< Ayyukan Manzanni 25 >

1 Da Festas ya shiga lardin, kuma bayan kwana uku, ya tashi daga Kaisariya ya tafi Urushalima.
Φῆστος οὖν ἐπιβὰς τῇ ἐπαρχίᾳ μετὰ τρεῖς ἡμέρας ἀνέβη εἰς Ἱεροσόλυμα ἀπὸ Καισαρείας,
2 Sai babban firist da manyan Yahudawa suka kawo wa Festas sara a kan Bulus.
ἐνεφάνισάν τε αὐτῷ οἱ ἀρχιερεῖς καὶ οἱ πρῶτοι τῶν Ἰουδαίων κατὰ τοῦ Παύλου, καὶ παρεκάλουν αὐτὸν
3 Suka roki tagomashi wurin Festas ya kira Bulus zuwa Urushalima domin su kashe shi a hanya.
αἰτούμενοι χάριν κατ᾽ αὐτοῦ, ὅπως μεταπέμψηται αὐτὸν εἰς Ἱερουσαλήμ, ἐνέδραν ποιοῦντες ἀνελεῖν αὐτὸν κατὰ τὴν ὁδόν.
4 Amma Festas ya amsa masu cewa, Bulus dan sarka ne a Kaisariya, kuma ba da dadewa ba shi da kansa zai koma can.
ὁ μὲν οὖν Φῆστος ἀπεκρίθη τηρεῖσθαι τὸν Παῦλον εἰς Καισαρείαν, ἑαυτὸν δὲ μέλλειν ἐν τάχει ἐκπορεύεσθαι·
5 “Saboda haka duk wadanda za su iya, su biyo mu. Idan akwai wani laifi game da mutumin, sai ku zarge shi.”
οἱ οὖν ἐν ὑμῖν, φησίν, δυνατοὶ συγκαταβάντες, εἴ τί ἐστιν ἐν τῷ ἀνδρὶ ἄτοπον, κατηγορείτωσαν αὐτοῦ.
6 Bayan kwana takwas ko goma, sai ya gangara zuwa Kaisariya. Washegari ya zauna bisa kursiyin shari'a ya bada umarni a kawo Bulus a gabansa.
διατρίψας δὲ ἐν αὐτοῖς ἡμέρας οὐ πλείους ὀκτὼ ἢ δέκα, καταβὰς εἰς Καισάρειαν, τῇ ἐπαύριον καθίσας ἐπὶ τοῦ βήματος ἐκέλευσεν τὸν Παῦλον ἀχθῆναι.
7 Da Bulus ya iso, Yahudawa daga Urushalima suka tsaya kusa, suka yi ta kawo kararraki, amma basu iya tabbatar da su ba.
παραγενομένου δὲ αὐτοῦ περιέστησαν αὐτὸν οἱ ἀπὸ Ἱεροσολύμων καταβεβηκότες Ἰουδαῖοι, πολλὰ καὶ βαρέα αἰτιώματα καταφέροντες, ἃ οὐκ ἴσχυον ἀποδεῖξαι,
8 Bulus ya kare kansa ya ce, “Ban yi wa kowa laifi ba, ko Yahudawa, ko haikali, ko kuma Kaisar.”
τοῦ Παύλου ἀπολογουμένου ὅτι Οὔτε εἰς τὸν νόμον τῶν Ἰουδαίων, οὔτε εἰς τὸ ἱερόν, οὔτε εἰς Καίσαρά τι ἥμαρτον.
9 Amma Festas yana neman farin jini wajen Yahudawa, sabo da haka ya tambayi Bulus ya ce, “Kana so ka je Urushalima in shari'anta ka a can game da wadannan abubuwa?”
ὁ Φῆστος δὲ θέλων τοῖς Ἰουδαίοις χάριν καταθέσθαι, ἀποκριθεὶς τῷ Παύλῳ εἶπεν, Θέλεις εἰς Ἱεροσόλυμα ἀναβὰς ἐκεῖ περὶ τούτων κριθῆναι ἐπ᾽ ἐμοῦ;
10 Bulus ya ce, “Ina tsaye a Ddakalin Shari'ar Kaisar inda dole a shari'anta ni. Ban yi wa Yahudawa laifi ba, kamar yadda ka sani sosai.
