< Ayyukan Manzanni 22 >

1 “Yanuwa da Ubanni, ku saurari kariya ta zuwa gare ku yanzu.”
Ἄνδρες ἀδελφοὶ καὶ πατέρες, ἀκούσατέ μου τῆς πρὸς ὑμᾶς νυνὶ ἀπολογίας.
2 Da taron sun ji Bulus na magana a harshen Ibraniyawa sai sun yi tsit. Ya ce,
Ἀκούσαντες δὲ ὅτι τῇ Ἑβραΐδι διαλέκτῳ προσεφώνει αὐτοῖς μᾶλλον παρέσχον ἡσυχίαν. καὶ φησίν·
3 Ni Bayahude ne daga garin Tarwasa na Kilikiya, amma a karkashin Gamaliyal aka ilimantar da ni. An horar da ni sosai bisa ga bin hanyar dokokin kakkaninmu. Ina da himma ga bin Allah kamar yadda ku ma kuna da ita.
⸀Ἐγώεἰμι ἀνὴρ Ἰουδαῖος, γεγεννημένος ἐν Ταρσῷ τῆς Κιλικίας, ἀνατεθραμμένος δὲ ἐν τῇ πόλει ταύτῃ παρὰ τοὺς πόδας Γαμαλιήλ, πεπαιδευμένος κατὰ ἀκρίβειαν τοῦ πατρῴου νόμου, ζηλωτὴς ὑπάρχων τοῦ θεοῦ καθὼς πάντες ὑμεῖς ἐστε σήμερον,
4 Na tsananta wa wannan Hanyan har ga mutuwa; na daure maza da mata sa'annan na jefa su cikin gidan yari.
ὃς ταύτην τὴν ὁδὸν ἐδίωξα ἄχρι θανάτου, δεσμεύων καὶ παραδιδοὺς εἰς φυλακὰς ἄνδρας τε καὶ γυναῖκας,
5 Hakannan ma babban firist da dukan dattawa za su ba da shaida cewa na karbi izini daga wurinsu domin 'yan'uwa da ke a Dimashku, saboda in tafi can. Haki na shine in daure mabiyan Hanyan nan, in kawo su Urushalima domin a hukunta su.
ὡς καὶ ὁ ἀρχιερεὺς μαρτυρεῖ μοι καὶ πᾶν τὸ πρεσβυτέριον· παρʼ ὧν καὶ ἐπιστολὰς δεξάμενος πρὸς τοὺς ἀδελφοὺς εἰς Δαμασκὸν ἐπορευόμην ἄξων καὶ τοὺς ἐκεῖσε ὄντας δεδεμένους εἰς Ἰερουσαλὴμ ἵνα τιμωρηθῶσιν.
6 Sa'anda ina cikin tafiya, ina kuma kusa da Dimashku, da tsakar rana sai farat daya ga babban haske daga sama ya haskaka kewaye dani.
Ἐγένετο δέ μοι πορευομένῳ καὶ ἐγγίζοντι τῇ Δαμασκῷ περὶ μεσημβρίαν ἐξαίφνης ἐκ τοῦ οὐρανοῦ περιαστράψαι φῶς ἱκανὸν περὶ ἐμέ,
7 Na fadi kasa sa'anan na ji murya na ce da ni, 'Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mani?'
ἔπεσά τε εἰς τὸ ἔδαφος καὶ ἤκουσα φωνῆς λεγούσης μοι· Σαοὺλ Σαούλ, τί με διώκεις;
8 Na amsa, 'Wanene kai, Ubangiji?' Ya ce mani, 'Nine Yesu Banazarat wanda kake tsananta wa.'
ἐγὼ δὲ ἀπεκρίθην· Τίς εἶ, κύριε; εἶπέν τε πρὸς ⸀ἐμέ Ἐγώ εἰμι Ἰησοῦς ὁ Ναζωραῖος ὃν σὺ διώκεις.
9 Wadanda ke tare da ni sun ga hasken, amma ba su gane muryar wanda ya yi magana da ni ba.
οἱ δὲ σὺν ἐμοὶ ὄντες τὸ μὲν φῶς ⸀ἐθεάσαντοτὴν δὲ φωνὴν οὐκ ἤκουσαν τοῦ λαλοῦντός μοι.
10 Na ce, 'Me zan yi ya Ubangiji?” Ubangiji ya ce mani, 'Tashi ka tafi cikin Dimashku, a can za a fada maka abinda wajibi ne ka yi.
εἶπον δέ· Τί ποιήσω, κύριε; ὁ δὲ κύριος εἶπεν πρός με· Ἀναστὰς πορεύου εἰς Δαμασκόν, κἀκεῖ σοι λαληθήσεται περὶ πάντων ὧν τέτακταί σοι ποιῆσαι.
