< Ayyukan Manzanni 4 >
1 Yayin da Bitrus da Yahaya suna kan magana da mutanen, sai firistoci da shugaban masu tsaron Haikali da kuma Sadukiyawa suka afko masu.
2 Sun damu sosai domin Bitrus da Yahaya suna koyar da mutane game da Yesu kuma suna shelar tashinsa daga matattu.
3 Suka kama su suka jefa kurkuku sai washegari, domin yamma ta riga ta yi.
4 Amma mutane da yawa da suka ji sakon suka ba da gaskiya; kimanin mazaje dubu biyar ne kuwa suka ba da gaskiya.
5 Washegari, da shugabaninsu, da dattawansu, da Marubuta suka taru a Urushalima.
6 Anas babban firist, yana nan, da Kayafa, da Yahaya da Iskandari, da dukan dangin babban firist
7 Da suka kawo Bitrus da Yahaya a tsakiyarsu sai suka tambaye su, “Da wanne iko, ko cikin wanne suna k ka yi haka?”
8 Sai Bitrus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya ce, “Ku shugabanni da dattawan jama'a,
9 idan mu yau ana tuhumarmu saboda aikin kirki da aka yi ga wannan mara lafiya - ta yaya wannan mutum ya sami lafiya?
10 Bari ku da dukan mutanen Isra'ila, ku san wannan, cikin sunan Yesu Almasihu Banazare, wanda kuka giciye, wanda Allah ya tayar daga matattu ta dalilinsa ne wannan mutumin yake tsaye a gaban ku lafiyayye.
11 Yesu Almasihu ne dutsen da ku magina kuka ki, amma an mai da shi kan gini.
12 Babu ceto daga kowanne mutum, domin babu wani suna da aka bayar karkashin sama, a cikin mutane wanda ta wurinsa za a iya samu ceto.''
13 Sa'adda, suka ga karfin halin Bitrus da Yahaya, suka gane mutane ne talakawa marasa ilimi, sai suka yi mamaki, suka kuma lura suka gane Bitrus da Yahaya sun kasance tare da Yesu.
14 Da yake suna ganin mutumin nan da aka warkar tare da su, sai suka rasa abin yi.
15 Amma bayan sun fitar da manzannin daga majalisa sai suka tattauna a tsakaninsu.
16 Suka ce, “Yaya za mu yi da wadannan mutane? Babu shakka aikin al'ajibi ya faru ta wurinsu, kuma sananne ne ga dukan mazauna Urushalima, kuma ba mu da iko mu musanci haka.
17 Amma saboda kada ya cigaba da yaduwa cikin mutane, bari mu yi masu kashedi kada su kara magana da kowa cikin wannan suna.''
18 Suka kira Bitrus da Yahaya suka dokace su kada su kara magana ko kuma koyarwa ko kadan a cikin sunan Yesu.
19 Amma Bitrus da Yahaya suka amsa suka ce, ''Ko ya yi daidai a gaban Allah mu yi maku biyayya fiye da shi, ku hukunta.
20 Baza mu iya daina magana game da abubuwan da muka ji kuma muka gani ba.''
21 Bayan sun sake yi wa Bitrus da yahaya kashedi, sai suka sake su, su tafi. Domin ba su iya samu wata hujja da za su hore su a kai ba, domin dukan mutane suna yabon Allah saboda abin da ya faru.
22 Mutumin da ya sami wannan al'ajibi na warkarwa yana sama da shekara arba'in.
23 Bayan an sake su, Bitrus da Yahaya suka zo cikin mutanensu suka ba da rahoton duk abin da manyan firistoci da dattawa suka fada masu.
24 Da suka ji haka, suka daga muryarsu tare ga Allah suka ce, ''Ubangiji, kai da ka yi sama da duniya da teku da duk abin da ke cikinsu,
25 kai wanda ta wurin Ruhu Mai Tsarki ta bakin ubanmu Dauda bawanka, ya ce, 'Me ya sa al'ummai suka tunzura, kuma mutane suke tunanin abubuwan banza?
26 Sarakunan duniya sun hada kansu tare, kuma shugabanninsu sun taru don su yi gaba da Ubangiji, da kuma Almasihunsa.'
27 Hakika, Hiridus da Buntus Bilatus, tare da al'ummai da mutanen Isra'ila, sun taru a wannan birni domin su yi jayayya da bawanka mai tsarki Yesu, shafaffe.
28 Sun taru domin su aiwatar da dukan abin da hannunka da nufinka ya shirya zai faru.
29 Yanzu, Ya Ubangiji ka dubi kashedin su, ka ba bayin ka ikon furta maganar ka gabagadi.
30 Sa'adda ka mika hannunka domin warkarwa, alamu da al'ajibai su faru ta wurin sunan bawanka mai tsarki Yesu.”
31 Bayan sun gama addu'a, wurin da suka taru ya girgiza, suka cika da Ruhu Mai Tsarki, suka furta maganar Allah gabagadi.
32 Babban taron da suka ba da gaskiya kansu hade yake; kuma ba wanda ya ce da abinda ya mallaka nasa ne; maimakon haka, komai na su daya ne.
33 Da iko mai karfi manzannin suka yi shelar shaidarsu game da tashin Yesu Ubangiji daga matattu, babban alheri kuma na bisansu.
34 Babu wani a cikinsu wanda ya rasa komai, domin masu filaye da gidaje suka sayar suka kawo kudin abin da suka sayar
35 sai suka kawo kudin gaban manzanni. Aka rarraba wa kowanne mutum bisa ga bukatarsa.
36 Yusufu, Balawi, mutumin tsibirin Kubrus, wanda manzannisu ka yi wa lakani da suna Barnaba. (wato, mai karfafa zuciya).
37 Yana da fili sai ya sayar da shi ya kawo kudin gaban manzanni.