< Ayyukan Manzanni 7 >
1 Sai babban firist ya ce, ''Wadannan al'amura gaskiya ne?''
2 Sai Istifanus ya amsa ya ce, ''Ya 'yan'uwa da ubanni, ku saurare ni, Allah Madaukaki ya bayyana ga ubanmu Ibrahim tun yana can kasar Mesofotamiya, kafin ma ya zauna a kasar Haran;
3 ya ce masa, 'Ka bar kasarka da danginka, ka tafi kasar da zan nuna maka.'
4 Sa'annan ya bar kasar Kaldiyawa ya zo ya zauna a Haran; daga can, bayan rasuwar mahaifinsa, sai Allah ya kira shi zuwa wannan kasa da kuke ciki.
5 Amma Allah bai ba shi kasar gado ba tukuna, ko da misalin tafin sawunsa. Amma ya alkawarta - ko da yake bai riga ya haifi da ba tukuna - wanda zai ba shi kasar gado, shi da zuriyarsa, a bayansa.
6 Allah ya yi magana da shi kamar haka, cewa zuriyarsa za su yi bakonci a wata kasa wadda ba tasu ba, mutanen wannan kasar kuwa za su gwada masu bakar azaba su kuma bautar da su har shekaru dari hudu.
7 'Kuma zan hukunta wannan al'umma da ta bautar da su,' Allah ya ce, 'Bayan haka za su fito daga wannan kasa su bauta mini a wannan wuri.'
8 Allah ya ba Ibrahim alkawarin kaciya, sai Ibrahim ya haifi Ishaku ya yi masa kaciya a rana ta takwas; Ishaku ya haifi Yakubu, Yakubu kuma ya haifi ubanni Isra'ila su goma sha biyu.
9 Wadannan 'yan'uwa suka yi kyashin danuwansu Yusifu suka sayar da shi bauta zuwa Masar. Amma Allah na tare da shi.
10 Ya kuwa cece shi daga dukan sharin da yan uwansa suka kulla masa, Allah kuwa ya ba shi tagomashi da hikima a gaban Fir'auna, sarkin Masar. Fir'auna kuwa ya mai da shi mai mulki a dukan kasar Masar da kuma dukan mallakarsa.
11 Sai aka yi babbar yunwa a dukan kasar Masar da ta Kan'ana, iyayenmu suka sha wuya saboda rashin abinci.
12 Amma lokacin da Yakubu ya ji akwai hatsi a kasar Masar, sai ya aiki ubannimu a karo na farko.
13 Da suka je a karo na biyu, sai Yusifu ya bayyana kansa ga yanuwansa; a wannan lokaci ne Fir'auna ya gane da yanuwan Yusufu.
14 Yusufu ya aiki yanuwansa su kawo Yakubu ubansu da dukan mallakarsu da iyalansu zuwa Masar, Dukansu mutane saba'in da biyar ne.
15 Yakubu ya tafi ya zauna a Masar; shi da zuriyarsa har mutuwar su.
16 Aka dauke su zuwa Shekem aka binne su a kabarin da Ibrahim ya saya da kudin azurfa daga hannun yayan Hamor a Shekem.
17 Yayin da alkawarin Allah ya kusato wanda Allah ya fada wa Ibrahim, mutanen suka karu suka hayayyafa kwarai a Masar,
18 Sai a ka yi wani sarki a Masar wanda bai san Yusifu ba,
19 Wannan sarki ya yaudari kakkaninmu ya yi masu mugunta kwarai da gaske, har ma ya kai ga suna barin jariransu cikin hasari don su ceci rayukansu.
20 A wannan lokaci ne aka haifi Musa, kuma kyakkyawan yaro ne sai aka yi renon sa tsawon wata uku a gidan mahaifinsa a asirce.
21 Yayin da aka jefar da shi, sai diyar Fir'auna ta dauke shi ta rene shi kamar danta.
22 Aka ilimantar da Musa da dukan ilimi irin na Masar; kuma ya shahara cikin fasahar magana da kuma ayyukansa.
23 Amma lokacin da yakai shekara arba'in, sai ya yi niyyar ya ziyarci 'yan'uwansa, Isra'ilawa.
24 Sai ya ga wani na cin zalin Ba Isra'ile, Musa kuwa ya taimaki wanda ake kwara ta wurin murkushe Bamasaren:
25 zaton Musa 'yan'uwansa za su fahimci taimakon Allah ne ya zo masu amma ina! Basu gane ba.
26 Washegari ya ga wasu Isra'ilawa na fada da junansu; ya yi kokari ya raba su; sai ya ce masu, 'Malamai, ku 'yan'uwan juna ne; don me kuke fada da junanku?'
27 Amma shi wanda ake kwarar makwabcinsa ya ture Musa a gefe guda, ya ce, 'Wa ya nada ka shugaba ko alkali akanmu?
28 Kana so ka kashe ni ne, kamar yadda ka kashe Bamasaren nan jiya?'
29 Da jin haka sai Musa ya gudu, zuwa kasar Midinawa, a matsayin dan gudun hijira. Anan ya haifi ''ya'ya biyu maza.
30 Bayan da shekaru arba'in suka wuce, sai mala'ika ya bayyana gare shi a jeji, kusa da dutsen Sinai, a cikin harshen wuta a cikin jeji.