εἶπεν δὲ ὁ Παῦλος, Ἐπὶ τοῦ βήματος Καίσαρος ἑστώς εἰμι, οὗ με δεῖ κρίνεσθαι. Ἰουδαίους οὐδὲν ἠδίκηκα, ὡς καὶ σὺ κάλλιον ἐπιγινώσκεις·
11 Idan lallai na yi laifi kuma na yi abin da ya chanchanci mutuwa, ban ki ba in mutu. Amma idan zarginsu karya ne, kada kowa ya bashe ni gare su. Ina daukaka kara zuwa ga Kaisar.”
εἰ μὲν οὖν ἀδικῶ καὶ ἄξιον θανάτου πέπραχά τι, οὐ παραιτοῦμαι τὸ ἀποθανεῖν· εἰ δὲ οὐδέν ἐστιν ὧν οὗτοι κατηγοροῦσίν μου, οὐδείς με δύναται αὐτοῖς χαρίσασθαι. Καίσαρα ἐπικαλοῦμαι.
12 Bayan Festas ya tattauna da majalisa ya amsa ya ce, “Kana kira ga Kaisar; za ka tafi wurin Kaisar.”
τότε ὁ Φῆστος συλλαλήσας μετὰ τοῦ συμβουλίου ἀπεκρίθη, Καίσαρα ἐπικέκλησαι, ἐπὶ Καίσαρα πορεύσῃ.
13 Bayan wadansu kwanaki, sarki Agaribas da Barniki suka iso Kaisariya domin su ziyarci Festas.
Ἡμερῶν δὲ διαγενομένων τινῶν, Ἀγρίππας ὁ βασιλεὺς καὶ Βερνίκη κατήντησαν εἰς Καισάρειαν, ἀσπασάμενοι τὸν Φῆστον.
14 Da ya kasance kwanaki da yawa, Festas ya fada wa sarki labarin Bulus ya ce, “Akwai wani mutum dan sarka da Filikus ya bari a kurkuku.
ὡς δὲ πλείους ἡμέρας διέτριβον ἐκεῖ, ὁ Φῆστος τῷ βασιλεῖ ἀνέθετο τὰ κατὰ τὸν Παῦλον λέγων, Ἀνήρ τίς ἐστιν καταλελειμμένος ὑπὸ Φήλικος δέσμιος,
15 Sa'anda nake a Urushalima, babban firist da dattawan Yahudawa suka kawo kararsa gare ni, suka roka a kashe shi.
περὶ οὗ γενομένου μου εἰς Ἱεροσόλυμα ἐνεφάνισαν οἱ ἀρχιερεῖς καὶ οἱ πρεσβύτεροι τῶν Ἰουδαίων, αἰτούμενοι κατ᾽ αὐτοῦ καταδίκην·
16 Game da wannan na amsa na ce masu, ba al'adar Romawa ba ce a ba da mutum tagomashi; sai wanda ake kararsa an bashi zarafi ya kare kansa a gaban masu kararsa, ya kuma bada hujjojinsa game da kararakin.
πρὸς οὓς ἀπεκρίθην ὅτι οὐκ ἔστιν ἔθος Ῥωμαίοις χαρίζεσθαί τινα ἄνθρωπον πρὶν ἢ ὁ κατηγορούμενος κατὰ πρόσωπον ἔχοι τοὺς κατηγόρους, τόπον τε ἀπολογίας λάβοι περὶ τοῦ ἐγκλήματος.
17 Saboda haka, da duk suka taru ban bata lokaci ba, washegari na zauna a kujerar shari'a, na ba da umarni a kawo mutumin.
συνελθόντων οὖν αὐτῶν ἐνθάδε ἀναβολὴν μηδεμίαν ποιησάμενος, τῇ ἑξῆς καθίσας ἐπὶ τοῦ βήματος, ἐκέλευσα ἀχθῆναι τὸν ἄνδρα·
18 Da masu karar suka fadi kararsu, sai na fahimci karar ba wani muhimmin abu a cikinta.
περὶ οὗ σταθέντες οἱ κατήγοροι οὐδεμίαν αἰτίαν ἔφερον ὧν ἐγὼ ὑπενόουν πονηρῶν·
19 Sai dai na ga cewa jayayya ce tsakanin su ta addini a kan wani Yesu da ya mutu, wanda Bulus ya ce yana da rai.
ζητήματα δέ τινα περὶ τῆς ἰδίας δεισιδαιμονίας εἶχον πρὸς αὐτόν, καὶ περί τινος Ἰησοῦ τεθνηκότος, ὃν ἔφασκεν ὁ Παῦλος ζῇν.
