< Ayyukan Manzanni 18 >
1 Bayan haka sai Bulus ya tafi Antakiya daga nan, ya wuce Korinti.
2 A can ya sadu da wani Bayahude mai sunan Akila, dan kasar Buntus ne; bai dade da zuwa garin ba, daga Italiya ya zo da matarsa mai suna Balkisu, saboda Kalaudiyas ya ba da umarni dukan Yahudawa su bar Roma; sai Bulus ya je wurinsu.
3 Bulus ya zauna a gidansu don sana'arsu daya ce, wato, masu aikin Tanti ne.
4 Saboda haka Bulus na zuwa majami'a, yana yin nazari tare da su a kowace Asabaci. Yana kokari ya rinjayi Yahudawa da Helinawa.
5 Amma a lokacin da Sila da Timoti suka iso Makidoniya, Ruhu ya matsa Bulus ya shaida wa Yahudawa cewa Yesu Almasihu ne.
6 Lokacin da Yahudawa suka tayar masa suna zarginsa. Bulus ya kakkabe rigansa a gabansu yana cewa, “Alhakin jininku yana kanku; daga yanzu zan koma wurin al'ummai.”
7 Da ya bar wurinsu, ya tafi gidan Taitus Yustus mai wa Allah sujada. Gidansa na kusa da majami'a.
8 Kiristus shine shugaban majami'a, sai shi da dukan iyalin gidansa sun ba da gaskiya ga Ubangiji. Korantiyawa da yawa suka ji jawabin Bulus suka ba da gaskiya, aka yi masu Baftisma.
9 Da dare Ubangiji ya ce wa Bulus a cikin wahayi, “Kada ka ji tsoro, amma ka yi magana kada kuma ka yi shuru.
10 Gama ina tare da kai, ba wanda zai cutar da kai, gama ina da mutane anan garin.”
11 Bulus ya zauna a nan tsawon shekara daya da wata shida, yana koyar masu da maganar Allah.
12 Amma da Galiyo ya samu zaman gwamnan Akaya, sai Yahudawa suka tayar wa Bulus har suka kai shi gaban dakalin shari'a.
13 Suna cewa, “Wannan mutumin yana kokarin rinjayar mutane su yi sujadar da ta saba wa dokarmu.”
14 Duk da haka kafin Bulus ya yi magana, Galiyo ya ce wa Yahudawa, “Ku Yahudawa in da karar ku ta wani babban laifi ce wanda ya aikata, da sai in hukunta.
15 Amma tun da ya ke akan al'amurar, kalmomi ne, da ta sunaye da dokokin ku, ku je ku sasanta al'amuran ku.”
16 Galiyo ya kore su daga dakalin shari'a.
17 Saboda haka sai suka kama Sastanisu, suka yi masa duka sosai a gaban dakalin shari'a. Amma Galiyo bai damu da yadda suka karasa ba.
18 Bulus kuwa, bayan ya zauna tare da su na wasu kwanaki masu yawa, ya bar 'yan'uwan zuwa Suriya ta jirgin ruwa, tare da Balkisu da Akila. Kafin ya bar tashar jiragen ruwa da ke a Sankuriya, ya tafi saboda ya aske kansa, domin ya dauki alkawarin Banazare.
19 Da suka iso Afisa, Bulus ya bar Balkisu da Akila anan. Shi kuwa ya shiga majami'ar Yahudawa yana nazari tare da su.
20 Da suka roki Bulus ya zauna da su na tsawon lokaci, bai yarda ba.
21 Ya kama hanyarsa ya bar su ya ce, “In Allah ya yardar mani zan dawo wurinku wata rana.” Sai ya shiga jirgin ruwa daga Afisa.
22 Daga saukar su a Kaisariya, sai ya haura zuwa Urushalima ya gai da iklisiya daga nan ya tafi Antakiya.
23 Bayan ya zauna na dan lokaci a wurin, Bulus ya kama hanyarsa zuwa yakin Galatiya da Firjiya anan ya karfafa almajirai.
24 A nan dai akwai wani Bayahude mai suna Afolos, dan asalin Iskandariya ne da haihuwa, ya zo Afisa. Shi masani ne a maganar Allah.
25 Afolos dai ya sami horo daga maganar Ubangiji. Shi mai kokari ne a ruhu, yana wa'azi da koyarwa daidai game da Yesu. Amma ya san da Baftismar Yahaya ne kadai.
26 Afolos ya fara wa'azinsa da gabagadi a cikin majami'a. Da Balkisu da Akila suka ji shi sai suka yi abokantaka da shi, suka kara bayyana masa game da labarin hanyar Allah mafi daidai.
27 Da ya so ya wuce zuwa cikin Akaya 'yan'uwa suka karfafa shi, sun rubuta wa almajiran da ke a Akaya, don su karbe shi da hannu biyu. Da ya iso wurinsu, ya kuwa karfafa 'yan'uwa da sun ba da gaskiya ta wurin alheri.
28 Afolos ya ba Yahudawa mamaki da irin ikon da yake da shi da gwanintarsa, yadda yake nunawa daga nassoshi cewa Yesu shine Almasihu.