< Ayyukan Manzanni 26 >
1 Sai Agaribas ya ce wa Bulus, “Za ka iya kare kan ka.” Sai Bulus ya daga hannunsa ya fara kare kansa.
2 “Ina farinciki, ya sarki Agaribas, game da saran da Yahudawa ke kawowa a kaina yau;
3 musamman ma don kai masani ne game da al'adun Yahudawa da al'amuransu. Don haka, ina rokanka ka yi hakuri ka saurare ni.
4 Hakika, dukan Yahudawa sun san yadda na yi rayuwa ta daga kurciyata a kasa ta, da kuma Urushalima.
5 Sun san ni tun farko, kuma yakamata su yarda cewa na yi rayuwa kamar Bafarase, darikan nan mai tsatsauran ra'ayi ta addininmu.
6 Yanzu ina tsaye a nan dominn a shari'anta ni, saboda alkawalin da Allah ya yi wa ubanninmu.
7 Domin wannan shine alkawalin da kabilunmu goma sha biyu suka sa zuciya su karba, yayin da suke yin sujada da himma ga Allah dare da rana. Saboda wanan bege, Sarki Agaribas, Yahudawa ke tuhuma ta.
8 Me ya sa wani zai yi tunani cewa abin mamaki ne Allah ya ta da mattatu?
9 Da, na yi tunanin yin abubuwa gaba da sunan Yesu Banazarat.
10 Na yi wadanan a Urshalima. Na kulle masu bi da yawa a kurkuku, sanadiyar iko da na samu daga wurin manyan firistoci, kuma da ake kashe su ma, ina ba da goyon baya.
11 Na wahalshe su sau dayawa a cikin dukan majamiu ina kuma yin kokari in tilasta masu su yi sabo. Na yi gaba mai zafi da su kuma na tsananta masu har zuwa birane na wadansu kasashe.
12 A sa'anda nake yin wannan, na tafi Dimashku da izinin manyan firistoci;
13 a cikin tafiyata kuma, da tsakar rana, ya sarki, na ga haske daga sama da ya fi rana sheki, ya haskaka kewaye da ni da kuma wadanda ke tafiya tare da ni.
14 Da dukanmu muka fadi kasa, na ji wata murya na magana da ni a harshen Ibraniyawa tana cewa, 'Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mani? Yana da wuya ka hauri abin da ke mai tsini.'
15 Sai na ce, 'Wanene kai ya Ubangiji?' Ubangiji ya amsa, 'Ni ne Yesu wanda kake tsanantawa.
16 Yanzu ka tashi tsaye domin saboda wannan dalili ne na bayyana gare ka in sanya ka, ka zama bawa da mashaidi na game da abubuwan da ka sani a kaina yanzu da wadanda zan bayyana maka daga bisani;
17 Zan kubutar da kai daga wurin mutane da kuma al'ummai da zan aike ka wurinsu,
18 domin ka bude idanunsu ka juyo su daga duhu zuwa haske da daga ikon Shaidan zuwa ga Allah, domin su karbi gafarar zunubai da gado da zan ba wadanda na kebe wa kaina ta wurin bangaskiya gare ni.'
19 Saboda haka, sarki Agaribas, ban yi rashin biyayya da wahayin da na gani daga sama ba;
20 amma, da farko ga wadanda ke a Dimashku, sa'annan a Urushalima da kasar Yahudiya gaba daya, da dukan Al'ummai, na yi wa'azi domin su tuba su kuma juyo ga Allah, su yi ayyukan da suka chanchanci tuba.
21 Domin wannan dalili ne Yahudawa suka kama ni a cikin haikali kuma suke kokari su kashe ni.
22 Allah ya taimake ni har wa yau, domin in iya tsayawa gaban mutane kanana da manya, in bada shaida game da iyakar abin da annabawa da Musa suka fada zai faru;
23 wato lallai Almasihu zai sha wahala, ya kuma zama na farko da za'a rayar daga matattu ya kuma yi shelar haske zuwa ga mutanen Yahudawa da Al'ummai.”
24 Da Bulus ya gama kare kansa, Festas ya yi magana da babban murya, “Bulus, kana hauka; yawan iliminka yasa ka hauka.”
25 Amma Bulus ya ce, “Ba na hauka, ya mai girma Festas; amma da karfin zuciya nake fadi kalmomin gaskiya da na natsuwa.
26 Saboda sarkin ya san wadannan abubuwa duka; shi ya sa nake magana gabagadi, don na hakikance cewa, ba abin da ke a boye gare shi; gama ba a yi wadannan abubuwa a boye ba.
27 Ko ka gaskanta da annabawa, Sarki Agaribas? Na sani ka gaskanta.”
28 Agaribas ya ce wa Bulus, “A cikin karamin lokaci kana so ka rinjaye ni ka mai da ni Krista?”
29 Bulus ya ce, “Ina roko ga Allah, domin ko a karamin lokaci ko a dogon lokaci, ba kai kadai ba, amma har da wadanda ke sauraro na yau su zama kamar ni, amma ban da wadannan sarkokin.”
30 Sai sarki ya tashi tsaye tare da gwamna da Barniki da dukan wadanda ke zaune tare da su;
31 da suka bar dakin taron, suka ci gaba da magana da juna suna cewa, “Wannan mutum bai yi wani abin da ya chanchanci mutuwa ko kuma dauri ba.”
32 Agaribas ya ce wa Fastos, “Da mutumin nan bai daukaka kara zuwa ga Kaisar ba da an sake shi.”