I řekl jemu Pán: Jdi, neboť on jest má nádoba vyvolená, aby nosil jméno mé před pohany i krále, i před syny Izraelské.
16 Domin zan nuna masa irin wahalar da zai sha sabo da sunana.''
Jáť zajisté ukáži jemu, kterak on mnoho musí trpěti pro jméno mé.
17 Sai Hananiya ya tafi, ya shiga gidan. Ya dora masa hannu a kai, ya ce, ''Dan'uwa Shawulu, Ubangiji Yesu, wanda ya bayyana a gareka a hanya sa'adda kake zuwa, ya aiko ni domin ka sami ganin gari ka kuma cika da Ruhu Mai Tsarki.''
I šel Ananiáš, a všel do toho domu, a vloživ ruce naň, řekl: Saule bratře, Pán Ježíš poslal mne, kterýž se ukázal tobě na cestě, po níž jsi šel, abys zrak přijal a naplněn byl Duchem svatým.
18 Nan take wani abu kamar bawo ya fado daga idanun Shawulu, kuma ya sami ganin gari; ya tashi aka yi masa baftisma;
A hned spadly s očí jeho jako lupiny, a on prohlédl pojednou; a vstav, pokřtěn jest.
19 kuma ya ci abinci sai aka karfafa shi. Ya zauna tare da almajirai a Dimashku kwanaki da yawa.
A přijav pokrm, posilnil se. I zůstal Saul s učedlníky, kteříž byli v Damašku, za několiko dní.
20 Nan take ya fara shellar Yesu cikin haikali, yana cewa shine dan Allah.
A hned v školách kázal Krista, pravě, že on jest Syn Boží.
21 Dukan wadanda suka saurare shi suka yi mamaki suka ce ''Ba wannan mutumin ne yake hallaka mutanen Urushalima da ke kira bisa ga wannan suna ba? Ya kuma zo nan domin ya ba da su a daure ga manyan firistoci.''
I divili se náramně všickni, kteříž jej slyšeli, a pravili: Zdaliž toto není ten, jenž hubil v Jeruzalémě ty, kteříž vzývali jméno toto, a sem na to přišel, aby je svázané vedl k předním kněžím?
22 Amma Shawulu kuwa ya sami iko sosai, kuma yana haddasa damuwa tare da rinjaya tsakanin Yahudawan dake zama a Dimashku ta wurin tabbatar da Yesu shine Almasihu.
Saul pak mnohem více se zmocňoval a zahanboval Židy, kteříž byli v Damašku, potvrzuje toho, že ten jest Kristus.
23 Bayan kwanaki da yawa, sai Yahudawan suka yi shiri domin su kashe shi.
A když přeběhlo drahně dnů, radu mezi sebou na tom zavřeli Židé, aby jej zabili.
24 Amma shirin su ya zama sananne ga Shawulu. Suna fakkon sa ta wurin tsaron kofar birnin dare da rana domin su kashe shi.
Ale zvěděl Saul o těch úkladech jejich. Ostříhali také i bran ve dne i v noci, aby jej zahubili.
25 Amma da tsakar dare almajiransa suka daukeshi a kwando, suka zurara shi ta katanga.
Ale učedlníci v noci vzavše ho, spustili jej po provaze přes zed v koši.
26 Sa'adda ya zo Urushalima, Shawulu ya yi niyyar hada kai da almajirai, amma dukansu suna tsoronsa, domin ba su yarda cewa shima ya zama almajiri ba.
Přišed pak Saul do Jeruzaléma, pokoušel se přitovaryšiti k učedlníkům, ale báli se ho všickni, nevěříce, by byl učedlníkem.
27 Amma Barnaba ya dauke shi ya kawo shi wurin manzannin. Ya kuwa gaya musu yadda Shawulu ya sadu da Ubangiji a hanya, har Ubangiji ya yi magana da shi, kuma yadda Shawulu ya yi wa'azi cikin sunan Yesu gabagadi a Dimashku.
Barnabáš pak přijav jej, vedl ho k apoštolům, a vypravoval jim, kterak na cestě viděl Pána, a že mluvil s ním, a kterak v Damašku svobodně mluvil ve jménu Ježíše.
28 Ya sadu da su lokacin shigar su da fitar su a Urushalima. Ya yi wa'azi gabagadi cikin sunan Ubangiji Yesu
I byl s nimi přebývaje v Jeruzalémě,
29 kuma yana muhawara da Yahudawan Helenanci; amma sun ci gaba da kokarin kashe shi.
A směle mluvě ve jménu Pána Ježíše, a hádal se s Řeky; oni pak usilovali ho zabíti.
