< Ayyukan Manzanni 16 >
1 Bulus ya kuma isa Darbe da Listira, in da akwai wani almajiri mai suna Timoti a wurin, dan wata Bayahudiya wadda ta ba da gaskiya; ubansa kuwa Baheline ne.
2 Ana maganar kirki a kansa ta bakin 'yan'uwa da ke Listira da Ikoniyan.
3 Bulus ya yi wa Timoti kaciya, domin yana so su yi tafiya tare, domin kuma saboda Yahudawan da ke wurin, sun san cewa ubansa Baheline ne.
4 Suna shiga cikin biranen, suna yi wa iklisiyoyi gargadi da su yi biyayya da umurnan da Manzanni da dattawa suka rubuta a Urushalima.
5 Bangaskiyar iklisiyoyi kuwa ta karu, ana kuma samun karuwa na wadanda suke ba da gaskiya kowace rana.
6 Bulus da abokan aikin sa sun shiga cikin lardin Firigiya da Galatiya, tun da Ruhu Mai Tsarki ya hana su wa'azin kalmar a cikin yankin Asiya.
7 Sun zo kusa da Misiya, da nufin shiga cikin Bitiniya, Ruhun Yesu ya hana su.
8 Da suka ratse ta cikin Misiya, sai suka shiga birnin Taruwasa.
9 Bulus ya ga wahayi cikin dare, wani mutumin Makidoniya na kiransa, yana cewa. ''Ka zo Makidoniya ka taimake mu''.
10 Bulus, da ganin haka, ya kama hanya zuwa Makidoniya, da tunanin Allah ne ya ke so su kai wa mutanen Makidoniya bishara.
11 Da barin Taruwasa, Bulus da kungiyarsa sun shiga jirgin ruwa zuwa Samutaraki, da gari ya waye kuma sun tafi Niyafolis;
12 Daga nan kuma suka tafi Filibi, birni na Makidoniya, mai muhimmanci ne a yankin Roma, in da mun yi zango kwanaki da dama.
13 Ranar Asabaci mun je kofar gari, gefen rafi, da tunanin samun wurin addu'a. Mun zauna mun kuma yi magana da matan da sun taru a wurin.
14 Wata mace mai suna Lidiya, 'yar kasuwa ce a birnin Tiyatira, mai bautar Allah ce, ta saurare mu. Ubangiji ya bude zuciyarta, ta mai da hankali ga maganar da Bulus ke fadi.
15 Sa'anda da aka yi mata Baftisma tare da mutanen gidanta, ta ce da mu, “Idan kun dauke ni mai bautar Allah, ku zo gidana ku zauna.” Sai ta rinjaye mu.
16 A daidai wannan lokaci, muna tafiya wurin addu'a, wata yarinya mai ruhun duba ta hadu da mu. Iyayen gijinta na arziki da ita sosai.
17 Tana bin Bulus, tare da mu, tana fadi da murya mai karfi cewa, ''Wadannan mutanen, bayin Allah mafi daukaka ne, suna sanar maku hanyar ceto ne''.
18 Ta dauki kwanaki tana haka. Amma Bulus ya yi fushi da ita ainun, ya juya ya umarci ruhun, ya ce, ''Na umarce ka, ka rabu da ita a cikin sunan Yesu Almasihu''. Ruhun ya yi biyayya ya rabu da ita nan take.
19 Da iyayengijinta suka ga cewa hanyar shigar kudinsu ta toshe, sai suka kama Bulus da Sila, suka ja su cikin kasuwa suka kai su gaban mahunkunta.
20 Da suka kai su Kotu, suka ce, ''Wadannan mutane Yahudawa ne, suna kawo tashin hankali a birninmu.
21 Suna koyar da abubuwa da ba su karbuwa a gare mu, balle mu aikata, a matsayinmu na Romawa.”
22 Sai jama'a gaba daya sun tayar wa Bulus da Sila; alkalan kuma sun yage rigunansu, sun ba da umarni a duki Bulus da Sila da bulala.
23 Bayan dukan, an jefa su Bulus a kurkuku, an ba mai tsaron kurkukun umurni ya kulle su da kyau, kada su gudu.
24 Shi kuma ya yi hakanan, ya sa masu sarkoki a kafafun su, kamar yadda aka umurce shi.
25 Da tsakar dare, Bulus da Sila suna yin adu'a, su na raira wakoki ga Allah, sauran 'yan sarkar su na jin su.
26 Nan da nan sai ga wata girgizar kasa, wadda ta sa ginshikan kurkukun sun kadu, nan da nan kofofin kurkukun sun bude, 'yan sarka kuma, sarkokin su sun karkatse.
27 Mai tsaron kurkukun ya tashi daga barci ya ga kofofin kurkukun a bude, ya zaro takobi, zai kashe kan sa, a tunanin sa, 'yan sarkar sun gudu.
28 Amma Bulus ya ta da murya da karfi, ya ce, ''kada kayi wa kanka barna, domin dukan mu muna nan''.
29 Mai tsaron kurkukun ya aika a kawo fitila, ya shiga ciki a gurguje da rawan jiki, ya fadi a gaban Bulus da Sila,
30 ya fitar da su waje ya ce, ''Shugabanni, me ya kamata in yi domin in tsira?''
31 Sun ce masa, ''ka ba da gaskiya ga Yesu Ubangiji, da kai da gidan ka, za ku sami tsira''.
32 Bulus da Sila suka fada masa maganar Ubangiji, tare da iyalinsa.
33 Shi mai tsaron kurkukun ya dauke su cikin daren, ya wanke raunukansu, an kuma yi masa Baftisma nan da nan tare da iyalinsa.
34 Ya kai Bulus da Sila gidansa, ya ba su abinci. Murna ta cika gidan mai tsaron kurkukun, domin iyalin sa duka sun ba da gaskiya ga Allah.
35 Da gari ya waye, alkalai sun ba da sako a saki Bulus da Sila.
36 Mai tsaron kurkukun kuwa ya sanar wa Bulus wannan magana ta alkalan, saboda haka ya ce wa Bulus, ''Ku tafi cikin salama''.
37 Amma Bulus ya ce masu, “Sun yi mana duka a fili a gaban mutane mu da muke Romawa, ba a kashe mu ba, sun kuma sa mu a kurkuku; suna koran mu a asirce? Su zo da kansu su fitar da mu.
38 Masu tsaron kurkuku sun mayar da maganar Bulus ga alkalan, wanda ya sa sun firgita, da jin cewa Bulus da Sila Romawa ne.
39 Alkalai da kansu sun zo sun roki Bulus da Sila; da suka fitar da su daga kurkukun, sun ce wa Bulus da Sila su bar birnin.
40 Da hakanan ne Bulus da Sila suka fita daga kurkuku, sun je gidan Lidiya. Da Bulus da Sila sun ga 'yan'uwa, sun karfafa su, sa'annan suka bar birnin.