< Ayyukan Manzanni 2 >

1 Da ranar Fentikos ta zo, dukansu suna tare wuri daya.
जब ईद — ए — पन्तिकुस्त का दिन आया। तो वो सब एक जगह जमा थे।
2 Nan da nan sai ga wata kara daga sama kamar ta babbar iska, kuma ta sauko ta cika duka gidan inda suke zaune.
एकाएक आस्मान से ऐसी आवाज़ आई जैसे ज़ोर की आँधी का सन्नाटा होता है। और उस से सारा घर जहां वो बैठे थे गूँज गया।
3 Sai ga wasu harsuna kamar na wuta sun bayyana a garesu aka rarraba su, kuma suka zauna bisa kowannensu.
और उन्हें आग के शो'ले की सी फ़टती हुई ज़बाने दिखाई दीं और उन में से हर एक पर आ ठहरीं।
4 Dukansu suka cika da Ruhu Mai Tsarki suka fara magana da wadansu harsuna, yadda Ruhu ya ba su iko su yi magana.
और वो सब रूह — उल — क़ुद्दूस से भर गए और ग़ैर ज़बान बोलने लगे, जिस तरह रूह ने उन्हें बोलने की ताक़त बख़्शी।
5 A lokacin akwai Yahudawa dake zaune a Urushalima, mutanen Allah, daga kowace kasa karkashin sama.
और हर क़ौम में से जो आसमान के नीचे ख़ुदा तरस यहूदी येरूशलेम में रहते थे।
6 Da suka ji wannan kara jama'a duk suka taru suka rude saboda kowannensu ya ji suna magana da harshensa.
जब यह आवाज़ आई तो भीड़ लग गई और लोग दंग हो गए, क्यूँकि हर एक को यही सुनाई देता था कि ये मेरी ही बोली बोल रहे हैं।
7 Suka yi mamaki matuka; suka ce, ''Lallai, wadannan duka ba Galiliyawa ba ne?
और सब हैरान और ता'ज्जुब हो कर कहने लगे, देखो ये बोलने वाले क्या सब गलीली नहीं?
8 Yaya mu ke jinsu duka, kowannensu na magana a cikin harshen da aka haife mu?
फिर क्यूँकर हम में से हर एक कैसे अपने ही वतन की बोली सुनता है।
9 Fisiyawa da Mediyawa da Elimawa, da Yahudawa da Kafadokiya, cikin Fontus da Asiya,
हालाँकि हम हैं: पार्थि, मादि, ऐलामी, मसोपोतामिया, यहूदिया, और कप्पदुकिया, और पुन्तुस, और आसिया,
10 cikin Firgia da Bamfiliya, cikin Masar da yankunan Libiya ta wajen Sur, da baki daga Roma,
और फ़रूगिया, और पम्फ़ीलिया, और मिस्र और लिबुवा, के इलाक़े के रहने वाले हैं, जो कुरेने की तरफ़ है और रोमी मुसाफ़िर
11 Yahudawa da tubabbun cikin Yahudanci, Kiretawa da Larabawa, duk munji su suna fadi a harshenmu game da manyan ayyukan Allah.''
चाहे यहूदी चाहे उनके मुरीद, करेती और 'अरब हैं। मगर अपनी अपनी ज़बान में उन से ख़ुदा के बड़े बड़े कामों का बयान सुनते हैं।
12 Dukansu suka yi mamaki suka rikice; suka ce da junansu, ''Menene ma'anar wannan?''
और सब हैरान हुए और घबराकर एक दूसरे से कहने लगे, “ये क्या हुआ चाहता है?”
13 Amma wasu suka yi ba'a suka ce, ''Sun bugu ne da sabon ruwan inabi.''
और कुछ ने ठठ्ठा मार कर कहा, “ये तो ताज़ा मय के नशे में हैं।”
14 Amma Bitrus ya tashi tare da sha dayan, ya daga murya ya ce da su, ''Mutanen Yahuda da dukanku dake zaune a Urushalima, bari ku san wannan; ku saurari maganata.