30 Da 'yan'uwa suka gane haka, sai suka kawo shi Kaisariya, suka kuwa tura shi zuwa Tarsus.
To zvěděvše bratří, dovedli ho do Cesaree, a poslali jej do Tarsu.
31 Sa'annan iklisiya dake dukan kasar Yahudiya, Galili da kuma Samariya suka sami salama da kuma ginuwa; suka kuwa ci gaba da tafiya cikin tsoron Ubangiji, da kuma ta'aziyar Ruhu Mai Tsarki, iklisiyar kuwa ta karu da yawan mutane.
A tak sborové po všem Judstvu a Galilei i Samaří měli pokoj, vzdělávajíce se, a chodíce v bázni Páně, a rozhojňovali se potěšením Ducha svatého.
32 Har ta kai, yayin da Bitrus ya zaga dukan yankin kasar, ya dawo wurin masu bi dake zama a garin Lidda.
Stalo se pak, že Petr, když procházel všecky sbory, přišel také k svatým, kteříž byli v Lyddě.
33 A can kuwa ya sami wani mutum mai suna Iniyasu, wanda yake shanyayye ne, yana kwance har tsawon shekara takwas a kan gado.
I nalezl tu člověka jednoho, jménem Eneáše, již od osmi let na loži ležícího, kterýž byl šlakem poražený.
34 Bitrus ya ce masa, ''Iniyasu, Yesu Almasihu ya warkar da kai. Tashi ka nade shimfidarka.'' Nan take sai ya mike.
I řekl mu Petr: Eneáši, uzdravujeť tebe Ježíš Kristus; vstaň a ustel sobě. A hned vstal.
35 Sai duk mazauna kasar Lidda da kasar Sarona suka ga mutumin, suka kuma juyo ga Ubangiji.
I viděli jej všickni, kteříž bydlili v Lyddě a v Sároně, kteříž se obrátili ku Pánu.
36 Yanzu kuwa a Yafa akwai wata almajira, mai suna Tabita, ma'ana ''Dokas.'' Wannan matar kuwa tana chike da ayyukan nagarta da halin tausayi da take yi ga mabukata.
Byla pak jedna učedlnice v Joppen, jménem Tabita, což se vykládá Dorkas. Ta byla plná skutků dobrých a almužen, kteréž činila.
37 Ya kai ga cewa a kwanakin can ta yi rashin lafiya har ta mutu; da suka wanke gawar ta suka kwantar da ita a bene.
I stalo se v těch dnech, že roznemohši se, umřela. Kteroužto umyvše, položili na síň vrchní.
38 Da shike Lidda na kusa da Yafa, almajiran kuma sun ji cewa Bitrus yana can, suka aika mutane biyu wurinsa. Suna rokansa, ''Ka zo garemu ba tare da jinkiri ba.''
A že byla blízko Lydda od Joppen, uslyšavše učedlníci, že by tam byl Petr, poslali k němu dva muže, prosíce ho, aby sobě neobtěžoval přijíti až k nim.
39 Bitrus ya tashi ya tafi da su, da isowar sa, suka kai shi benen. Sai dukan gwamrayen suka tsaya kusa da shi suna kuka, sai suka dauko riguna da sutura da Dokas ta dinka lokacin da take tare da su.
Tedy vstav Petr, šel s nimi. A když přišel, vedli jej na síň. I obstoupily ho všecky vdovy, plačíce a ukazujíce sukně a pláště, kteréž jim dělala, dokudž s nimi byla, Dorkas.
40 Bitrus ya fitar da su duka daga cikin dakin, ya durkusa, ya yi addu'a; sai, ya juya wurin gawar, ya ce, ''Tabita, tashi.'' Ta bude idanunta, da ta ga Bitrus ta zauna,
I rozkázav všechněm vyjíti ven Petr, poklek na kolena, modlil se, a obrátiv se k tomu tělu, řekl: Tabito, vstaň. A ona otevřela oči své, a uzřevši Petra, posadila se.
41 Bitrus kuwa ya mika hannunsa ya tashe ta; sa'annan ya kira masu bi da gwamrayen, ya mika ta a raye garesu.
A podav jí ruky Petr, pozdvihl jí; a povolav svatých a vdov, ukázal jim ji živou.
42 Wannan al'amari ya zama sananne cikin dukan Yafa, kuma mutane da yawa suka bada gaskiya ga Ubangiji.
I rozhlášeno jest to po všem městě Joppen, a uvěřili mnozí v Pána.
43 Ya kasance, cewa, Bitrus ya zauna kwanaki da dama a Yafa tare da wani mutum mai suna Saminu, majemi.
I stalo se, že za mnohé dni pozůstal Petr v Joppen u nějakého Šimona koželuha.

< Ayyukan Manzanni 9 >