31 Sa'adda Musa ya ga wutar, mamaki ya kama shi; sai ya maso kusa don ya kara dubawa, sai ya ji muryar Ubangiji na cewa,
32 'Nine Allah na ubanninka, Ibrahim, da na Ishaku, da na Yakubu.' Musa ya razana har ma bai sake daga kai ya duba ba.
33 Ubangiji ya ce masa, 'Tube takalminka, domin in da kake tsaye wuri mai tsarki ne.
34 Ba shakka na ga wahalar da mutane na ke sha a Masar, kuma na ji nishinsu, don haka na zo in cece su, yanzu fa sai ka zo, in aike ka zuwa Masar.'
35 Wannan fa shine Musan da suka ki, harma da cewa, 'Wanene ya nada ka alkali ko shugaba a kanmu?' Shine kuma wanda Allah ya aiko masu a matsayin shugaba da kuma mai ceto. Allah ya aiko shi ta hannun mala'ikan da ya gani a daji.
36 Bayan alamu da al'ajibai iri-iri a Masar da kuma Baharmaliya, Musa ya fito da su daga Masar da kuma cikin jeji, a lokacin da suka yi tafiya shekara arbain.
37 Wannan shine Musan da ya cewa Isra'ilawa, 'Ubangiji zai tayar maku da wani annabi kamar ni daga cikin Yan'uwan ku.'
38 Wannan shine mutumin da ke tare da mutane a jeji. Karkashin jagorancin mala'ikan da ya yi magana da shi a dutsen Sinai. Wannan ne mutumin da ke tare da ubannen mu, wannan shi ne mutumin da ya ba mu maganar Allah mai rai.
39 Wannan shine mutumin da ubannenmu suka ki su yi masa biyayya; su ka fitar da shi daga cikinsu, suka kudurta a zuciyarsu za su koma masar.
40 A lokacin ne suka cewa Haruna, 'ya yi masu allolin da za su jagorance su zuwa masar. Domin kuwa ga zancen Musan nan da ya fito da mu daga Masar, ba mu san abin da ya faru da shi ba.'
41 Sai suka kera dan maraki suka kawo wa gunkin hadaya, suka yi murna da abin da hannayensu suka kera.
42 Allah ya bashe su su bauta wa tauraran sama, kamar yadda yake a rubuce cikin littattafafan annabawa, 'Kun mika mani hadayu na yankakkun dabbobi a jeji ne a shekaru arba'in din nan ya ku Isra'ilawa?'
43 Kun yarda da haikalin Molek da kuma tauraron allahn nan Rafem, da kuma siffofin nan da kuka kera don ku yi masu sujada; don haka zan kai ku bauta har gaba da Babila.'
44 Kakkaninmu suna da alfarwa ta sujada domin shaida a cikin jeji, kamar yadda Allah ya umarta yayin da ya yi magana da Musa, cewa ya yi shi bisa ga salon da aka nuna mashi.
45 Wannan shine Alfarwar da kakkaninmu suka zo da shi, a lokacin Joshuwa. Wannan ya faru ne yayin da suka mallaki wannan kasa ta al'ummai da Allah ya kora a gaban kakkaninmu. Haka abin yake har ya zuwa zamanin Dauda,
46 wanda ya sami tagomashi a wurin Allah; don ya gina masujada domin Allah na Yakubu.
47 Amma Sulaimanu ne ya gina Gidan Allah.
48 Sai dai Madaukaki ba yakan zauna a gidan da hannaye suka gina ba, kamar yadda annabin ya ce,
49 'Sama kursiyina ce, duniya kuwa wurin ajjiye sawayena ne. To wane irin gida za ku gina mani? inji Ubangiji: ko kuwa ina ne wurin da zan huta?
50 Ko ba hannayena ne suka yi dukan wadannan ba?'
51 Ku mutane masu taurin kai masu zuciya mara kaciya da kunnuwa marasa ji, kullum kuna gaba da Ruhu Mai Tsarki, kuna aikata abin da kakkaninku suka aikata.
52 Wane annabi ne kakkaninku ba su tsanantawa ba? Sun kashe annabawan da suka rigayi zuwan Mai Adalcin nan, kuma kun zama wadanda suka kasance masu bashe shi da masu kashe shi,
53 kune mutanen da kuka karbi shari'a wadda mala'iku suka bayar, amma ba ku kiyaye ta ba”.
54 Yayin da majalisar suka ji wannan, sai ransu ya baci kwarai, har suna cizon hakoransu don gaba da Istifanus.
55 Amma shi, cike da Ruhu Mai Tsarki, sai ya daga idonsa sama, ya ga daukakar Allah; ya kuma hango Yesu na tsaye a hannun daman Allah.
56 Istifanus ya ce, “Duba, ina ganin sama ta bude, ga Dan Mutum na tsaye a hannun dama na Allah.”
57 Amma yan majalisar suka daga murya da karfi, suka yi ihu, suka kuma toshe kunnuwansu, gaba dayansu suka afka masa;
58 suka fitar da shi bayan gari, suka jejjefe shi da duwatsu, don shaida sai suka tube manyan rigunansu suka ajiye a gaban wani matashi da ake ce da shi Shawulu.
59 Lokacin da suke kan jifan Istifanus, ya dinga kira yana cewa, ''Ya Ubangiji Yesu, ka karbi ruhu na.”
60 Ya durkusa ya daga murya da karfi, ya ce, “Ya Ubangiji, kada ka rike wannan zunubi a kansu.” Yayin da ya fadi wannan, sai ya yi barci.