लेकिन पतरस उन ग्यारह रसूलों के साथ खड़ा हूआ और अपनी आवाज़ बुलन्द करके लोगों से कहा कि ऐ यहूदियो और ऐ येरूशलेम के सब रहने वालो ये जान लो, और कान लगा कर मेरी बातें सुनो!
15 Domin wadannan mutanen ba buguwa suka yi ba yadda kuke zato, domin yanzu karfe tara ne na safe kawai.
कि जैसा तुम समझते हो ये नशे में नहीं। क्यूँकि अभी तो सुबह के नौ ही बजे है।
16 Amma wannan shine abinda aka fada ta wurin annabi Yowel.
बल्कि ये वो बात है जो योएल नबी के ज़रिए कही गई है कि,
17 Allah ya ce, 'Haka zai kasance a kwanakin karshe, zan zubo Ruhuna a kan dukan mutane, 'ya'yanku maza da mata za su yi anabci, kuma samarinku za su ga wahayoyi, kuma tsofaffinku za su yi mafarkai.
ख़ुदा फ़रमाता है, कि आख़िरी दिनों में ऐसा होगा कि मैं अपनी रूह में से हर आदमियों पर डालूँगा और तुम्हारे बेटे और तुम्हारी बेटियाँ नुबुव्वत करें गी और तुम्हारे जवान रोया और तुम्हारे बुड्ढे ख़्वाब देखेंगे।
18 Haka kuma a bisa bayi na maza da mata, a kwanakin nan zan zubo da Ruhuna, kuma za su yi anabci.
बल्कि मै अपने बन्दों पर और अपनी बन्दियों पर भी उन दिनों में अपने रूह में से डालूँगा और वह नुबुव्वत करेंगी।
19 Zan nuna al'ajibai a sararin sama da kuma alamu a bisa duniya, jini da wuta, da girgije.
और मैं ऊपर आस्मान पर 'अजीब काम और नीचे ज़मीन पर निशानियां या'नी ख़ून और आग और धुएँ का बादल दिखाऊँगा।
20 Rana zata juya ta koma duhu kuma wata ya koma jini, kafin Babbar ranan nan ta Ubangiji ta zo.
सूरज तारीक और, चाँद ख़ून हो जाएगा पहले इससे कि ख़ुदावन्द का अज़ीम और जलील दिन आए।
21 Zai kuma zama dukan wanda ya kira ga sunan Ubangiji zai sami ceto.
और यूँ होगा कि जो कोई ख़ुदावन्द का नाम लेगा, नजात पाएगा।
22 Mutanen Isra'ila, ku saurari wadannan magana. Yesu Banazare, mutumin da Allah ya tabbatar da shi gareku ta wurin manyan ayyuka da ban mamaki da alamu da Allah ya yi ta wurinsa a tsakiyarku, kamar yadda ku da kanku kuka sani.
ऐ इस्राईलियों! ये बातें सुनो ईसा नासरी एक शख़्स था जिसका ख़ुदा की तरफ़ से होना तुम पर उन मोजिज़ों और 'अजीब कामों और निशानों से साबित हुआ; जो ख़ुदा ने उसके ज़रिए तुम में दिखाए। चुनाँचे तुम आप ही जानते हो।
23 Saboda tabbataccen shiri da riga sani na Allah, aka bayar dashi, ku kuma, ta hannun mutane 'yan tawaye, kuka gicciye shi kuma kuka kashe shi.
जब वो ख़ुदा के मुक़र्ररा इन्तिज़ाम और इल्में साबिक़ के मुवाफ़िक़ पकड़वाया गया तो तुम ने बेशरा लोगों के हाथ से उसे मस्लूब करवा कर मार डाला।
24 Wanda Allah ya tayar, bayan ya cire zafin mutuwa daga gareshi, saboda ba zai yiwu ba ta rike shi.
लेकिन ख़ुदा ने मौत के बंद खोल कर उसे जिलाया क्यूँकि मुम्किन ना था कि वो उसके क़ब्ज़े में रहता।
