< Ayyukan Manzanni 5 >

1 Sai wani mai suna Hananiya da matarsa Safiratu, suka sayar da filinsu,
But a certain man named Ananias, together with Sapphira his wife,
2 Hananiya kuwa ya boye wasu daga cikin kudin filin, (kuma da sanin matarsa), sa'annan suka kawo ragowar kudin a gaban manzannin.
sold a possession, and secreted part of the price, his wife also being conscious to it; and bringing: some part, laid it at the feet of the apostles.
3 Amma Bitrus ya ce, ''Hananiya don me shaidan ya cika zuciyarka, har ka yi wa Ruhu Mai Tsarki karya? Har ka boye wasu daga kudin filin?
But Peter said, Ananias, why hath Satan so filled thine heart, that thou shouldst lie to the holy Ghost, and keep back part of the price of the land?
4 Sa'adda ba ka sayar da filin ba, ba mallakarka bane? Bayan da ka sayar ma, ba naka bane? Don me kayi irin wannan tunanin a zuciyarka? To ba mutane ka yi wa karya ba, Allah ka yi wa.”
While it remained, did it not remain thy own? and when sold, was it not in thy own power? what is the meaning that thou hast taken this into thine heart? Thou hast not lyed to men, but to God.
5 Nan take da jin haka, Hananiya ya fadi ya ja numfashinsa na karshe. Dukan mutanen da suka ji labarin kuwa tsoro mai girma ya afko masu
And Ananias at the hearing of these words fell down and expired: and great fear came on all that heard these things.
6 Matasa suka zo suka nannade gawarsa, suka fitar da shi waje suka binne shi.
And some of the young men arose, and wrapped him up; and they carried him out, and buried him.
7 Bayan wajen sa'a uku, sai matarsa ta iso, ba tare da sanin abin da ya faru ba.
And about the space of three hours after, his wife also came in, not knowing what had happened.
8 Sai Bitrus ya ce mata, ''ki gaya mini ko nawa kuka sayar da filin?'' Sai ta amsa, ''ta ce kaza ne.”
And Peter said to her, Tell me whether ye sold the land for so much. And she said, Yes, for so much.
9 Sa'annan Bitrus ya ce mata, ''Don me kuka shirya wannan makidar tare da mijinki don ku gwada Ruhun Ubangiji? Kiji tafiyar wadanda suka bizne mijinki a bakin kofa, kuma za su dauke ki yanzu.''
Then Peter said unto her, Wherefore have ye agreed together to tempt the Spirit of the Lord? behold the feet of those, who have been burying thy husband, now at the door, and they shall carry thee out.
10 Nan take sai ta fadi a gabansa, ta ja numfashinta na karshe, matasan kuwa suka zo suka same ta ta mutu; sai suka dauki gawarta suka kai waje suka kuma bizne ta kusa da mijinta.
And immediately she fell down at his feet and expired: and the young men coming in found her dead, and they carried her out and buried her by her husband.
11 Tsoro mai girma kuwa ya afko wa iklisiyar gaba daya da dakan wadanda suka ji wadan nan al'amura.
And great fear came upon the whole assembly, and upon all that heard these things.
12 Ayyukan alamu da ban mamaki masu yawa kuwa sun faru ga mutane, ta hannun manzannin. Dukansu kuma suna nan tare a dakalin Sulaimanu,
And by the hands of the apostles were many signs and wonders done among the people: And they all met with one accord in Solomon's portico:
13 Sai dai babu mai karfin halin ya hada kai tare dasu; amma suna da kwarjini sosai a gaban jama'a.
but no other presumed to join himself to them; however the people magnified them.
14 Har wa yau aka rika samun karin masu ba da gaskiya, dinbin jama'a, maza da mata,
And true believers were the more willingly added to the Lord, even multitudes both of men and women.
15 har sukan dauki marasa lafiya su kai su bakin titi, suna kwantar da su a bisa gadaje da shinfidu, domin idan Bitrus ya zo wucewa ko da inuwarsa ma ta taba wasunsu.
insomuch that they brought the sick out into the streets, and laid them on beds and couches, that at lest the shadow of Peter, as he came by, might pass over some of them.
16 Mutane dayawa kuwa sukan zo daga garuruwan da ke kewaye da Urushalima, suna kuma kawo masu rashin lafiya, da wadanda aljannu ke damunsu, aka kuma warkar da su duka.
And a great number out of the cities round about also came together to Jerusalem, bringing those that were infirm and that were troubled with impure spirits; and they were all cured.
17 Amma babban firist ya taso tare da duk wadanda ke tare da shi (wato 'yan darikar Sadukiyawa); suka cika da kishi matuka
Then the high priest rose up, and all that were with him, (being of the sect of the sadducees, ) and were filled with rage:
18 suka kama manzannin suka kuma jefasu a kurkuku.
and laid their hands on the apostles, and put them in the public prison.
19 A cikin dare sai mala'ikan Ubangiji ya bude kofofin kurkukun ya kuma fito da su waje, ya ce,
But an angel of the Lord opened the doors of the prison by night, and having brought them out said,
20 “Kuje ku tsaya a gaban haikali ku kuma gaya wa mutane maganar wannan rai.”
"Go stand and speak in the temple to the people all the words of this life."
21 Sa'adda suka ji haka, sai suka tafi haikalin da wayewar gari suka yi koyarwa. Amma babban firist da jama'arsa suka zo suka kuma kira taro da kuma dukan yan majalisa, da dattawan jama'ar Isra'ilawa suka fito suka kuma ba da umarni, a fito masu da manzannin.
And hearing this, they went early in the morning into the temple and taught the people. But the high priest being come, and they that were with him, to the council-chamber, they called together the Sanhedrim, and all the senate of the children of Israel, and sent orders to the prison that they should be brought before them.