20 Na rasa yadda zan bincike wannan al'amarin, sai na tambaye shi ko zai je Urushalima a shari'anta shi kan wadannan abubuwa.
ἀπορούμενος δὲ ἐγὼ τὴν περὶ τούτων ζήτησιν, ἔλεγον εἰ βούλοιτο πορεύεσθαι εἰς Ἱεροσόλυμα κἀκεῖ κρίνεσθαι περὶ τούτων.
21 Amma da Bulus ya nemi a lura da shi, Kaisar ya shari'anta shi, sai na ba da umarni a ajiye shi har sai na aika shi wurin Kaisar.”
τοῦ δὲ Παύλου ἐπικαλεσαμένου τηρηθῆναι αὐτὸν εἰς τὴν τοῦ Σεβαστοῦ διάγνωσιν, ἐκέλευσα τηρεῖσθαι αὐτὸν ἕως οὗ ἀναπέμψω αὐτὸν πρὸς Καίσαρα.
22 Agaribas yace wa Festas. “Zan so ni ma in saurari mutumin nan.” “Gobe za ka ji shi,” in ji Fostus.
Ἀγρίππας δὲ πρὸς τὸν Φῆστον, Ἐβουλόμην καὶ αὐτὸς τοῦ ἀνθρώπου ἀκοῦσαι. Αὔριον, φησίν, ἀκούσῃ αὐτοῦ.
23 Washegari Agaribas da Barniki suka zo tare da kasaitaccen taro suka shiga dakin taro tare da hafsoshi da shugabanin gari. Da Festas ya ba da umarni, aka fito da Bulus wurinsu.
Τῇ οὖν ἐπαύριον ἐλθόντος τοῦ Ἀγρίππα καὶ τῆς Βερνίκης μετὰ πολλῆς φαντασίας, καὶ εἰσελθόντων εἰς τὸ ἀκροατήριον σύν τε χιλιάρχοις καὶ ἀνδράσιν τοῖς κατ᾽ ἐξοχὴν τῆς πόλεως, καὶ κελεύσαντος τοῦ Φήστου ἤχθη ὁ Παῦλος.
24 Festas ya ce, “Sarki Agaribas da dukanku da kuke tare da mu a nan, kun ga mutumin nan, dukan Yahudawa sun gana da ni a Urushalima da nan kuma. Suna mani ihu cewa, bai chanchanta a bar shi da rai ba.
καί φησιν ὁ Φῆστος, Ἀγρίππα βασιλεῦ καὶ πάντες οἱ συμπαρόντες ἡμῖν ἄνδρες, θεωρεῖτε τοῦτον περὶ οὗ ἅπαν τὸ πλῆθος τῶν Ἰουδαίων ἐνέτυχόν μοι ἔν τε Ἱεροσολύμοις καὶ ἐνθάδε βοῶντες μὴ δεῖν αὐτὸν ζῇν μηκέτι.
25 Na gane bai yi wani abin da ya chanchanci mutuwa ba; amma saboda ya daukaka kara zuwa Kaisar, na yanke shawara in aika shi.
ἐγὼ δὲ κατελαβόμην μηδὲν ἄξιον αὐτὸν θανάτου πεπραχέναι, αὐτοῦ δὲ τούτου ἐπικαλεσαμένου τὸν Σεβαστὸν ἔκρινα πέμπειν.
26 Amma ba ni da wani dalili na musamman da zan rubuta wasika ga Kaisar. Saboda wannan dalili na kawo shi gabanku, masamman kai ya sarki Agaribas. Domin in sami karin abin da zan rubuta game da shi.
περὶ οὗ ἀσφαλές τι γράψαι τῷ κυρίῳ οὐκ ἔχω, διὸ προήγαγον αὐτὸν ἐφ᾽ ὑμῶν, καὶ μάλιστα ἐπὶ σοῦ, βασιλεῦ Ἀγρίππα, ὅπως τῆς ἀνακρίσεως γενομένης σχῶ τι γράψω·
27 Gama a ganina wauta ce in aika dan sarka ba tare da na rubuta laifi a kansa ba.”
ἄλογον γάρ μοι δοκεῖ πέμποντα δέσμιον, μὴ καὶ τὰς κατ᾽ αὐτοῦ αἰτίας σημᾶναι.

< Ayyukan Manzanni 25 >