11 Ban iya ganin wuri ba domin walkiyar hasken, sai na tafi cikin Dimashku ta wurin jagorancin wadanda ke tare da ni.
ὡς δὲ οὐκ ἐνέβλεπον ἀπὸ τῆς δόξης τοῦ φωτὸς ἐκείνου, χειραγωγούμενος ὑπὸ τῶν συνόντων μοι ἦλθον εἰς Δαμασκόν.
12 A can na sami wani mai suna Ananiya, mai tsoron Allah bisa ga sharia, da kyakyawan suna kuma a gaban Yahudawa da ke zama a can.
Ἁνανίας δέ τις ἀνὴρ ⸀εὐλαβὴςκατὰ τὸν νόμον μαρτυρούμενος ὑπὸ πάντων τῶν κατοικούντων Ἰουδαίων,
13 Ya zo gare ni ya ce, 'Dan'uwa Shawulu, karbi ganin gari.' A daidai wannan sa'a na gan shi.
ἐλθὼν πρὸς ⸀ἐμὲκαὶ ἐπιστὰς εἶπέν μοι· Σαοὺλ ἀδελφέ, ἀνάβλεψον· κἀγὼ αὐτῇ τῇ ὥρᾳ ἀνέβλεψα εἰς αὐτόν.
14 Sa'annan ya ce, 'Allah na kakkaninmu ya zabe ka ka san nufinsa, ka ga Mai Adalcin nan, ka kuma ji muryar da ke fitowa daga bakinsa.
ὁ δὲ εἶπεν· Ὁ θεὸς τῶν πατέρων ἡμῶν προεχειρίσατό σε γνῶναι τὸ θέλημα αὐτοῦ καὶ ἰδεῖν τὸν δίκαιον καὶ ἀκοῦσαι φωνὴν ἐκ τοῦ στόματος αὐτοῦ,
15 Gama za ka zama mashaidinsa ga dukan mutane game da abinda ka gani da wanda ka ji.
ὅτι ἔσῃ μάρτυς αὐτῷ πρὸς πάντας ἀνθρώπους ὧν ἑώρακας καὶ ἤκουσας.
16 A yanzu me ka ke jira? 'Tashi a yi maka baftisma a wanke zunubanka, kana kira bisa sunansa.'
καὶ νῦν τί μέλλεις; ἀναστὰς βάπτισαι καὶ ἀπόλουσαι τὰς ἁμαρτίας σου ἐπικαλεσάμενος τὸ ὄνομα ⸀αὐτοῦ
17 Bayan da na dawo Urushalima, sa'anda ina addu'a a cikin haikali, sai na karbi wahayi.
Ἐγένετο δέ μοι ὑποστρέψαντι εἰς Ἰερουσαλὴμ καὶ προσευχομένου μου ἐν τῷ ἱερῷ γενέσθαι με ἐν ἐκστάσει
18 Na gan shi ya ce mani, 'Gaggauta ka bar Urushalima yanzu, domin ba za su yarda da shaidarka game da ni ba.'
καὶ ἰδεῖν αὐτὸν λέγοντά μοι· Σπεῦσον καὶ ἔξελθε ἐν τάχει ἐξ Ἰερουσαλήμ, διότι οὐ παραδέξονταί ⸀σουμαρτυρίαν περὶ ἐμοῦ.
19 Na ce, 'Ubangiji, su da kansu sun san yadda na sa su a kurkuku na kuma doddoke wadanda suka gaskanta da kai a kowacce masujada.
κἀγὼ εἶπον· Κύριε, αὐτοὶ ἐπίστανται ὅτι ἐγὼ ἤμην φυλακίζων καὶ δέρων κατὰ τὰς συναγωγὰς τοὺς πιστεύοντας ἐπὶ σέ·
20 A sa'anda a ke zubar da jinin mashaidinka Istifanus, ina nan tsaye ina goyon baya, ina kuma lura da rigunan wadanda suka kashe shi.'
καὶ ὅτε ⸀ἐξεχύννετοτὸ αἷμα Στεφάνου τοῦ μάρτυρός σου, καὶαὐτὸς ἤμην ἐφεστὼς καὶ συνευδοκῶν ⸀καὶ φυλάσσων τὰ ἱμάτια τῶν ἀναιρούντων αὐτόν.
21 Amma ya ce mani, 'Tafi, domin zan aike ka can wurin Al'ummai.'
καὶ εἶπεν πρός με· Πορεύου, ὅτι ἐγὼ εἰς ἔθνη μακρὰν ἐξαποστελῶ σε.
22 Mutanen sun bar shi yayi magana har zuwa ga wannan lokacin. Amma sai suka ta da murya suna cewa, 'A kawar da wannan dan taliki daga duniya: don bai kamata ya rayu ba.'