25 Gama, game da shi, 'Ina ganin Ubangiji a gabana ko yaushe, domin yana gefen hannun damana saboda kada in firgita.
क्यूँकि दाऊद उसके हक़ में कहता है। कि मैं ख़ुदावन्द को हमेशा अपने सामने देखता रहा; क्यूँकि वो मेरी दहनी तरफ़ है ताकि मुझे जुम्बिश ना हो।
26 Saboda haka zuciyata na farin ciki harshena yana yin murna. Kuma, jikina zai zauna gabagadi.
इसी वजह से मेरा दिल ख़ुश हुआ; और मेरी ज़बान शाद, बल्कि मेरा जिस्म भी उम्मीद में बसा रहेगा।
27 Gama ba za ka watsar da raina a lahira ba, ba kuwa za ka bar Mai Tsarkinka ya ga ruba ba. (Hadēs g86)
इसलिए कि तू मेरी जान को 'आलम — ए — अर्वाह में ना छोड़ेगा, और ना अपने पाक के सड़ने की नौबत पहुँचने देगा। (Hadēs g86)
28 Ka bayyana mani hanyar rai; da fuskarka zaka cika ni da farin ciki.
तू ने मुझे ज़िन्दगी की राहें बताईं तू मुझे अपने दीदार के ज़रिए ख़ुशी से भर देगा।
29 'Yan'uwa, zan yi magana da ku gabagadi game da baba Dauda: ya mutu kuma aka bizne shi, kuma kabarinsa na nan tare da mu har yau.
ऐ भाइयों! मैं क़ौम के बुज़ुर्ग, दाऊद के हक़ में तुम से दिलेरी के साथ कह सकता हूँ कि वो मरा और दफ़्न भी हुआ; और उसकी क़ब्र आज तक हम में मौजूद है।
30 Domin haka, don shi annabi ne kuma ya san Allah ya yi masa alkawari da rantsuwa cewa daga cikin zuriyarsa zai sanya wani bisa kursiyinsa.
पस नबी होकर और ये जान कर कि ख़ुदा ने मुझ से क़सम खाई है कि तेरी नस्ल से एक शख़्स को तेरे तख़्त पर बिठाऊँगा।
31 Ya hango wannan al'amari kuma ya yi magana game da tashin Almasihu, 'Ba ayi watsi da shi ba a lahira, kuma jikinsa bai ga rubewa ba.' (Hadēs g86)
उसने नबुव्वत के तौर पर मसीह के जी उठने का ज़िक्र किया कि ना वो' आलम' ए' अर्वाह में छोड़ेगा, ना उसके जिस्म के सड़ने की नौबत पहुँचेगी। (Hadēs g86)
32 Wannan Yesun - Allah ya tashe shi, wanda dukanmu shaidu ne.
इसी ईसा को ख़ुदा ने जिलाया; जिसके हम सब गवाह हैं।
33 Saboda haka yadda aka tashe shi zuwa hannun dama na Allah kuma ya karbi alkawarin Ruhu Mai Tsarki daga wurin Uba, shine ya zubo mana wannan da kuke gani kuma kuke ji.
पस ख़ुदा के दहने हाथ से सर बलन्द होकर, और बाप से वो रूह — उल — क़ुद्‍दुस हासिल करके जिसका वा'दा किया गया था, उसने ये नाज़िल किया जो तुम देखते और सुनते हो।
34 Dauda bai hau zuwa sama ba, amma ya ce, ''Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna hannun dama na,
क्यूँकी दाऊद बादशाह तो आस्मान पर नहीं चढ़ा, लेकिन वो ख़ुद कहता है, कि ख़ुदावन्द ने मेरे ख़ुदा से कहा, मेरी दहनी तरफ़ बैठ।
35 har sai na maida makiyanka abin takawar sawunka.'''
जब तक मैं तेरे दुश्मनों को तेरे पाँओ तले की चौकी न कर दूँ।’
36 Saboda haka, bari gidan Isra'ila su sani tabbas wannan Yesun wanda kuka gicciye, Allah ya maishe shi Ubangiji da kuma Almasihu.