22 Amma ma'aikatan da suka je kurkukun basu sami kowa, a kurkukunba, sai suka dawo suka ba da rahoto,
But when the officers came they found them not in the prison: so they returned,
23 Su ka ce kurkukun a rufe gam da masu gadi suna nan a tsaye a bakin kofar amma da muka shiga, bamu sami kowa a ciki ba.
and told them, saying, the prison we found shut with all safety, and the keepers standing without before the doors: but when we opened them, we found no body within.
24 Yanzu sa'adda shugaban haikalin da manyan firistoci suka ji wadannan kalamai, sai suka rikice sosai game da su, suka ce yanzu me wannan zai haifar.
Now when the high priest, and the captain of the temple, and the chief priests heard these words, they were in doubt concerning them, what this would come to;
25 Sai wani ya zo ya ce masu, ''Wadannan mutanen da kuka jefa a kurkuku suna can a cikin haikali suna koyar da jama'a.''
when there came one and told them, saying, behold, the men whom ye put in prison, are in the temple teaching the people.
26 Sai shugaban haikalin ya je da ma'aikatansa suka kawosu, ba tare da tashin hankali ba, domin gudun kada jama'a su jejjefesu.
Then the captain went with the officers and brought them, but not with violence; for they were afraid of the people least they should be stoned:
27 Da suka kawo su, sai suka gabatar da su gaban majalisa, babban firist kuwa ya tuhume su,
and when they had brought them, they set them before the council. And the high priest asked them,
28 cewa ''Ba mun yi maku kashedi da karfi kada ku yi koyarwa cikin wannan sunan ba? Amma ga shi duk kun cika Urushalima da koyarwarku, kuna kuma neman kusa jinin mutumin nan ya sauko kanmu.”
saying, Did not we strictly charge you not to teach in this name? and behold ye have filled Jerusalem with your doctrine, and would bring this man's blood upon us.
29 Amma Bitrus da manzannin suka amsa suka ce, ''Dole mu yi wa Allah biyayya ba mutane ba.
But Peter, and the other apostles, answered, and said, We ought to obey God rather than men.
30 Allah na ubanenmu ya ta da Yesu, wanda kuka kashe, ta wurin rateye shi a bisa itace,
The God of our fathers hath raised up Jesus whom ye slew and hanged on a tree.
31 Allah kuwa ya daukaka shi a hannun damarsa, domin ya zama sarki da kuma mai ceto, ya ba Isra'ila tuba da gafarar zunubai.
Him hath God exalted with his right hand as a prince and saviour, to give repentance to Israel, and remission of sins:
32 Mu kuwa shaidu ne ga wadannan al'amura, haka ma Ruhu Mai Tarki, wanda Allah ya bayar ga dukan wadanda suka yi biyayya a gareshi.''
and we are his witnesses of what we declare; and so is the holy Spirit, whom God hath given to them that obey Him.
33 Da yan majalisa suka ji haka sai suka fusata kwarai da gaske, har suka nemi su kashe manzannin.
And when they heard this, they were cut to the heart, and took counsel to put them to death.
34 Amma wani Bafarise mai suna Gamaliel, malami ne kuma na attaura wanda dukan jama'a suna martabawa, sai ya mike ya ba da umarni cewa a fid da manzannin waje na dan lokaci.
But a certain pharisee, named Gamaliel, a doctor of the law, held in much esteem by all the people, stood up in the council, and ordered the apostles to be taken out a little while; and then he said unto them,
35 Sai ya ce masu ''Ya ku mutanen Isra'ila, ku lura sosai da a binda kuke niyyar yi wa mutanen nan,
Men of Israel, take heed to yourselves, what ye are about to do, as to these men.
36 A kwanakin baya wani ya zo mai suna Tudas ya dauki kansa wani abu, kimanin mutane dari hudu ne suka bishi, amma da aka kashe shi jama'arsa baki daya sai suka watse, ba wanda ya kara jin labarinsu.
For some time ago one Theudas arose, pretending to be some extraordinary person, to whom was joined a number of men, about four hundred: who was slain, and all that followed him were dispersed and came to nothing.
37 Bayansa kuma, aka yi wani mai suna Yahuza na Galili wanda a kwanakin kidaya, ya zo ya rinjayi mutane da yawa, shima ya lalace, duk wadanda suka bi shi kuwa suka watse.
After him arose Judas the Galilean, at the time of the registring, and drew much people after him: but he also perished, and all that followed him were dispersed.
38 Don haka ina gaya maku ku rabu da mutanen nan, domin idan shirinsu ko kuma ayyukansu na mutane ne za su lalace.
And therefore as to the present affair I advise you to refrain from these men and let them alone: for if this counsel or this work be of men, it will come to nothing;
39 Amnma idan abin nan daga Allah yake baza ku iya lalata su ba; kada ya zama kuna gaba da Allah.'' Sai suka rinjayu.
but if it be of God, ye cannot defeat it, least ye be found fighting even against God.
40 Da suka kira manzannin ciki suka yi masu duka, sai suka umarce su da cewa kada su sake koyarwa a cikin sunan Yesu, sai suka barsu suka tafi.
So they took his advice, and having called for the apostles and scourged them, they charged them not to speak in the name of Jesus, and let them go.
41 Suka fita daga cikin majalisar, suna murna domin sun cancanta su sha wulakanci saboda sunan.
And they departed from the presence of the council rejoicing that they were counted worthy to suffer disgrace for his name.
42 Bayan haka kullayomin suna zuwa haikali, suna bi gida gida, suna wa'azi, suna kuma koyarwa ba fasawa cewa Yesu shine Almasihu.
And every day in the temple and from house to house they ceased not from teaching and preaching that Jesus was the Christ.

< Ayyukan Manzanni 5 >