Ἤκουον δὲ αὐτοῦ ἄχρι τούτου τοῦ λόγου καὶ ἐπῆραν τὴν φωνὴν αὐτῶν λέγοντες· Αἶρε ἀπὸ τῆς γῆς τὸν τοιοῦτον, οὐ γὰρ καθῆκεν αὐτὸν ζῆν.
23 Sa'anda suke tadda muryarsu, suna jefar da tufafinsu da kuma baza kura a iska,
⸀κραυγαζόντων⸀τεαὐτῶν καὶ ῥιπτούντων τὰ ἱμάτια καὶ κονιορτὸν βαλλόντων εἰς τὸν ἀέρα,
24 babban hafsan ya umarta a kawo Bulus a farfajiyan. Ya umarta da cewa a bincike shi da bulala, domin ya san dalilin da suka ta da ihu gaba da shi haka.
ἐκέλευσεν ⸂ὁ χιλίαρχος εἰσάγεσθαι αὐτὸν εἰς τὴν παρεμβολήν, ⸀εἴπαςμάστιξιν ἀνετάζεσθαι αὐτὸν ἵνα ἐπιγνῷ διʼ ἣν αἰτίαν οὕτως ἐπεφώνουν αὐτῷ.
25 Bayan da suka daure shi da tsirkiya, Bulus ya ce wa Jarumin da ke kusa da shi, “Ko daidai ne bisa ga doka a yi wa Barome wanda ma sharia ba ta kashe shi ba bulala?”
ὡς δὲ ⸀προέτειναναὐτὸν τοῖς ἱμᾶσιν εἶπεν πρὸς τὸν ἑστῶτα ἑκατόνταρχον ὁ Παῦλος· Εἰ ἄνθρωπον Ῥωμαῖον καὶ ἀκατάκριτον ἔξεστιν ὑμῖν μαστίζειν;
26 Da Jarumin ya ji haka, ya tafi wurin babban hafsan, yana cewa, “Me kake so ka yi? Gama wanan mutumin dan asalin Roma ne.”
ἀκούσας δὲ ὁ ἑκατοντάρχης προσελθὼν ⸂τῷ χιλιάρχῳ ἀπήγγειλεν λέγων· ⸀Τίμέλλεις ποιεῖν; ὁ γὰρ ἄνθρωπος οὗτος Ῥωμαῖός ἐστιν.
27 Babban hafsa ya zo ya ce masa, “Gaya mani, kai dan asalin Roma ne?” Bulus ya ce, “Haka ne.”
προσελθὼν δὲ ὁ χιλίαρχος εἶπεν αὐτῷ· Λέγε μοι, ⸀σὺῬωμαῖος εἶ; ὁ δὲ ἔφη· Ναί.
28 Babban hafsan ya amsa masa, “Da kudi masu yawa na sayi yancin zama dan kasa.” Amma Bulus ya ce, “An haife ni dan kasar Roma.
ἀπεκρίθη ⸀δὲὁ χιλίαρχος· Ἐγὼ πολλοῦ κεφαλαίου τὴν πολιτείαν ταύτην ἐκτησάμην. ὁ δὲ Παῦλος ἔφη· Ἐγὼ δὲ καὶ γεγέννημαι.
29 “Sai mutanen da sun zo su tuhume shi sun bar shi nan da nan. Babban hafsa shi ma ya tsorata da ya gane Bulus dan asalin Roma ne, domin ya riga ya daure shi.
εὐθέως οὖν ἀπέστησαν ἀπʼ αὐτοῦ οἱ μέλλοντες αὐτὸν ἀνετάζειν· καὶ ὁ χιλίαρχος δὲ ἐφοβήθη ἐπιγνοὺς ὅτι Ῥωμαῖός ἐστιν καὶ ὅτι ⸂αὐτὸν ἦν δεδεκώς.
30 Washegari, babban hafsan ya so ya san gaskiyar tuhuma da Yahudawa suke yi a kan Bulus. Sai ya kwance shi daga sarka, ya kuma umarci babban firist da dukan majalisa su sadu. Sai ya kawo Bulus ya sa shi a tsakiyarsu.
Τῇ δὲ ἐπαύριον βουλόμενος γνῶναι τὸ ἀσφαλὲς τὸ τί κατηγορεῖται ⸀ὑπὸτῶν Ἰουδαίων ἔλυσεν ⸀αὐτόν καὶ ἐκέλευσεν ⸀συνελθεῖντοὺς ἀρχιερεῖς καὶ ⸀πᾶντὸ ⸀συνέδριον καὶ καταγαγὼν τὸν Παῦλον ἔστησεν εἰς αὐτούς.

< Ayyukan Manzanni 22 >