“पस इस्राईल का सारा घराना यक़ीन जान ले कि ख़ुदा ने उसी ईसा को जिसे तुम ने मस्लूब किया ख़ुदावन्द भी किया और मसीह भी।”
37 Da suka ji haka sai suka soku a zukatansu, suka cewa Bitrus da sauran manzanni, '''Yan'uwa me za mu yi?''
जब उन्हों ने ये सुना तो उनके दिलों पर चोट लगी, और पतरस और बाक़ी रसूलों से कहा, “ऐ भाइयों हम क्या करें?”
38 Sai Bitrus ya ce masu, ''Ku tuba ayi wa kowannenku baftisma, cikin sunan Yesu Almasihu domin gafarar zunubanku, kuma za ku karbi baiwar Ruhu Mai Tsarki.
पतरस ने उन से कहा, तौबा करो और तुम में से हर एक अपने गुनाहों की मु'आफ़ी के लिए ईसा मसीह के नाम पर बपतिस्मा ले तो तुम रूह — उल — क़ुद्दूस इनाम में पाओ गे।
39 Domin alkawarin a gareku ne da 'ya'yanku da duk wadanda ke nesa, dukan iyakar mutanen da Ubangiji Allahnmu zai kira.''
इसलिए कि ये वा'दा तुम और तुम्हारी औलाद और उन सब दूर के लोगों से भी है; जिनको ख़ुदावन्द हमारा ख़ुदा अपने पास बुलाएगा।
40 Da maganganu da yawa ya ba da shaida kuma ya karfafa su; ya ce, ''Ku ceci kan ku daga wannan muguwar tsara.''
उसने और बहुत सी बातें जता जता कर उन्हें ये नसीहत की, कि अपने आपको इस टेढ़ी क़ौम से बचाओ।
41 Sai suka karbi maganar sa kuma aka yi ma su baftisma, a wannan rana kuma aka sami karin rayuka wajen dubu uku.
पस जिन लोगों ने उसका कलाम क़ुबूल किया, उन्होंने बपतिस्मा लिया और उसी रोज़ तीन हज़ार आदमियों के क़रीब उन में मिल गए।
42 Su ka cigaba cikin koyarwar manzanni da zumunta, cikin kakkaryawar gurasa da kuma cikin addu'o'i.
और ये रसूलों से तालीम पाने और रिफ़ाक़त रखने में, और रोटी तोड़ने और दुआ करने में मशग़ूल रहे।
43 Tsoro ya sauko bisa kowane rai, kuma aka yi abubuwan ban mamaki da alamu da yawa ta wurin manzannin.
और हर शख़्स पर ख़ौफ़ छा गया और बहुत से 'अजीब काम और निशान रसूलों के ज़रिए से ज़ाहिर होते थे।
44 Duka wadanda suka ba da gaskiya suna tare kuma komai nasu na kowanensu ne,
और जो ईमान लाए थे वो सब एक जगह रहते थे और सब चीज़ों में शरीक थे।
45 kuma suka saida kadarorinsu da mallakarsu kuma suka rarrabawa kowa, bisa ga irin bukatar da kowannensu yake da ita.
और अपना माल — ओर अस्बाब बेच बेच कर हर एक की ज़रुरत के मुवाफ़िक़ सब को बाँट दिया करते थे।
46 A kowace rana suka cigaba tare da nufi daya a cikin haikali, suna kakkarya gurasa a gidaje, kuma suna raba abinci tsakaninsu cikin farin ciki da tawali'u a zuciya;
और हर रोज़ एक दिल होकर हैकल में जमा हुआ करते थे, और घरों में रोटी तोड़कर ख़ुशी और सादा दिली से खाना खाया करते थे।
47 Suna yabon Allah kuma suna da tagomashi a gaban dukan mutane. Ubangiji kuma kullum yana kara masu wadanda suke samun ceto.
और ख़ुदा की हम्द करते और सब लोगों को अज़ीज़ थे; और जो नजात पाते थे उनको ख़ुदावन्द हर रोज़ जमाअत में मिला देता था।

< Ayyukan Manzanni 2 >